Knock Knock

8.8K 835 71
                                    

Ta dago rikitattun idanuwanta ta sauke akan Kamal sannan ta kuma kallon hoton, cikin rawar murya tace "amma sanda aka haifeta ce min kayi dani take kama" ya danyi dariya yace "ke baki ga kamar ba? In my eyes she does look like you" Nura ya lura da yadda jikinta yake rawa, ya matso kusa da ita yana kallon hoton ya dafa wuyanta yace "are you alright dear?" Ta kalle shi kawai ba tare da ta ce komai ba, dan bata ma fahimci me yace ba hankalinta yana can wani tunani daban, ya sake maimaitawa sannan tace "am fine" duk sai suka dauka tunanin Khadija ne ta dawo mata sabo, ta sake cewa da Kamal "please in babu damuwa ina son ka bar min hoton nan" ya daga kafada yace "babu komai, you can keep it. Ina da wadansu. Na saka anyi su  yawa ne tun lokacin da ake cigiyarta" a hankali tace "thank you" daga nan sai Maryam ta shigo ta kawo musu abinci da ruwa, suka yi mata godiya amma suka ce sauri suke yi jirgin su zai tashi in few minutes. Ta kira wo musu 'ya'yan da suka haifa ita da Kamal, yara duk sunyi wayo masha Allah, maza hudu, Abubakar, umar, usman da Aliyu, sai mace guda daya mai sunan Yakumbo wacce suke kira da Amnah. Sanda zasu fito yi musu rakiya ne Nura ya fakaici idonsu ya ajiye musu wata envelope mai kauri, dan yasan in ya bawa Kamal kudi hannu da hannu ba lallai ya karba ba, sannan ya ja Kamal gefe yayi masa tayin cewa ya karbi gidansa daya gina saboda in sunzo gari suke zama, yace "tunda in munzo din ba zaman muke ba, Inna tafi son mu zauna a gurin ta, ku koma can kawai ku zauna har sai sanda Allah ya hore muku kukayi naku" Kamal ya girgiza kai yace "nagode sosai da kulawa, amma kaima kasan Alhaji ba zai bari ba, a inda ka ganni anan dai ka barni anan din har zuwa yadda hali zaiyi" Nura baiji dadi ba amma ya fahimta, yasan halin Alhajin su Kamal, jajirtaccen bafulatani ne, very proud, ba zai taba bari dansa ya zauna a gidan aro ba. Suka yi exchanging phone numbers daga mazan har matan sannan suka rabu.

Har suka shiga cikin jirgi suka zauna hankalin Aisha baya tare da ita, Nura ya rabu da ita sai da jirgin su ya tashi sukayi settling a sama sannan ya dafa hannunta yace "talk to me", ta kalleshi blankly sannan ta kalli hannunta, scar din hannunta tana nan har yau amma ta zuciyarta ta baje tun tuni, ta bude hannun ta tana sake kallon hoton jaririyar da Kamal ya bata, 'yar Khadijah, gudan jininta. Ta juyo bayan picture din taga rubutu kamar haka: Aisha Humairah Kamal, born on........ , lost on ............. Tayi noticing dates din sannan ta dago ta kalli Nura a kusa da ita tace "sunan ta Humairah" ya bita da kallo cikin rashin fahimta, ta sake cewa "sunanta Humairah, as in Humairar mu ta gida" sai yanzu ya fahimci me take nufi, da sauri ya fara girgiza kansa, ta rike hannunsa cikin rawar murya tace "Nura ka yarda dani, I am 70% sure cewa itace, tun sanda na dauko yarinyar nan jikina yake bani itace amma na kasa tabbatarwa, kullum ina neman hanyar da zambi in tabbatar da zargina, amma maganganun da Kamal yayi yau sun saka na nunka zargina" ya riko ta saboda ganin yadda jikinta yake karkarwa yace "Aisha look at me, just because yarinyar nan ba'a san iyayenta ba kuma sunan su yazo daya da yarinyar Kamal ba zai saka ta zama yarinyar Kamal ba. Aisha nawa ce a duniya? sunan Aisha kusan yafi kowanne suna yawa, it maybe a coincidence" tace "yes, it may, but then it may be true" yace "babu wani similarities a tsakanin su, besides cewa duk farare ne ban ga kamanni ba sam" tace "that is because baka san Khadijah ba. Na tabbatar zaka iya kirga ganin da kayi mata a rayuwa. Tunda aka haifi Khadijah na san ta, zan iya cewa nafi kowa sanin ta hatta iyayen mu ba zasu nuna min sanin Khadijah ba. Yes, a fuska Humairah bata kama da khadija, amma kuma yadda suke gudanar da abubuwansu iri daya ne, yanayin jikinsu, maganarsu, dariyarsu, tafiyarsu, wani abun in Humairah tayi sai inji kamar in kira ta da Khadijah ta amsa" ta mika masa hoton yarinyar tace "just look at this picture" ya karba yana dubawa, a hankali dan yatsansa ya sauka a kan habar babyn, shima yaga abinda Aisha ta gani. Jikin Nura ya fara sanyi yanzu, amma baya son ya kara wa Aisha false hope, yace "amma ba kya ganin cewa 'yar Khadijah ba zata kai Humairah shekaru ba?" Aisha tace "that's what I want to confirm as soon as mun sauka Abuja" Nura ya shafa fuskarsa yace "amma in Humairah itace Humairah then ina Khadijah take? Ya akayi ta kai 'yarta gidan marayu?" Aisha ta rufe fuskarta da hannayenta, emotions din da take ta rikewa suna so sufi karfinta su fito, bata son tayi kuka, bata son ta jawo hankalin mutane kansu. Sai data saita numfashinta sannan ta kalli Nura tace "if Humairah is Humairah then Khadija is dead".

Aisha_HumairahWhere stories live. Discover now