The Cook and the Student

8.9K 786 5
                                    

Har bayan kwana uku Umma tana ta tunanin maganganun aminiyar tata, bata son Aishan taga kamar basa santa ne ya saka zasu tura ta aiki a gurin siyar da abinci, saboda mutanen mu suna yiwa duk mai harkar sayar da abinci wani kallo na daban, amma ita tasan Mama tana daga cikin mutane masu ruko da akidar musulunci sosai, dan tasan ko ita ba zata gaya mata addini ba, kuma tasan yadda 'ya'yanta suke da tarbiyya.

A rana ta ukun ne dai ta daure ta gaya wa Abba shawarar da suka yi da Mama. Tayi shiru tana jiran taji ta ina zai fara yi mata fadan zata mayar masa da 'ya kamar 'yar talla, amma ga mamakin ta sai taji yace "in dai hakan zai taimaka mata wajan samun mijin aure na amince ta fara zuwa ɗin" sai kuma Umma taji babu dadi, taso ya ɗanyi mata fada ko yayane ya nuna mata ya damu da 'yar tasa, amma sai ta fahimci cewa abinda yafi damuwa dashi shine ta samu mijin aure, tace "ai ba zancen mijin aure bama Alhaji, yadda zata koyi shiga mutane itama ta ke jin dadin rayuwa irin na sauran mutane shi muke nema mata"

Ya ɓata rai yace "ku mata karamar ƙwaƙwalwa ne daku, wanne irin jin dadin rayuwa kuma? Wanne irin shiga mutane kuma kike so ta koya, me ya rage a rayuwar Aisha kuma in banda muyi ta mata addu'a ta samu miji tayi aure? Ke kullum ana nuna miki annabi kina runtse ido. Akwai wani jin daɗi ga mace da ya wuce dakin mijinta?" ya tashi ya dauki hularsa ya saka ya fice.

Duk ran Umma yayi mata babu dadi ta rasa sanin in abinda take yi dai dai ne ko ba dai dai bane ba, tana neman shawara. Ta dauki wayarta ta kira sister dinta Bilkisu, wacce take aure a kano unguwar gwauron dutse, aunty Bilki tana da zafi sosai, dan haka itama tafi shiri da Aisha akan Khadija. Tana ɗauka suka gaisa cikin raha kowa yana tambayar lafiyar iyalin kowa. Umma tace "Bilkisu shawara nake nema" Aunty Bilki tace "ina jinki yaya" nan Umma ta bata labarin duk halin da ake ciki da kuma amsar da ta samu daga maigidan nata.

Sun jima suna tattauna maganar, suna lissafa good sides da bad sides din aikin da Aisha zata fara zuwa, a karshe dai suka ga cewa the good outweigh the bad, dan suna ganin Aisha tana da tarbiyya sosai da kuma kamun kai, dan haka da wahala a samu gurɓacewar tarbiyyarta wanda hakan shine bad side ɗin da sukayi considering, maganar mutane sun ajiyeta a gefe tunda dai duk abinda zakayi ba zaka taɓa yiwa mutane dai dai ba.

Da wannan shawarar Umma ta kwana, washegari suna breakfast tayi breaking news din tace "Aisha ina son zaki fara bin Khadija makaranta, zaki ke zama a gurin Mama kina taya ta aiyuka a cafeteria, da yamma sai ki dawo gida". Aisha jin maganar tayi wani iri, ta kasa yanke hukuncin me take ji a ranta, Khadija ce tayi retaliating, ta ajiye chokalin hannunta tace "Umma? Me kike cewa? Aikatau zaku tura Aisha cafeteria?" Abba ya hade rai yace "waye yace miki aikatau zata yi? Kinji ance za'a ke biyan ta kudi ne ko makamancin haka? Zuwa zata ke yi kawai saboda ta rage zaman gida"

Nan take hawaye ya taru a idon Khadija, tace "gaskiya ni dai ba'ayi min adalci ba, wannan ai zubar min da class ɗina za'a yi, kawai kuma muna tare da friends ɗina sai kuma ace ga sister ta can tana siyar da abinci a cafeteria? Da wanne idon zan kalli 'yan ajin mu?"

Wani haushi ne ya kama Aisha, Khadija tana da son kanta da yawa, she cares about no one but herself, kawai sai ta samu kanta da cewa "Umma na yarda zanke zuwa, zan fara daga gobe" da sauri Khadija ta mike ta turo baki tana bubbuga kafa ta shige daki, Umma tayi ajjiyar zuciya tace "Allah ya shirya min ke Khadija" Abba kuma yi yayi kamar baisan me suke yi ba.

Washegari kamar yadda Aisha ta saba tashi da assuba haka ta tashi, cikin sauri ta fara aiyukan gida, tayi shara tayi mopping ta shiga kitchen ta dama kunu ta fere doya ta dora sannan ta koma daki da sauri tayi wanka ta dawo kitchen ta fara soya doyar sai ga Umma tazo ta karba tana karasawa ita kuma ta koma daki ta shirya, sai a lokacin Khadija ta tashi, tana ta faman ɓata fuska ta shiga wanka. Sai da suka gama breakfast sannan ta fito, ta ci kwalliya kamar mai zuwa gidan biki, amma ta zura dogon hijab har kasa, tana bude kwanon abincin tayi tsaki, "jiya naci doya yau ma ace doyar zanci?" Umma tace "uban wa yace kar ki tashi ki dafa abinda kike so? Kina bacci aka dafa miki abinci maimakon kice kin gode sai kiyi complain?". Khadija kunu kawai tasha, Abba ya dauko dari biyar ya bata yace ta ci abinci a makaranta, ba kunya ba tsoron Allah ta karbe duk kuwa da cewa jakarta fal take da kudin samari. Abba yana gamawa yace su tashi ya ajiye su ya wuce gurin aiki, da sauri Aisha ta shiga daki, minti biyu sai gata ta fito, duk suka saki baki suna kallonta, hijab ne a jikinta itama dogo, amma ba shi ne abin mamakin ba, nikab ne a daure a fuskarta, babu abinda kake gani sai idanuwanta, ta tsaya tace " Abba na fito" Umma tayi ajjiyar zuciya.

Sai a lokacin Khadija ta dan saki fuskarta, taji dadin saka nikab din da Aisha tayi saboda tasan babu wanda zai ganeta ballantana ya dangantata da ita.

Tunda aka sauke su a bakin gate kowa ta kama hanyar ta, Aisha tayi hanyar cafeteria Khadija kuma tayi hanyar hostel.

A haka rayuwa ta cigaba da tafiyar musu, kullum zasu fita tare amma suna shiga kowa zai kama gabansa. Da farko Aisha ta fara zuwa gurin Mama ne kawai saboda Umma tace mata taje, kuma ba zata iya yi mata musu ba, a hankali kuma sai ta fara jin dadin abin, dan sosai Mama take janta a jikinta, Sa'a da Binta kuma sun zama tamkar kannenta, sosai take jin dadin aiki a gurin musamman saboda soyayyar ta da girki, in ta shiga tun safe suka fara abinci bata tafiya gida sai karfe biyar, shima Mama ce take cewa ta tafi gida bawai dan sun gama aiki ba ko kuma dan ta gaji ba.

Zamanta a gurin ya saka ta kara ƙwarewa a harkar girki, dan yanzu ta iya dishes na different tribes, duk girkin kuma da aka koyawa Aisha in tayi sai kaji yafi na wanda ya koya mata din ma daɗi saboda ita bata cewa lallai ka'ida kaza zata bi, tana mayar da girki ne tamkar practical, in ta gwada waccan hanyar sau ta sake gwadawa ta waccan dan taga wacce zata fi.

Amma har yau bata iya bude fuskarta, kullum da nikab take zuwa kuma har ta tafi bata cire shi duk kuwa da mitar da Mama ta kanyi mata cikin wasa. Yanayin cafeteria din hall ne madaidaici, da tables da kujeru a jere, sai doguwar kanta a karshe, inda tanan ake bada order ɗin abinci, ɗan corridor ne a bayan kantar, a hannun damansa kitchen ne, sai hannun hagu kuma daki ne mai hade da toilet inda su Aisha suke zama su huta kuma suyi sallah.

Sosai Aisha ta fara sabawa da regular customers ɗinsu, har wasa suke yi da dariya, yawancinsu sun san ƙwarewar Aisha akan harkar girkin dan haka in sunzo sai suyi ta nemanta, ayi ta wasa da dariya da su Binta suna cewa suma sun iya abincin ai. Amma duk da haka Aisha bata cire nikab dinta ba, har yanzu ta kasa samun confidence ɗin facing mutane da fuskarta, gani take suna ganin cewa ita ba kyakykyawa bace ba zasu fara ƙyamarta. Ta riga ta saka a ranta cewa ita bata da kyau kuma mutane sunfi son kyakykyawa.

Khadija sam bata zuwa cafeteria din da Aisha take aiki, dan bata son abinda zai dangantata da ita. Wannan ya saka sam basu taba haduwa a cikin makaranta ba, in sun rabu a bakin gate sai dai kuma in sun koma gida suke sake haduwa.
Wata rana su Aisha suna cikin aikinsu sai ga order daga office din vc, emergency ana bukatar abinci za'a kaiwa baƙin vc, ba tare da shakkar komai ba Mama ta ce Aisha ta hada abincin, nan take Aisha ta kira su Binta dan suzo su taya ta haɗawa.

Ta bud'e freezer din su ta tabbatar tana da duk abinda take bu'kata. Ta yanke shawarar zatayi grilled catfish, buttered macaroni da kuma coconut kisses as appetizer. Farko suka yanka cabbage da carrots da albasa da attaruhu, yanka mai kyau. Ta dauko katon catfish ta wanke ta cire kayan ciki. Ta debo yankakkun attaruhu tumatir tafarnuwa da albasa ta zuba a tukunya ta zuba ruwa dan kadan ta rufe, sai ta yayi laushi sannan ta bude ta zuba gishiri dan kadan da maggi, ta saka mai kadan ta dan soya masa masa. Ta dauko kifin da ta wanke ta dan tsaga samanshi da kasanshi yadda kayan hadin zasu ratsa shi. Ta samu karamin bowl ta hada sinadaran dandanon ta da spices din duk da take buƙata. Daga nan sai ta dora kifinta akan foil paper ta barbadeshi da wannan hadin da kuma souce din attaruhun ta tayi, ta tabbatar ko ina ya samu sannan ta nannade foil paper din ta saka shi a oven din da ta riga tayi pre heating.

Daga nan sai ta koma kan macaronin ta, tafasa daya tayi mata ta tace ta ta ajiye. Ta debi yankakkun wankakkun cabbage, carrots, green beans, peas ta tafasa su, tafasa daya, ta tace ta ajiye. Ta tafasa kwai shima ta yayyanka kanana ta ajiye. Dama suna da tafashashshen nama, shima ta dauko ta yayyanka kanana ta ajiye. Ta dora empty tukunya akan wuta ta zuba butter mai yawa a ciki, sannan ta zuba yankakkiyar albasar ta mai yawa tare da attaruhu da kayan 'kamshi a ciki, ta ringa juyawa har sai da albasar tayi brown sannan ta dauko yankakkun kayan lambun nan da nama da kwai duk ta zuba a ciki, tayi ta soya su a tare har sai da suka hade jikin su sannan ta zuba ruwan nama kadan akai, ta zuba gishiri da maggi da curry. Sannan ta kawo tafasashshiyar macaronin ta ta zuba a ciki ta juya ta rufe. Minti biyar ta kara juyawa ta sauke. A lokacin ta duba kifinta shima taga yayi sai ta sauke.

Daga nan sai ta dauko kwai guda hudu ta fasa a bowl, ta cire kwanduwar ta ajiye a gefe, ta zuba gishiri kadan sugar kadan, ka rinka kadawa har sai da taga ya narke yayi ruwa sosai sannan ta dauko gogaggiyar coconut ta zuba akan kwan ta juya har ya hade jikinsa. Ta saka tea spoon ta ringa jerawa akan farantin gashi sannan ta saka a oven ta barshi 5 minutes sannan ta sauke.

Tana gamawa ta hada komai ta jera ta bayar aka kai Senate building inda office din vc yake. Hatta Mama sai da tayi mamakin dadin abincin. Tace "Aisha Allah yayi miki baiwa, kuma insha Allah wannan baiwar zata kaiki inda baki taba tsammani ba".

Aisha_HumairahDonde viven las historias. Descúbrelo ahora