NIDA YA AHMAD

4.1K 317 86
                                    

*🍒🌺NIDA YA AHMAD🌺🍒*

*BY ASMERHLUV*

*WATTPAD@ASMASANEE*

*INSTAGRAM@BYNERH_AUGIE*

*_GSK INA GANIN MASOYYAN NABLA SONFI YAWA WANNAN IRIN COMMENT GSK NA YABA SOSAI MUSAMMAN MY WATTPAD,KUNA SANI NISHADI ALLAH YA BAR MU TARE HAR GIDAN ALJANNA AMEEN👌💖_*

بسم الله الرحمن الرحيم

*119~120*
   
      "Tashin ta ke nan ba kuma kalmar dake fitowa bakin ta sai ya sake ni , lumshe idon ta tayi zafafan hawaye na xobo wa saman face,daidai lkc doc ya shigo duba ta , subhanallah yafada lkc da yaga halin da take ciki yadda jikin ta ke cira ga zafafan hawaye dake mata kwaranya saman fuska ,alurar bacci yayi mata wanda nan take bacci ya dauke ta amma fa har yanxun jikin ta cira yake kmr mai ciyon farfadiya,
*******
    "Jikin sa yau ya saki ,har ya samu yayi wanka yayi sallah xahar ya samu yayi ,sai lkc ya samu ya kunna phones dinsa dake off,
  "Kunna family phones dinsa bai da wuya call din ammy na shigo wa lumshe idon sa yayi yana tuna halin daza ta shiga na rashin sa har na tsawon sati daya,kiran na kokarin tsinkewa ya daga,
   "Har yana iya jiyo lkc da sauke a jiyan xuciya,
  "Sannu Ahmad,ashe har anyi lkc da xaka iya barin mu ba tare da sani naba koh abbu kan hakan da nayi ka kyauta?,,,,
   " Lumshe idon sa yayi yana jin dacin mgn mahaifiyar tasa,
  "Can ciki yayi mgn wadda da kaji ta kasan ta mara sa lpy ce,
  "Ammy ai bakya so na don da xaki naime ni koh kin san halin da nake ciki inda nake,da azabar da nake ciki?yayi mgnr yana numfashi kasa kasa,
  "Ay nan take ammy ta mike tsaye inda take xaune cike da tashin hankali tace me yake damun ka Ahmad kana ina? tayi masa tambayar ajere,,
   "Tauri ya sarkafe shi wanda ya hani shi  fadin abunda yake so ya fada,nan take ammy ta rikice saiga hawaye suna sulalo mata saman fuska(don ba karamin so take wa yaron nata ba)
   "Sai famar kiran Ahmad Ahmad,fadamin ina kake Ahmad,ina ya kasa mgn sai taurin da yake daga karshe ma jifa da wayar yayi saman bed,
  "Bil hakki tauri ya turnuke shi tun yana saman gado har ya sauko kasa,damar sa akwai gorar ruwa gefen sa,,,ya kafa ya shanye gorar ruwan tass,kamin ya samu taurin ya lafa ,,,,saman gado ya koma yana maida numfashi,,,
   "Hkl tashe ramlarh da ta sauko taga ammy na share hawaye take tambayar ta lpy ,,ba tare da komi ba ammy ta kwashe komi tafada ma ramlarh itama nan take hkl ta ya tashi,,
  Nikam ina skull ban san me ake toyawa ba a gida😁(xaki sani ne lkc da Ahmad ya samu damke k'i ne😀)
      "Family doc dinsa ya kira ya sheda masa ya same sa a guest house dinsa,
   "Ba dade wa ba doc koh yaxo don dama yasan gidan,
   "Lkc da ya auna Ahmad ya ga halin da yake ciki ba karamin jin jina al'amarin yayi ba,drip ya saka masa yayi masa allurar bacci,yafita ,ya dauki a 3 hour kamin ya dawo,ledar pharmacy,lkc Ahmad ya falka kuma a lkc ruwa suka kare,
  "Doc ya kama masa ya mike ya jin gina da pillow da ya tare masa baya,,,ganin kmr alamar Ahmad baici koh mi ba yasa doc yace kitchen ya samu kuku dake shashen ya samar ma Ahmad light food tare da black tea,
   Ya koma dakin inda ya iske Ahmad lumshe da idanu da alama tunani yakeyi,, Allah sarki Ahmad tunanin Nabeela yakeyi wanda bata masan yanayi ba,saida doc yayi gairan murya sa'an Ahmad yasan da shigowar sa,murmushi yake Ahmad ya sakar ma doc kamin yayi masa alama da hannu alamar ya tada shi,,,,
   "Brush yayi ,yai wanka ya dauro alwalla,lkc da yafito doc yafita hakan yasa ya saka jallabiya ya tada sallah,, la'asar lkc ma an kusa magrib hakan yasa yana kare asar ana tada sallah magrib sai ya hade yayi,shima doc sallah yaje yayi,
  "Saida ya amso abincin da kuka ya shirya ma Ahmad,
  "Ba wani ci Ahmad yayi ma abincin ba gara ma black tea din,Magani Doc yabama Ahmad ,,, atakaice dai saida Ahmad yayi sallah Isha doc ya kara saka masa drip,,,ya gwada masa yadda cire drip din idan suka kare yayi masa saida safe,
   "Wasa wasa saida Ahmad ya kwashe 3 ana sama masa drip ,yana kuma shan drugs,Alhamdllh yaji dama dama,
*****
    "Ammy hadda yar rama tayi ,da ka ganta kasan tana cikin damuwa saide ta kan danne idan tana gaban nabla cos bata son ta tambaye ta meke faruwa,
  Yanxu haka xaune take tayi ta gumi tana tunanin,sosai tayi xurfi cikin tunani,har yayi sallama bata ji shigowar sa ba,
  Hannu sa yasa ya janye hannu ta da tayi ta gumi wanda yasa ta dawo firgigit daga tunanin da take ciki,,,
  "Xummut ta mike tana shafa gefen fuskar sa ganin take gixo yake mata,
  Murmushi ya sakar mata yana rikoh hannu ta,suka xauna saman three star,
  Ammy baki da lpy ya tambaye ta cike da damuwa ganin yadda tafada,,
  Cikin sanyi tace duk damuwar da nake ciki yanxu ta kawar tunda shalele na ya dawo gare ni,
  "Kamshin turaren da ya baibaye masa sa hanci yasa ya kasa cewa kala sai dago da kansa da ya ya bi saitin inda kamshin ke fitowa,
   "Sanye nake cikin riga da skirt din cool  dark blue lace anyi masa xanen furen ni masu kyau dauke da ratsin baki,na ya na gyale ,hannu rike da jikka sosai shigar tayi mun kyau kmr bada jiki na twins da princess suka fito ba,
   "Saman jikin ammy na fada ina sakar mata murmushi wadda yasa Ahmad kusan shidewa daga inda yake tamkar mutum mutumi,
  "Ammy ni xan tafi xan kai dare na fada a shagwabe wanda ya kara daskare Ahmad,
   "Duba na da murmushi tayi tace baby har dare fa kika ce ita iftinan din fa ina kika barta,
   "Kai ammy tana fa wurin ramlarh kuma na bar mata duk wani abu da xata kuma ma ammy idan na fita da ita wa xai taya miki baby na fada ina kara narmewa saman jikin ammy tare da rufe fuska ta da hannu wa'inda ke dauke da jan lalle a yatsu na ,,,, murmushi ammy tayi tana mai fadin a dawo lpy ,,, cikin da kwarkwasa na mike xan bar wurin da sauri Ahmad xai rikoh gyale nawa ammy tayi saurin rikoh hannu sa tana mai hararar sa,
  "Hakan yasa na fita ina sakin murmushi mugun ta,
  "Wanna kuma fushin name na Ahmad tafada kmr bata san abunda ke faruwa ba,
  "Kasa mgn yakeyi sai faman huci yake idanun sa sunyi jawur dasu kmr garwashi,
"Hannu sa ya xare da na cikin ammy ya mike har yana tan gadi yabar parlour,,
  "Cike da tausayi ammy ta bishi da kallo tana jin tausayin yaron nata yana ratsa ilahirin jikin ta ,amma dole ta daure ta nuna bata jin komi don farin cikin nabla,,bayan haka gara ta dauki yancin ta kada Ahmad ya dauka a grantee ya same ta,,,
  "Tafiya yake yana tan gadi kmr wanda yayi shaye shaye hakan kuma yayi daidai da shigowar ,zeenarht , twins da yumna daga islamiya,ay suna ganin uban nasu su kayi kansa da gudu suna ihu,,
  ****
  "Aunty Aisha xaune gaban doc yana mata bayanin abunda ke damun lubna inda yake ce mata sis ta na dauki da hawan jini inda jinin ta har ya haura 100 ,bayan haka kuma tana dauke da ciyon xuciya wanda yake gab da kaiwa limit dinda abun baxaiyi kyau,don haka dole na ayi mata abunda take so kamin akai ga rasa ta,,,
  "Inalillahi wa'innailaihi raji'un itace kalmar da aunty Aisha ke maimai tawa , zafafan hawaye na silalo wa saman fuska ,Allahum ajirni fi musubati,wanna wace irin rayuwa ce ni Aisha diyar mutun 2 jikayan mutum 4,
  "Yanxu kije ki biya bill don a koh wane lkc xata iya farkawa,gyada masa kadai ta iya tabar office din jiki a sake,
  ****
  "Ganin yaran sa ya rage masa xafin abunda nabla ta kun sa masa,
   "Ba ni na dawo gidan ba sai karfe 9 isma'il ya maido ni gida,motor isma'il na wuce wa AHMAD na fitowa xaije part din mommy hakan yasa bai ga motar ba,
  "Taku na nake a hkl kwakwata ban lura da shiba sai shi nayi kwara da mutum,da sauri na dago ay koh karaf ido mu suka sarkafe cikin na juna,
  Da sauri na dauke nawa ina jan tsaki na matsa xan bar wurin da sauri ya jawo ni ya maida ni gaban sa ya tsalkafo hannu su da ta baya ya jawo ni jikin sa,,duk da yaji xafin tsakin da nake masa kullun amma hakan ya daure yace
  "A hkl cikin muryar mai taushi nabeelah kina so ne ki kashe ni ya fada yana axa kaine saman wuya na still yana goga fuskar shi gefen fuska ta
  "Ya ilahi wat is dis nafada can kasa makoshi,kamin na ja duk wata jarumtaka ta na ture shi daga jiki na,,,,
   "Cike da tsiwa nace wat is dis Ahmad nifa bana son iskan ce sai kayi ta
  Wait..... wait...Nabeela, repeat wat u just said now..sarai na gane abunda yasa shi cewa haka yasa nace
   Cewa nayi Ahmad bana son iskan ci koh ba Ahmad ne sunan naka nafada cike da tsiwa hada rike kunkuru cike da rashin mutunci,
    "Kasa mgn yayi sai kallo da yake bina dashi kmr bai taba gani na ba ,,,,
  Kamin can ciki naji yana fadin Nabeela Ahmad naji kin kira kai tsaye fa
  Toh miye a ciki don na kira koh akaui sauran alaka ta da kaine don haka ka shafa min lpy ina gama fadin haka nabar wurin ,kasa hana ni yayi sai ido da ya bini dashi,
   "Kasa shiga cikin gidan yayi ya juya ya bar part din,,,
   ""Bayan sati 1...!!!
"Ga ba daya Ahmad ya fita harkar nabla duk da shi kadai yasan abunda yake ji,,,
   "Tun karfe biyu nake shirya special abinci yau xanyi bako,ba ita ta fito ba sai karfe 4,don karfe biyar bakon nawa xaixo,direct toilet na shiga na tsala wanka nayi fess dani ,make up sosai na tsantsara ma fuska ta,
  "Dakakkiyar shadda wadda taji aiki riga da siket na saka na dauki gyale kalar aiki na yafa bayan na tsantsara darmin dan kwai,
  "Lkc kiran waya ta ya shigo ban dauka ba don nasan  ko waye ramlarh na kira nace taje ta dauki kayan takai gani nan xuwa,ke sis ina xaki da wannan kwalliyar haka? ramlarh ta tambaye ni tana miko min iftinan dake kuka ,inda kika aike ni ,idan baxaki iya xuwa ba ki fadamin na kai da kaina,abun bai kai can ba sis na tafi ,ga dai yafi miki nafada ina koma wa cikin dakin,,,,
   "Don kawai kada na bata make up dina ,yasa na kasa bama princess dita abincin ta sai ruwa na dirka mata van ma samu lkc hada mata madara ba😀(wlh kina tsula tsiyar ki nabla amma wlh ina guje miki haduwar ki da Ahmad🤣)
  "Allah sarki haka yarinyar tana ji tana gani tayi bacci dole ,na kaita dakin su ramlarh na wuce,
  "Dakin da aka tanadar ma baki sai baxa kamshi nakeyi,
  "Inda na iske isma'il sanye cikin sky blue shadda sai buga uban kamshi yakeyi sosai yayi kyau,kaina a k'asa na shiga parlour da sallama ta,
  "Daga da fararen idon sa yayi yana kallon na cike da so da kwana ya amsa min,kujerar dake gefen sa na xauna ina gyada shi bai amsa ba saima mikewa yayi ya dawo gaba na yayi gurfane yana so ya kalle fuska ta da na rufe da tafin hannu na,,,
****
    "Sanye yake cikin riga amr less tashan iska ,sai 3 qauter trouser ,gashin kan sa na sheki yana fidda kyalli ,har ya wuce ta gaban  extra room nd follow for guest sai yagan sa bude ga kuma shoes na macce da namiji hakan ya kwadai to da don shiga dakin hakan yasa ya kusa parlour kai tsayen sa tare da sirariyar sallama wadda shi Kadai yaji abunsa,,

Tau babbar mgnr wai dan akuya ya haifi dan zakara🤔

Nikoh asma'u nace meke shirin faruwa kuma🙄haka fans
  
Happy jum'at Mubarak

Don't forget to recite suratul khahafi🤗

#nida ya Ahmad
#vote
#Share
#follow
#pray
#so mai tsuma jiki

Ana mugun tare💕💕

Asmerhluv ce💃💃💃💃💃
  
  

           
   

NIDA YA AHMADWhere stories live. Discover now