The Run Girl

9K 808 13
                                    

Washegari sai ga daya daga cikin protocol din vc yazo gurin Mama, farko ta dauka cewa abinci yazo ci, shima kuma bada niyyar cin abincin yazo ba amma ganin sakwarar da Aisha tayi serving wani hade da vegetable soup da sassanyar sobo ya saka dole ya zauna babu shiri shima aka zuba masa ya ci sannan yaje gurin Mama da maganar da vc ya aiko shi da ita.

Yace "Hajiya Maryam dama haka kuka iya girki bamu sani ba? Muna can muna kashe kudin mu a waje ashe naku yafi dadi?" Cikin fara 'a da jin dadi Mama tace "thank you sir" yace "gaskiya jiya da naji vc da bakin sa suna santin girkin ku sai na dauka exaggerating suke yi, sai yanzu na tabbatar kin iya girki da gaske" ta sake cewa "thank you Sir, amma bani nayi ba, yarinyata ce, ta fini iya girki sosai" yace "is that so? Then tell her vc have a job for her. Zata ringa yin girki breakfast da lunch kullum. Sai muke billing dinku duk wata".

Mama ta ringa yi masa godiya kamar zata durkusa a kasa, ta kuma ce ayi musu godiya gurin VC. Taji dadi sosai saboda ta san zasuke samun kudi sosai, sannan kuma hakan wani cigaba ne a ɓangaren Aisha.

Tun da ta gaya wa Aisha ta kasa rufe bakinta dan dadi, taji dadin cewa wani ya yaba da abinta, wani as mighty as the vc ya yaba mata, shikenan ita abunda ba kuɗi ko fame ba .

Tana komawa gida Umma ta lura cewa yau tana cikin farin ciki, amma bata ce mata komai ba har sai da suka hadu suna cin abincin dare, tace "albishirinku" duk suka ajiye cokulan hannunsu suna kallonta, Umma ce tace "goro" nan Aisha ta basu labarin abinda ya faru da kuma aikin da VC ya bata. Umma murna, ta jawo Aisha jikinta ta rungume, Abba yace "amma Rabi'a ya kamata kiyiwa Maryam magana, ya kamata yanzu ta ringa bawa Aisha wani percentage a cikin kudin da zata ke samu, tunda dai ai ba zata ke yi mata bautar banza ba. Nima na samu in rage kayan ɗakin da yake kaina"

Khadija tace "wait, wai har kudi zata ke samu sosai?" Abba yace "eh mana, ai kamar kwangila ce za'ake basu, kudin da zasu ke samu sai ya ninka kudin da zasu ke kashewa" Khadija ta tabe baki tace "to Allah ya rufa asiri, kar taje ta kwafsa a koro su daga ita har Maman" da sauri Umma tace "wanne irin mugun baki ne wannan Khadija?" Khadija tace "ba mugun baki nake ba, kawai ina duba possibility din faruwar hakan ne, saboda duk munsan zuzutawa ne kawai irin na mutane amma A'isha ba wani iya girki tayi can ba" daga haka ta mike ta shigewarta daki, babu wanda ya kira ta yayi mata fadan abinda tayi. Nan suka zauna Abba yana ta plan din yadda zai ke ajiye kudin in an samu da irin abubuwan da zai siya dasu.

Aisha tana shiga daki ta fara shirin kwanciya, ta dauka ma Khadija bacci take yi, tana kwanciya taji khadija tace "don't let this get into your head. These things don't last ima jiye miki jin kunya. Gwara ki tsaya a matsayin da Allah ya ajiye ki".

Aisha bata bari maganganun Khadija sun shiga kanta ba, dan haka washegari ta fara aikin ta. Tun daga ranar kullum aikinta shine abincin Senate, da sassafe take fita tayi breakfast a kai musu, sannan tayi lunch shima akai musu. Kullum kara kwarewa take yi akan girki, kullum kara innovating sababbin girkuna take yi, kuma kullum tayi sai an yaba mata. Mama ce ta siya mata babbar waya, babu abinda take yi da ita sai binciken recipe.

Ahaka har aka gama first semester, result ya fito, ga mamakin Aisha sai taga Khadija taci da yawa daga courses dinta guda biyu kawai ta fadi, taji dadi sosai har ranta, ta yadda cewa Khadija da gaske take da tace zata yi karatun ta saka ran nan gaba ma in kanta ya kara budewa sai result din nata yafi haka kyau.

Ana komawa second semester duk suka cigaba da al'amuransu, by now Aisha ta saba sosai da students din da suke zuwa cin abinci gurinsu, dan har zama take yi suyi hira, da yawa daga cikinsu sun san ita take yiwa vc abinci dan har lallabata suke yi ta sammusu in tayi, a cikin su akwai wani Nura, kyakykyawan bafulatani ne mutumin Adamawa. Nura bashi da magana sosai amma sai Allah ya hada jininsa da A'isha musamman da ya fahimci itama bafulatana ce shikenan ya makale mata, kullum in yazo cin abinci baya zama a inda tables suke sai dai ya jawo kujera kan kanta yana ci yana yiwa Aisha hira da fulatanci, tun bata biye masa har ta saba sai ta zauna suyi ta yarawa su Sa'a suna cewa zaginsu suke dan sun san basa ji.

Aisha_HumairahOnde histórias criam vida. Descubra agora