Emotions Aisha taji yana shigarta, the likes of which she has never known. Tunda take babu wanda ya taba yaba wa kamanninta, ko da a cikin mata ne kuwa ballanta namiji, namijin ma kuma as handsome and as fit as Kamal. Ta sunkuyar da kanta kasa tana jin kamar hawaye yana taruwa a idonta, ko da haka Kamal ya barta ya gama mata komai, ko da just appreciation din ya bar ta ya gama mata komai.
Appreciation abu ne mai muhimmanci sosai a dangantaka, dangantaka ta aure ko ƙawance ko saurayi da budurwa ko tsakanin 'ya da uwa ko d'a. In kawarki ta sayi sabuwar jaka misali, in ta nuna miki, ko da kuwa jakar bata yi miki ba, please kar ki kushe mata, kice "kai jakar nan taki tayi kyau, gashi tayi matching da kayanki" idan mijinki ya siyo wani abu ya kawo miki, ko da kuwa abin bai yi miki kyau ba, ki ce "amma baban Maama wannan atamfar daka siyo min tayi kyau sosai, dama ina ta ganin irin ta ina sha'awa, nagode Allah ya kara budi ya kuma raya mana zuri'ah" idan matarka tayi wanka tayi kwalliya "masha Allah, ni kullum kara kyau kike yi" ko da kuwa ba kara kyau din take yi ba.
Yabo yana kara wa mutane kwarin guiwa, kushe kuma yana sacewa mutane guiwar su, in ya siyo miki kaya kika kushe su ba lallai ne gobe in yaga wadansu ya siyo miki ba, idan wanda ya siyo yau basu yi miki ba na gobe maybe zasuyi miki. Ko 'ya'yanki ne suka yi abu ki ringa yaba musu, abinda basuyi dai dai ba sai ki gyara musu ba tare da kin kushe wanda suka yi ba. Dan Allah mu ke kokarin yaba wa junan mu, you have no idea how much a simple "you look beautiful today"can mean to someone.
A hankali Aisha tace "thank you" yayi dariya mai sauti yace "wai kunyata kike ji ne naga kina ta wani sunkuyar da kai? Ko fuskar ce ba kya so inyi ta kallo ina jin dadi?" Ta ja mayafinta ta sake rufe fuskarta, tace "dama haka kake da surutu? You don't look like mai surutu" yace "and am not, bani da magana sosai, amma ke kike saka ni, i don't know why I always want to talk to you, ji nake kamar mu zauna in yi ta baki labarina har sai kinsan komai game dani, kema kuma ina so ki bani labarinki har sai na san komai a kan ki" tace "ni bani da wani labari ai, there is nothing to tell, I am me and that's all" yace "no, ban yarda ba, wayo kike so kiyi min, kowa da kika gani a duniya have a story to tell. Irin labarin yadda kuke da siblings dinki, rayuwar makarantarki da kawayenki, samarinki da dai sauransu"
Tayi shiru tana lissafin duk abinda ya lissafa bata da ko daya. Bata da siblings din sai Khadija, which equals to zero, bata da kawaye ballantana samari, kawarta daya Umma, sai kuma Nura.
A lokacin suka karaso kofar gidan su, ta sauko shima ya fito, yana kallonta yace "naga gida, yanzu kuma ina neman a bani izni inke zuwa muna gaisawa" bata ce komai ba yace "ko ba kya so inzo?" Tayi saurin girgiza kanta tace "bance haka ba, you are always welcome" yayi godiya yayi mata sallama ya koma adaidaita sahu suka tafi.
Ta jima a tsaye a gurin, a ranta tace "what just happened? Me yake shirin faruwa ne ni Aisha? What am I getting myself into?" Amma babu mai bata amsoshin tambayoyinta dan haka ta juya ta shige gida. Tana shiga gidan gwoggo ta fara yi mata fadan taje tayi zamanta bata dawo da wuri ba, ita kuwa ko a jikinta, dan yau yadda take jin zuciyarta fari kal kamar takarda, bata jin akwai wani abu da zai bata mata rai.
Kwana biyu bayan nan. Aisha tayi lecture da safe ta safi cafeteria tana aiki kafin yamma kuma ta sake wata lecture din. Tana cikin aikin Kamal ya shigo, tana sallamar wasu, sai daya bari ta gama sallamarsu sannan ya matso, tayi kamar bata ganshi ba, yace "Humairah" batare data kalleshi ba ta amsa, yace "Kamal ne" tace "I know" yace "I know you know, kawai ina son inji dalilin da yasa kike ja min aji da yawa haka, jiya fa ina nan ina jiran ki gama muyi magana kawai sai ce min aka yi har kin tafi, na rasa me yasa kike ture ni ne ba tare da kin bani dama kin sanni ba" bata bashi amsa ba, sai ta juya ta shiga cikin kitchen, ta rike kanta tana jin wani iri a zuciyarta, tabbas ta san one day one time, Allah zai kawo mata miji, amma ba irin wannan ba, dai dai ruwa dai dai tsaki, wannan ba kalar ta bane ba, he will end up breaking her heart, wannan kalar irin su Khadija ne.
VOUS LISEZ
Aisha_Humairah
FanfictionIt is a story about two sisters that are like the two sides of a coin, totally different yet part of each other. It is a story about loneliness, sadness, discrimination, hypocrisy, self pity and of course love. Get your handkerchiefs ready because t...