The New Girl

9.4K 828 33
                                        

Tunda jirgin su Abbas ya sauka a Abuja  yake fama da babansa akan batun asibiti. Shi so yayi daga airport ya wuce dashi asibiti shi kuma uban yaki yafi so a kaishi gida in yaso likitansa ya bishi can ya duba shi. Dole hakan akayi yi. Suka tafi tangamemen empty gidansa da babu kowa sai ma'aikata. Ya kaishi har bedroom dinsa sannan ya kira doctor din a waya ya sanar dashi halin da ake ciki. Daga nan ya zauna a kan kujera ya zubawa mahaifin nasa ido yana lura da yadda numfashinsa yake fizga cikin jin jikin yanayin da yake ciki.

Yana ta so yayi masa maganar blood test dinsa amma kuma yana ganin that was not the right time. A haka doctor yazo ya same su yayi duk gwaje gwajensu na likitoci, ya daura masa ruwa da duk abinda ya kamata sannan yaja Abbas gefe yace "Ina ganin a shawarce ya kamata a fita dashi" Abbas yayi saurin cewa "saboda me? akwai abinda kake tunani ne?" likitan yayi studying Abbas a karshe ya yanke hukuncin he was strong enough to take the news sannan yace "I am suspecting lung cancer, but am not sure. Kuma ya kamata ayi diagnosing da wuri dan asan matakin da za'a dauka considering cewa jikinsa ba zai iya fighting ba" sai yayi saurin karawa da cewa "saboda shekarunsa" Abbas yace "and because he is HIV positive" doctor ya tsaya yana kallonsa, Abbas ya gyada kai yace "yes, na sani. Amma abinda ban sani ba shine ya akayi ya samu? How?" doctor yace "bazan iya gaya maka ba. Doctor-patient confidentiality." Abbas yace "OK. But at least tell me tun yaushe yake dauke dashi?" doctor yace "shekaru goma kenan ina treating dinsa, Yana shan magani yana komai dan haka bashi da problem."

Washegari Abbas yayi breaking news din to his father. Ya gaya masa kuma decision din da doctor ya ke son dauka na fita dashi waje. A lokacin ne kuma ya gaya masa yasan HIV status dinsa. News din cancer ba karamin girgiza shi yayi ba, dan tsoro ne karara ya fito a fuskarsa. A ransa yace "so, this is it" Mutuwar dai gata nan tazo amma kuma bai shirya ba, akwai abubuwa da yawa da yake so yayi kafin mutuwarsa sannan yana so yaga 'ya'yan Abbas. Ya tabbatar cewa ya bar jininsa a doron kasa. Tabbas bai shiryawa mutuwa ba saboda shi kamar yanzu ne ma yake jin dadin rayuwar. Ya juya yana kallon Abbas da yake zaune yana jiran amsar sa, he looked so pure, so innocent. Yace "kace masa yayi duk shirye-shiryen da suka dace na tafiyar" amma Abbas ba wannan amsar yake jira ba, kuma shi uban ya sani amma sai ya gimtse ya koma ya kwanta ya rufe idonsa yana jan numfashi da kyar.

Wani kululu ya tsaya a makogwaron Abbas, ya mike tsaye yana kallon tsohon yace "tunda na hadu da kai, abu guda daya dayasa na yafe maka nake maka kallon uba shine dan ina sakawa a zuciya ta cewa abinda ya faru tsakanin ka da Hajiya was a mistake, mistake din da babu wanda yafi karfin ya fada kansa. Na saka a raina cewa daga nan duk kunyi learning mistakes dinku kuma baku kara kusantar wata hanya makamanciyar wadda kuka bi ba.  But right now I feel so ashamed. I feel so dirty. Shin kasan kuwa hukuncin da ubangiji ya tanadarwa mazinacin da har ya tsufa bai tuba ba? Annabi cewa yayi ba zai ji ko kamshin aljanna ba bayan ita kuma aljanna ana iya jin kamshinta har tsahon tafiyar shekara dubu saba'in. Wanda duk baiji kamshinta ba kuwa to tabbas ba zai shige ta ba" ya juya da sauri yayi hanyar fita daga dakin yana jin ba zai iya ci gaba da kallon tsohon ba.

Har sai da ya kai bakin kofa sannan yaji daga bayansa ance "have you ever wondered why bani da aure a shekaru na?" ya juyo amma bai ce komai ba, ya cigaba da cewa "na samu ciwon nan tun zamanin kuruciyata tun bayan kuskuren daya faru da mahaifiyarka. Ni kaina bansan yadda akayi na samu ba, zata iya yiwuwa a gurin aski ne ko kuma a asibiti, ni dai kawai an gwada ni ance ina dashi" Abbas ya dawo ya zauna akan kujerar daya tashi yana auna maganar tasa. Ya cigaba da cewa "tun a lokacin nasan sakayya ce Allah yayi wa mahaifiyarka akaina ta wannan hanyar, tun a lokacin kuma na kudure niyyar ba zanyi aure ba saboda bazan shafawa wata ko wasu ciwon dani na dauko wa kaina ba. Daga baya nayi aurarraki saboda surutun mutane amma duk matar dana aura in taji ciwon da nake dashi sai ta ki zana dani ta gudu. Wannan yasa nake a yadda nake yanzu Abbas, alone. Babu mata babu 'ya'ya ballantana jikoki. Sai kai kadai Abbas. Kai kadai nake da kai duk duniya. Yanzu gashi rayuwata tazo karshe kuma zan mutu alone. Please Abbas ka daure ka cika min burina kafin in bar  duniya inga family dinka. I am living a sad and lonely life please don't let me have a sad and lonely death".

Aisha_HumairahDonde viven las historias. Descúbrelo ahora