Abba fada yake yi har muryarsa tana sarkewa, Khadijah kuma kuka take yi kamar idonta zai fado kasa. Yayinda gwoggo take ta faman rantse rantse cewa abinda Aisha ta fada karya take yi, amma Abba ko sauraronta baiyi ba, dan yaji a jikinsa cewa ba karya bane ba, kawai babu yadda zaiyi da yayar tasa ne, amma ya san ta riga ta cuceshi, yasan Dr AbdulRazak ya riga ya cuce shi babu yadda zaiyi dashi, babu abinda zaiyi masa sai dai yayi masa Allah ya isa, wadda kuma yasan Allah sai ya isar masa din, ko ba jima ko ba dade kamar yadda yazo har gida ya dauki 'yarsa ya lalata masa ita to shima sai anyi wa tasa 'yar haka.
Garin fadan ne ya shiga dakin gwoggo, anan ne yaga lodin kaya a tsakar daki, ya tsaya kawai yana kallon kayan yana jin wani bakin ciki yana taso masa, ashe shi sayar da mutuncin 'yar tasa akayi bai sani ba. Ya san kuma shima mai laifi ne, shi ya fara bude wa yarinyarsa ido da duniya da kuma son abin duniya, shi ya nuna mata cewa she can get anything she wants, har ta saka abin a ranta kuma har kuma yanzu gashi ya zama rayuwarta.
Aisha ranar bata kuma fitowa ba, dan tasan yadda gwoggo ta zuciya zata iya ballata, ita dama jiki ba jiki ba. Tana nan a kwance a daki har ta daina jin maganganun su, har bacci ya fara daukanta taji an bugo kofar dakin da karfi an shigo, ta tashi zaune da sauri taga Khadijah a tsaye tana huci kamar wata zakanya, idonta ya kada yayi jawur haka fatar fuskarta gabakidaya, ta fara magana cikin dacin murya mai cike da tsana da kyama, tace "I hate you. Na tsane ki fiye da komai a duniya. You are a curse to my life. Duk wani abu na ke ce kike ruguza min shi. Da ace ina da damar chanza 'yar'uwa da tun sanda na bude ido na na ganki a matsayin 'yar uwata da tuni na chanza ki. Bansan laifin me nayi wa Allah ya hada ni da jaraba a matsayin yaruwa ba. To ki sani, daga yau you are not my sister, babu ni babu ke, ko a ranki kar ki kuma sakawa cewa ni na hada dangantaka da ke" ta juya ta fice daga dakin.
Aisha ta koma ta kwanta, a hankali hawaye ya cigaba da bin kuncinta. Wannan wacce irin rayuwa ce tsakaninta da 'yar 'uwarta? Gudan jininta? Anya kuwa da akwai 'yan'uwa irinsu a duniya?
Washegari duk suka tashi kamar babu abinda ya faru, sai Abba da lokaci daya ya wani irin fadawa kamar marar lafiya. Abincin karyawa ma da kyar ya danci kadan ya barshi yace ya koshi. A ranar ne kuma result din su Aisha ya fito, 9 credits take dashi, murna kamar ta zuba ruwa a kasa ta sha, amma ita kadai tayi murnar ta, daga gwoggo har Khadijah harara suke binta da ita, babu wanda yace mata ci kanki ballantana a taya ta murna. Nura ne dama yaje ya fiyo mata dashi kuma kawo mata har gida, ta nuna wa Abba shima yayi murna sosai, sati daya bayan nan admission list ya fito, ana kafewa Nura ya kira ta a waya ya sanar da ita sunanta ya fito, kuma an bata medicine din da take nema, ranar Aisha har da kukan dadi tayi a daki, yayin da Khadija kuma tayi kuka bakin ciki a daki, tana ganin ya za'ayi Aisha ta tafi makaranta ta karanci medicine yayin da ita kuma take gida a zaune tana zaman banza?
Har yanzu kuma Prince charming bai zo ba, serious masu neman nata ma duk sun fara ja da baya dan sun lura ba auren nasu zata yi ba, duk yawanci masu nemanta yanzu masu son taba jikinta ne.
Aisha ta kira Aunty Bilkisu ta gaya mata labarin admission dinta, itama tayi murna sosai, washegari sai ga kudin registration nan ta aiko mata dashi dama ashe tana tara mata da niyyar zata biya mata, ta nuna wa Abba shima yaji dadi sosai, yace "dama ina ta lissafin yadda zan samu kudin da zan biya miki dashi, har ina tunanin ko kudinki da nake ajiyewa zan dauko in baki kiyi amfani dashi, amma tunda an samu wannan din shikenan, zan cigaba da ajiye miki sai bikin ki ayi amfani dashi" Aisha ta sunkuyar da kanta tana jin nauyin kalmar bikinta, amma kuma tana mamakin kudin da yake cewa ya ajiye mata, dan ita ta dauka duk kudin da take bashi kashewa yake yi musamman saboda halin rashin kuɗi da yake ciki, shi yasa yanke hukunci ba tare da facts ba bashi da kyau, babanta ne shi, he may not like her as much as he likes her sister, but he is still her father.
Nura ne ya taya Aisha registration, har ta gama gaba daya, sannan ta fara zuwa lectures. Ranar da zata fara zuwa har zazzabi tayi saboda tsoro, wannan shine asalin abinda ya sa ta bawa Khadija takardun ta tun farko, saboda tsoron facing mutane, amma gashi yanzu Nura yayi convincing dinta har ta sake exams kuma gashi yanzu zata fara zuwa makaranta. Bata san yaya mutane zasu karbeta ba, bata san kuma yaya zata karbi mutane ba, but she is sure of one thing, she is not going to show her face, saboda ta fahimci itace take repelling mutane daga gurinta.

YOU ARE READING
Aisha_Humairah
FanfictionIt is a story about two sisters that are like the two sides of a coin, totally different yet part of each other. It is a story about loneliness, sadness, discrimination, hypocrisy, self pity and of course love. Get your handkerchiefs ready because t...