Ansha voting ba laifi. Duk groups din nake ciki na facebook da whatsaap naji ra'ayoyinku kuma na yaba da yadda kowa yake kawo hujjojinsa da zasu yi backing ra'ayinsa. Alhamdulillah, dole a duk inda aka samu sabanin ra'ayi dole wadansu zasu rinjayi wadansu kuma a koda yaushe bature yace majority carry the vote. A whatsaap an samu majority, a facebook ma haka, a wattpad ne zance kusan aka danyi doguwar jayayya amma still shima wasu sun rinjayi wasu. So. Xamu dora daga inda muka tsaya, yadda labarin ya tafi shi zai nuna wa mutane ainahin su waye suka rinjaya.
Na kuma fahimci cewa akwai wadanda suke bukatar a kara yi musu bayani akan haramci ko halaccin hadin Abbas da Khadija, ni ba malama bace ba amma nasha karo da bayanin malamai akan halaccin yin irin wannan auren. Dalili na na farko shine aure bai shiga tsakanin Khadija da Dr ba, dan haka abinda suka aikata haram ne while shi kuma aure da zasuyi da Abbas halal ne. Halal kullum itace gaba da haram, babu ta yadda za'ayi haram ta danne halal. Sannan duk munsan ayar alqu'anin data lissafo matan da suka haramta mumini ya aura kuma a cikin su banga anyi mentioning din matar da uba yayi lalata da ita ba, a karshen ayar kuma akace bayan wadanda aka lissafa duk sauran mata sun halatta. Dalili na biyu kuma shine; shi Abbas ba dan sunna bane ba, shege ne, dan haka islamically bashi da wani hadi da babansa, ba zaiyi gadonsa ba kanar yadda ba zaiyi amfani da sunansa ba. Idan da ace Dr yana da 'ya mace to islamically akwai aure tsakaninta da Abbas ballantana Khadija. Wannan shine abinda na sani. Allahu a'alam. Inda akwai malamai zasu iya yi mana karin bayani dan mu karu. Kuma insha Allah kafin nan kafin mu karkare littafin zan tura tambayar nan zuwa ga malamai magada annabawa dan su bamu hujjoji na ayoyi da hadisai wadanda ni daku gaba daya zamu karu dasu.
Amma kamar yadda wadanda suka nuna rashin amincewarsu da auren Abbas da Khadija suka fada "ana barin halal ko dan kunya".
Har Khadija ta koma gida jikinta bai bar karkarwa ba. Sai data shiga daki sannan ta rufe kanta sannan ta kifa kanta a pillow ta fara zubar da hawayen da take rikewa, ita kanta bata san kukan me take yi ba amma tasan yana da dangantaka da tsoron ubangiji da yake kara shigarta tun sanda ta dora idonta akan Dr. Babu abinda ya gagari Allah. Dan'adam baya taba yiwa Allah yawo saboda shi yake rubuta komai na rayuwarka yasan me kayi a baya ya kuma san me zakayi a gaba.
A wani bangare na jikinta tana jin tamkar wannan wata dama ce da Allah ya bata na ta rama abinda Dr yayi mata sannan kuma ta auri miji na nuna wa sa'a kamar yadda yake mafarkinta a da. Amma kuma sai zuciyartata tunatar da ita cewa wannan mafarki ne na waccan khadijan ba wannan ba, waccan selfish evil khadijan. She is no longer that person kuma she intends to remain this, saboda ta bi waccan hanyar taga ba mai bullewa ba ce ba kuma cike take da kayoyi da sarkakiya. She will do the right thing amma a yanzu bata san menene right thing din ba. Zata yi istikhara, zata nemi zabin ubangiji kuma ta tabbatar zaiyi mata zabin alkhairi daga ita har Abbas din.
Bata kira shi ba kuma shima bai kira taba har dare. Sai da daddare tana cikin yanka wata riga da zata dinkawa humairah sannan ya kira, tana dauka yace "am very sorry Khadija. Gashi munyi alkawari kuma ban cika ba na barki kin shiga ke kadai sannan gashi kinje kin duba mahaifina amma ban kira nayi miki godiya ba ko kuma inji yadda kika je gida ba. Nagode Allah ya saka da khairan" tace "ameen. Babu komai" yace "abinda yasa ban samu na kira ki ba, bayan kin bar asibiti dazu, something terrible happened to my father. He had a cardiac arrest" ta lumshe idonta tana jiran taji yace Allah yayi masa rasuwa sai taji yace "da kyar doctors suka shawo kan matsalar. He is stable now" ta bude idonta tace "Allah sarki, Allah ya bashi lfy" yace "ameen. Nagode sosai" suka sake yin shiru, Khadija tana jin babu dadi a ranta. Yace "ina tausayin bawan Allahn nan sosai Khadija. Na taba gaya miki kuwa cewa bashi da kowa a duniya sai ni? Gabaki daya rayuwarsa yayi tane cikin kadaici da rashin kulawa a bisa wani kuskure da ya aikata a zamanin yarintarsa, he is a good man, shi yasa wani lokacin sai inyi ta jin a raina tamkar baiyi deserving rayuwar da yake ciki ba, amma nasan hakan shine yadda ubangiji ya tsara masa kuma Allah is all knowing and the most wise." Bata ce komai ba amma zuciyarta tayi mata nauyi sosai. So, Dr has been lying to his son kenan, yana nuna masa shi na Allah ne. Lallai ubangiji shi yake fitar da kyakykyawa daga mummuna, jin tayi shiru ya cigaba "tun daya farka yake tambaya ta ke. It is like he wants to know ya muke ciki dake akan maganar aure. Saura kadan in gaya masa cewa babu maganar aure a tsakanin mu dan kinki karba ta amma kuma sai na kasa, na rasa wanne zan dauka, ina jin babu dadi saboda karyar da nake masa sannan kuma i don't want to break his heart in na gaya masa gaskiya. I don't know what to do Khadija, nima ina son inyi auren nan amma na kasayi saboda wani dalili sannan kuma ban taba jin wata mace tayi min a matsayin matar aure ba sai ke, ke kuma kince a'a, ya kamata ki daure ki bani dama muyi magana ta fahimtar juna. Ki fahimce ni dan Allah, babu sharri a tare dani sai alkhairi" taji hawayen tausayinsa ya zubo mata, ta bude baki da kyar tace "wannan shi yasa nace bazan aure ka ba Abbas. You are too good for me. Alkhairi ne a tare da kai ni kuma sharri ne yake ta bibiyata a duk inda nake, you are too pure, too innocent" sai kawai taji yayi 'yar karamar dariya yace "you are wrong. I am neither pure nor innocent, in fact, zan iyace miki i am dirty. Dirtier than koma menene kike ganin yayi staining rayuwarki" tace "you won't understand maganar da nake yi maka. Ka bar maganar kawai kamar yadda hausawa suke cewa a bar kaza a cikin gashinta saboda sometimes fige ta din babu alkhairi a cikinsa" yace "inji wa? Ta yaya za'ayi enjoying kazar in tana cikin gashinta? I told you already ni ban damu da koma menene a past din ki ba amma in kin gaya min shikenan, ni future nake so mu gina tare ni dake in kin amince, amma nafi son ki san koni wanene kafin mu saka foundation din komai. Ki bani dama, dan Allah, ki bani dama inzo inda kike muyi magana" a hankali ta zare wayar daga kunnenta ta ajiye a gefe sannan ta kashe. Ba zata iya cigaba da sauraron sa ba kamar yadda bata san amsar da zata bashi ba. Bai sake kira ba shima.
ESTÁS LEYENDO
Aisha_Humairah
FanfictionIt is a story about two sisters that are like the two sides of a coin, totally different yet part of each other. It is a story about loneliness, sadness, discrimination, hypocrisy, self pity and of course love. Get your handkerchiefs ready because t...
