Love, Sweet Love

9.5K 815 26
                                    

Washegari tunda assubar fari mutanen Yola suka dauki hanya, Aisha har ta fara sabawa da sisters din Nura dan haka ta saka sukayi mata alkawarin zasu dawo in sun sami hutun makaranta. Mutanen Kano kuwa sai da gari ya waye sosai sannan suka fara shirin tafiya, nan Aisha ta zauna ta dasa musu kuka wai bata so su tafi, Aunty Fatima yayar Umma da suke uba daya tace "sakarcin banza kenan kike yi ko menene haka? Ba dan gari da nisa ba da yaya zamuyi mu kwana a gidanki ma ballantana har ki samu damar cewa kar mu tafi, to so kike yi mu karkade guri duk kanin mu mu zauna miki zaman daki?".

Aunty Bilki ta jawo Aisha jikinta tace "yaya Fati ai lallabata ya kamata ayi ba fada ba kuma" Aunty Fatima ta dungurewa Aisha kai tace "ai ke ce mai shagwabata shi yasa har take mana wannan iyayin, 'yar kare, ba sai kin kara ganin mu a gidan ki ba ballantana har kice kar mu tafi" Aunty Bilki dai ta zauna rarrashi da nasiha har Aisha ta daina kukan, sai kuma tace "aunty to ki bar min Zahra ta zauna anan, tun da dai babu abinda take yi a gidan" Aunty tace "kiyi hakuri, zata zo amma ba yanzu ba, ki bari sai kin kwana biyu tukunna sannan sai ta tambayi babanta ta taho ta taya ki zama. Yo ke da kike karatu ma wanne zama za'a tayaki? Bayan kullum wuni kike yi a makaranta sai dare. Ki bari sai kun sake wani hutun sai tazo ku zauna tare" ita dai Aisha ta fahimci Aunty hanya hanya take yi mata, bata so ta bar Zahra a gurinta. A bangaren Aunty kuma tana ganin rashin dacewar abin ne, tunda Zahra ba yarinya bace ba dan itama ta isa a aurar da ita, dan haka bai dace tazo gidan yayarta ta zauna ba.

A haka dai suka rabu, Zahra na kuka Aisha na kuka. Nura ne ya dauko musu shatar mota har gida sannan ya dauko kudi masu yawa ya basu yace su sha ruwa a hanya, da suka ki karba ma ajiye musu yayi ta tashi daga gurin. Lokacin da suke shiga mota ne ya lura da kukan da Aisha take yi ya faki ido yayi mata gwalo ita kuma ta harare shi. Suna fita daga gate din gidan Aisha ta juya da sauri ta koma ciki, kafin Nura ya rufe gate har ta shige dakin kasa ta tsaya tana yarfa hannu, tana jin shigowarsa palo tayi sauri ta shige toilet ta turo kofa. Ya shigo dakin yaga bata nan sai ya fita ya hau sama, nan ma ya duba ko'ina bata nan ya kuma saukowa kasa ya koma dakin, har ta bude kofa taji motsinsa ta yi sauri ta koma a lokacin shi kuma yana shigowa ya ga motsin kofa, dariya yayi a ransa yace "au dodo na zama kuma yau?" Ya samu bakin gado ya zauna ya dauko wayarsa yana duba sakonni taya murna da aka turo masa daga wadanda basu samu damar halattar bikin ba, yana karantawa yana reply. Har ya gaji da zama ya jawo pillow ya kwanta, abinka da wanda gajiya dama taci karfinsa nan take sanyin AC da laushin katifa suka debe shi sai bacci. A hankali Aisha ta turo kofar ta leko da kanta, nan ta ganshi kwance da waya a hannu amma idonsa a rufe, ta danyi motsi da kofar da ta tabbatar bacci yake yi amma taga ko motsi baiyi ba.

Ta fito a hankali tana kallonsa nan ta fahimci da gaske baccin yake yi. Haka kawai sai taga ya kara yi mata kyau sosai, fatar sa tana fitar da tsantsar kwanciyar hankali da nutsuwa, fuskarsa fes without emotions. Ta durkusa a gabansa tayi tagumi da hannayenta a jikin gadon tana kallonsa. Itama ji tayi sanyin ACn ya fara ratsata kuma dama jiya ba wani baccin kirki tayi ba saboda kusan kwana sukayi suna hira. A hankali ta fara gyangyadi, tagumin nata ya zame ta kwantar da kanta a kan gadon dai dai saitin fuskar Nura sai bacci ya dauke ta itama.

Cikin bacci Nura yayi juyi sai yaji hannunsa ya taba wani abu, ya kuma shafawa sai yayi sauri ya bude idonsa yana kwallon inda hannun nasa yaje, gabansa ne first ya fadi sai kuma murmushi ya sauka a fuskarsa tunowa da yayi cewa Aisha tare da komai nata halak malak dinsa ce, babu wani abu nata da zai taba ya zama yayi laifi, ya gyara kwanciyarsa yana kallon yadda kirjinta yake hawa yana sauka in tana numfashi, ya dora hannunsa akan gashin kanta wanda ya bayyana sakamakon dankwalinta daya zame, bai taba ganin gashin Aisha ba ko da kuwa silli daya ne duk tsahon shekarun da yayi da sanin ta dan haka sai darajar gashin ya karu sosai a idonsa, ya karasa zame dan kwalin yana mamakin irin cika da tsahon gashin tamkar wadda ta daura attachment din da 'yammatan yanzu suke sakawa, sai dai wannan kana gani kasan daga Allah yake, ya kai hannun sa a hankali ya shafa yaji laushinsa tamkar auduga, ajjiyar zuciya yaji ta sauke amma kuma bata farka ba sai sake dunkule wa da tayi kamar mage. Ya duba agogo yaga lokacin zuhr da saura dan haka ya tashi ya daga ta chak ya dora akan gadon shima ya hau ya jawo blanket ya rufe su, yana lullubesu ta sake matsowa jikinsa, yayi murmushi ya zagaye ta da hannayensa ya saka fuskarsa cikin gashinta yana shakar kamshinta. A haka bacci irin wanda Nura ba zai iya tuna rabon da yayi mai dadin sa ba ya dauke shi.

Aisha_HumairahDonde viven las historias. Descúbrelo ahora