Kwanci tashi asarar mai rai inji hausawa,a hankali shekaru suka yi ta tafiya har sisters din suka girma suka zama 'yammata.
Kamar yadda mutane sukayi tsammani haka ce ta kasance, Khadija grew up to be a very beautiful young lady, kyakykyawa sosai, irin kyan da in ka kalle ta sai ka sake kallonta, komai nata tamkar ita ta yiwa kanta.
Fara ce tas, doguwa mai doguwar fuska da dogon hanci, da siraran pink lips masu daukar hankali. Sexy eyes ne da ita matsakaita masu jan halkalin duk wanda ta kalla. Khadija tana da girman jiki dan in ka kalle ta zaka dauka tafi shekarun ta saboda komai da ake bukata a jikin mace Khadijah tana dashi tun kafin ta gana zama macen. Ga farin jini da Allah ya bata, dan tun tana jss3 take da samari, sai da Abba ya ajiye son da yake mata yayi mata fada sosai sannan aka daina zuwa zance gurinta, abinda basu sani ba shine ba wai daina samarin tayi ba, a'a daina kawo su gida tayi. Tana ss1 wani saurayinta ya saya mata waya, amma kaf gidan in banda Aisha da suke kwana tare babu wanda yasan tana da wayar, dan kashe ta take sai dare in Umma ta tafi dakin Abba sannan zata dauko tayi ta wayar ta, ta raba dare tana hira da samari wani lokacin har sai Aisha tayi bacci Khadijah tana waya. Aisha tayi kokarin yi mata fada sai tace "baƙin ciki kike yi min? Dan ke baki da saurayin da zai sai miki wayar?" Tun daga nan Aisha bata kuma yi mata magana akan hakan ba.
Har suka girma kan Khadija babu komai na karatu, boko da islamiyya duk zero, sai kwalliya da iya daukan wanka, wannan kuwa in da ace ana grading da A zata ke samu kullum. Sanda aka kai su senior class aka dinka musu sabon uniforms, Khadija sai ta dauki nata ta kai gurin tailor akayi shaping rigar, wandon ma aka mayar mata na gayu, Umma tayi ta mata fada daga karshe ta bata dogon hijab tace take sakawa akan kayan, amma Khadija sai ta zame ta je gurin tailor yayi mata dan karamin hijab, kullum sai ta saka babban ta fita daga gida, tana barin layinsu zata cire tasa ka karamin ta tayi tafiyar ta.Makarantar su mixed ce mata da maza, dan haka Khadija samari ne da ita a cikin students da kuma cikin staff, dan har fada ake yi akanta. Aisha abin yana damunta amma da tayi mata magana sai ta hauta da masifa, a karshe ma ta hada ta da wani malami saurayin ta ya zane ta wai ta saka mata ido da yawa.
Duk da Khadijah bata taba furtawaba amma A'isha ta san cewa Khadijah ta a jin takaicin kasancewar su sisters, tana ganin kamar munin Aishan yana reflecting on her, dan haka duk yadda zata yi bata son wani abu ya hada ta da Aishan a waje yadda za'a gane cewa sister dinta ce. Dan haka ko makaranta basa tafiya tare, Aisha da wuri take tafiya saboda bata son tayi missing assembly ita kuma Khadija sai ta tsaya ta jira kawayenta sun biyo mata.
Hatta yasaiyyadin islamiyyar su saurayin Khadija ne. A cikin samarinta akwai mai bata kudi, mai saka mata kati, mai kaita shopping din kayam kwalliya da sweets (bada sanin Umma take zuwa ba, duk abinda ta siyo kuma sai ta boye a dakin su inda tasan umman ba zata gani ba) dan haka kullum jakar Khadija da kudi, a makaranta sai abinda take so zata ci.
A bangaren Aisha kuwa tun ranar da su head girl suka yi mata dariya suka kira ta da mummuna tun a ranar ta saka a ranta cewa ita din mummunar ce. Dan haka ta kara jan jikinta baya daga cikin mutane, ta zama very self conscious of her appearance, gani take yi kamar duk abinda tayi za'ayi mata dariya ne. Ko dariya taji mutane suna yi a gefe takan saka a ranta cewa da ita suke, kuma a lokuta da dama da itan suke.
Aisha bata da girman jiki sam, 'yar karama ce in ka ganta ba zaka ce takai shekarun ta ba, baka ce sosai, kuma kankantar jikinta sai yasa kanta ya zama kamar yayi girma da yawa. Tana da manyan idanu farare tas, dan idonta har yafi na Khadija fari, hakan yasa kana kallonta idon zaka gani fari tas a cikin bakar fuska. Fuskarta doguwa ce, hancinta yana da tsaho da fadi gabakidaya yadda ya zamanto tamkar yayi wa siririyar fuskarta girma.
Tun daga primary har secondary Aisha bata taba daukan second position ba, kullum ita ce first, amma kuma sam bata da zakewa a aji, dan da wahala ayi tambaya ta daga hannu ko kuma ita tayi tambayar, saboda sam bata son abinda zai jawo hankalin mutane kanta ballantana suga munin ta suyi mata dariya. Bata da kawa ballantana aboki, in kaga Aisha tare da wani ko wata to ka tabbatar karatu suka zo ta koya musu.
YOU ARE READING
Aisha_Humairah
FanfictionIt is a story about two sisters that are like the two sides of a coin, totally different yet part of each other. It is a story about loneliness, sadness, discrimination, hypocrisy, self pity and of course love. Get your handkerchiefs ready because t...