The Price 2

8.8K 1K 193
                                    

I know. Nasan duk hakurin da zanbaku won't make up for zaman jirana da kukayi. Nasan jira akwai cin rai, ko nice aka bari da jira bazan ji dadi ba kuma labarin ma zai iya fita daga kaina, amma ina so ku sani cewa inayin iyakacin kokarina, abubuwa ne yaddaka tsara su ba lallai ne su tafi a haka ba. Kuyi hakuri, insha Allah mun kusa zuwa karshe.

Nasan yadda some of you suke feeling a game da hadin Abbas da Khadija, dan haka na baku dama a karshen episode dinnan ina so kowa ya fada min ra'ayinsa, banda son zuciya please, ku dubi abin da idon basira sannan ku auna da abubuwan da suke faruwa in reality sai kuyi voting, ni kuma nayi muku alkawarin I will go with the highest votes ko da ba haka na tsara labarin ba in dai har nasan message din da nake so in fitar ya fita.

My wattpad followers, ina son ku irin sosai dinnan kuma inajin dadin comments dinku da votes dinku. Bana responding ne saboda inajin kunyar ku, kunyar barinku da nake yi kuna ta jirana kullum. Amma nayi alkawarin in mun gama duk zan biku personally in baku hakuri. Hope za'a yafe min.

Abbas ya cika alkawarinsa, tun rabuwarsu da Khadija bai kira number din data bashi ba amma kuma koda yaushe tana cikin zuciyarsa bai manta da ita ba, kuma yana addu'ar Allah ya kawo dalilin da zai saka ta chanza shawarar ta game dashi, game da aure. He kept himself busy da gyaran gidan babansa, making it as comfortably welcoming as possible amma kuma duk da haka it felt empty, tamkar makabarta.

Wannan ya saka ya fara bin few relatives din baban nasa daya sani yana rokonsu da su zo su dan zauna a gidan, su dan raya gidan amma amsar da yake samu kusan duk daya ce "da sanda yake cin duniyarsa da tsinke bai neme mu ba sai yanzu da cuta ta same shi shine zai neme mu muyi jinyarsa? Ba ruwan mu dashi kamar yadda bama bukatar dukiyarsa" haka ya hakura yabarsu, dama kuma duk faraway cousins ne dan duk da jikin babu su a duniya.

Sai gashi ma ana gobe za'a kawo shi sai Abbas ya samu labarin cewa ba gida za'a kawo shi ba, asibiti za'a wuce dashi saboda yana bukatar support din machines wajan numfashi dan haka dole asibiti zai zauna har sai an yi installing such machines a gidansa sannan zai koma gida. Ranar dazai dawo Abbas ne kadai yaje ya taroshi a airport, ya ganshi anyo wheeling dinsa a wheel chair ga wayoyi duk a jikinsa, yaganshi ya kara tsufa ya motse ya yamushe kamar skeleton, kansa da fuskarsa duk babu gashi saboda chemotherapy, kawai sai Abbas ya ji zuciyarsa ta karye. Ya karasa gabansa ya tsaya amma ya kasa cewa komai.

A hankali ya bude idonsa ya kalle Abbas sai murmushi ya bayyana a fuskarsa yace murya can kasa "ya na ganka kai kadai? Ina take?" Abbas ya durkusa a gabansa yace "zata zo daga baya. I want you to settle down first kafin ta ganka" Yace "wanne settling down zanyi kuma? Ni da nake da kididdigaggen lokaci a duniya?" Abbas ya mike tsaye yana kara jin zafi a zuciyarsa. Me yasa cancer bata da magani? Me yasa aids bata da magani? Me yasa zasu kama tsoho kamar wannan a wannan lokacin? Me yasa kaddararsu tazo a haka? Amma shin kaddarar ce ta kawo su inda suke yanzu ko kuma wani abin ne daban?

Sai da suka kwana biyu a asibiti sannan Abbas yayi summoning courage ya kirawo number din Aisha. Shima kuma ya kira ne saboda naci da baban nasa yake masa dan yau kin amsa gaisuwarsa ma yayi. Bayan ta dauka ya gaisheta cikin mutuntawa sannan ya gaya mata Khadijah yake nema. Aisha tayi mamaki, dan sam bata taba tunanin Khadija zata kula wani har ta bashi number ya kirata ba, amma kuma a wani bangaren na zuciyarta tayi murna sosai, tana ganin kamar wannan alama ce ta cewa Khadija was ready to move on in life, abinda Aisha bata yi tsammani nan kusa ba.

Ta daga murya ta kira Khadijah wadda take daki tana kan keken sakarta. Tana zuwa ta mika mata wayar tace "ana nemanki". Tun kafin Khadija ta karba tasan waye, farko data jishi shiru har ta fara murna ta dauka ya bar maganar saboda sam bata son ta bata masa rai, he seemed like a very nice person, amma kuma ba zata iya yin abinda yake so ba, aure. Yes, zata iya zuwa taga babansa kamar yadda yace amma ba zata iya aurensa ba. Ta samu guri ta zauna ta gaishe shi, ya amsa mata sannan yace "da fatan baki manta dani ba. Sunana Abbas, nine na same ki a dutse mukayi magana. Kin tuna ni?" ta gyada kai kamar yana kallonta tace "na gane ka. Yazo ne?" yace "yazo, shekaran jiya. Ban kira ki ba saboda nayi tunanin kamar abinda zanyi ba dai dai bane ba, kamar yaudara ce, and I don't want to break his heart more in ya gane cewa ba auren zamuyi ba. But he kept insisting, dan haka bani da wani option sai wannan din. Will you come?" ta riga tayi masa alkawarin zataje tun a dutse dan haka she couldn't say no yanzu kuma.

Aisha_HumairahWhere stories live. Discover now