Bugu daya ya dauka. Suka gaisa suka dan taba hira yana bata labarin abubuwan da suka faru zuwansa kano, sannan ya tambaye ta, "to ya kuke ku kuma? Kin raka Mami taron?" Tayi ajjiyar zuciya sannan ta bashi labarin yadda taron ya kasance da kuma ganin da tayi wa Humairah da abubuwan data fahimta ta kuma ji daga bakin Mami da director dangane da yarinyar. Sannan ta dora da cewa "Nayi mana adopting dinta Hubby, na taho da ita gida yanzu haka. Nasan I should have contacted you kafin in yanke hukunci amma nima bansan me yazo kaina ba, ina jin yarinyar har cikin raina naji cewa bazan iya barin gurin ba tare da ita ba. Nasan nayi ba dai dai ba, kayi hakuri please"
Wayar taji ya katse gaba daya, ta tsaya saroro tana kallon wayar a hannunta tana jin kuma babu dadi a zuciyarta. Tunda suke da Nura basu taba samun major problem ba, sai dai few marital issues da ba za'a rasa ba, bata son su fara yanzu, bata son su fara saboda Humairah. Ta sake kiran wayarsa amma bai dauka ba, ta tabbatar yayi fushi da ita kuma tasan itace mai laifi. Ta tura masa message mai dauke da kalamai masu dadi na ban hakuri "dan Allah Hubby kayi hakuri, please kar ka yi fushi dani, kayi min komai ma amma dan Allah kar kayi fushi dani dan zuciyata ba zata dauka ba" babu reply, dan haka ta mike jiki babu kwari ta hau sama dakinsu tayi alwala tayi sallah ta nemi taimakon ubangiji sannan ta sake kiran number din Nura, wannan karon ya dauka amma bai yi mata magana ba, tace "dan Allah hubby kayi hakuri, ban san ka da yin fushi da Wifey dinka ba fa, tayi laifi amma ta durkusa akan gwuiwowinta tana neman afuwa, please a yafe min. Nayi maka alkawarin in har kazo kaga yarinyar nan na kuma baka cikakken labarinta da aka bani na tabbatar kai da kanka zaka yarda mu rike ta, in kuma baka yarda ba wallahi da kaina zan dauke ta in mayar da ita inda na dauko ta indai hakan zai saka farin ciki" sai lokacin yayi magana "in yaso Mami tace ni ne naki karbar yarinyar ko? Ai tun ranar gini ake yin zane ba wai sai daga baya ba. Tun kafin kiyi signing takardar karbar responsibilities dinta ya kamata ace kinyi excusing kanki waje kin kirani munyi maganar tukunna, ba wai sai da kika dauko ta kika kawo ta gida ba" tace "lokacin Hubby na san kana lecture, you might not be able to pick..." Ya katseta "tunda muke kin taba kirana ban dauka ba saboda ina busy? Duk inda nake, ko menene nakeyi Aisha my family always comes first, babu wani abu da zai hanani daukan waya daga gareki in dai tana hannuna, wannan shi yasa ko silent bana saka waya ta ko da kuwa ina meetings ne" tayi shiru bata ce komai ba, ya cigaba "ba wai dauko yarinyar ne ya bata min rai ba, ba kuma yarinyar ce bana so ba, the fact that kin dauko ta ba tare da amincewa ta ba shine abinda ya bata min rai, har zaki iya yanke hukunci of this magnitude ba tare da kin ji ra'ayina ba first" a hankali tace "Allah ya huci zuciyarka Allah ya baka hakuri" sun jima shiru a haka sannan yace "inna dawo goben zan ganta, sai kuma muyi magana akanta, zan koma can orphanage din in binciki file din nata sosai sannan kuma mu san educational status dinta dan musan yadda zamuyi da karatun ta"
Aisha tayi murmushin jin dadi tace "Nagode, Hubby, am sure you will like her in ka ganta, she is fulani and" ya katse ta da cewa "ina yarana? Ni banji hayaniya ba shiru nake ji a kusa dake" nan kuma sai hirar ta koma kan twins dinsu, a haka har ta sauko kasa ta kira su ta basu wayar suka sa a hands free suna ta mishi surutu yana biye musu.
Washegari Aisha ta tashi tayi sallar asuba ta fita da niyyar tashin Humairah kafin ta sauka kasa gurin twins, amma ga mamakinta tana shiga dakin sai ta tarar da ita zaune akan sallaya tana karatun alqur'ani, ta jima a tsaye tana kallonta tana mamakin irin yadda take karatun cikin nutsuwa da tsari da kira'a mai kyau, a ina yarinyar nan ta samu background din karatu haka? Tana tsaye har ta kai karshen surar da take karantawa ta rufe qur'anin ta juyo cikin sanyin murya tace "ina kwana?" Aisha ta karaso cikin dakin fuskarta da murmushi tace "ashe malama muka samu ni ban sani ba? Anya ba zan fara daukan karatu a gurin ki ba?" Humairah tayi murmushi ta sunkuyar da kanta tana wasa da carpet din dakin, a lokacin ne Aisha ta lura da jakar kayan Humairah tana nan yadda aka ajiye ta jiya ko bude ta ba tai ba, kayan da tazo dasu a jikinta sune dai ajikin nata har hijab din, da alama ma dasu tayi bacci bata chanza ba, ta ce "ya na ga kamar tun jiya baki chanza kaya ba? Ko baki da kayan sakawa?" Da sauri ta girgiza mata kanta, Aisha tace "bude jakar taki to inga ni" Humairah ta jawo jakar a hankali ta bude ta fara fito da kayan ciki. Akwai kayan sakawa, some of them masu kyau wadansu kuma sun tsufa, sai dai dukkansu a wanke suke tas a goge, babu wari ko kadan a tare dasu, nan Aisha ta ware mata wadansu ta ce ta bude wardrobe din dakin ta zuba a ciki, sauran kuma ta dauke su ta fita dasu tace bayarwa za'ayi. Bata jima ba ta dawo da 'yar karamar jaka a hannunta, toiletries ne a ciki da sauran kayan amfanin yau da gobe, ta ce da Humairah ta tabbatar ta shi yanzu tayi wanka ta chanza kaya sannan ta sauko kasa suyi breakfast tare kafin ita da yara su fita, ta gaya mata kuma ta shirya in ta dawo daga office zasu je siyayyar kayan sawarta da under wears. Har ta gama jawabinta Humairah tana nan durkushe a kan carpet da kaya a gabanta, sai da Aisha ta fita sannan ta bi kofar da kallo a ranta tace "ni da ba dadewa zanyi ba ina ni ina wani saka kaya a wardrobe. The ladies are always nice, sai mazan sun shigo cikin picture din sannan lamarin yake watsewa.
YOU ARE READING
Aisha_Humairah
FanfictionIt is a story about two sisters that are like the two sides of a coin, totally different yet part of each other. It is a story about loneliness, sadness, discrimination, hypocrisy, self pity and of course love. Get your handkerchiefs ready because t...