The Strange Girl

8.1K 737 24
                                    


Mami tabi hawayen nata da kallo, sannan ta juya ta kalli director tace "She is crying, why is she crying? Me akayi mata?" Director ta bude hannayenta tace "ban sani ba Mami, tun jiya da aka gaya musu zancen taron nan yarinyar nan take kuka, babu irin tambayar da banyi mata ba amma kinsan halinta duk tambayar da zaka yi mata ba zata taba baka amsa ba. As far as I know babu abinda akayi mata"

Mami ta jawo kujerar ta kusa da Humairah tace "Humairah me akayi miki? Wani ne yayi miki wani abu?" Amma maimakon ta bude baki ta bada amsa sai kara dunkule wa tayi a guri daya ta rufe fuskarta da gefen hijab dinta. Duk abinda suke yi Aisha da Basma suna kallonsu amma basu tanka musu ba. Mami tayi ajjiyar zuciya ta dafe goshinta tana kallon Humairah tace "Humairah, what do I do with you?" Aisha tayi gyaran murya tace "menene problem dinta ne wai? Me yasa ake dawo da ita in an dauke ta?"

Director ta mike ta dauko file a cikin cabinet ta zauna ta bude ta fara flipping through the pages tana karantowa Aisha comments din da ake samu daga adoptive parents din Humairah "strange child" "bad language" "lack manners" "bad upbringing" "mentally disturbed" da sauri Aisha tace "is she? I mean is she mentally disturbed" Mami ta girgiza kanta tace "I don't think so, a ka'ida duk yaron da aka kawo sai mun kaishi clinic anyi masa medical check up, sai mun duba mental well being dinsa kafin mu dauke shi, idan munga yaro yana da matsalar kwakwalwa mostly muna kokarin binciko iyayensa ne saboda masu tabin hankali suna bata ne ba wai ana yar dasu bane ba. Humairah bata da mental problem sam" Aisha tace "but there must be something, haka kawai ba za ake daukan ta ana dawowa da ita ba" ta juya gurin director tace "ku anan baku lura da wani behavior nata marar kyau da zai saka ake dawo muku da ita ba? Ni dai as far as I can see yanzu abinda nake gani a gabana shine innocent well mannered girl" director ta danyi murmushi tace "baki san Humairah bane ba, macijiya ce, kyau ne da ita amma kuma akwai harbi. Tun da aka kawo ta dama bata da mate a gidan nan. Ita kadai take al'amuranta babu wanda take kulawa babu wanda take yi wa magana. In an bata abinci zata dauka automatically taci, in an saka ta chores zata yi babu musu, amma problem dinta daya ne bata son ayi mata magana ballantana tambaya, kana fara mata tambaya zata fara maka kuka kuma komai abinka ba zata baka amsa ba. Problem dinta na biyu bata son maza, duk inda ta ga namiji a guri to yadda kika san me aljanu haka take behaving. Yanzu ma kukan da take yi tun jiya am guessing sabida tasan maza zasu zo gurin taron nan ne".

Mami ta katse ta da cewa "then that must mean something. Check her file, maybe da akwai wani abu da zai kara mana haske" director ta bude front page din file ta karanta a fili "Humairah Mahmud. Girl. 12 years old. Mother dead. Father unknown. No known relatives" Aisha tace "a ina aka same ta first?" Director ta rufe file din fuskarta cike da tausayi tana kallon Humairah tace "a kwance a kan kwali a karkashin gada a lagos" Aisha ta runshe idonta tana jin kamar zata yi kuka amma ta mayar da hawayen, ta bude idonta ta sauke akan Humairah wadda yanzu ta daina kukan sai ajjiyar zuciya tana wasa da bakin hijab dinta, Aisha ta lura su Mami ma duk Humairan suke kallo.

She is beautiful, very beautiful. Fatar ta fara ce tas kamar ka taba jini ya fito. Fuskarta 'yar karama zagayayyiya, idanuwanta dara dara masu yalwatacciyar gashin ido wanda a yanzu yake jike da hawaye, hancinta dogo da yazo har kusa da siraran jajayen lips dinta, daga saman hijab dinta Aisha tana iya hango kwanraccen gashin da ya nannade har kusan rabin goshinta sannan ya zagaya zuwa sides din kunnuwanta. She has the face of a baby but the body of a full grown woman.

Muryar Mami ce ta dawo da Aisha daga tunanin ta, tace "then that must explain her fear of men. Babu yadda za'a ce kyakkyawar budurwa kamar wannan tayi rayuwa a kasan gadar lagos with out being sexually harassed" Aisha tace a hankali "bafulatana ce, me ya kai yarinyar fulani kasan gadar lagos?" Mami itama cikin jimamin abin tace "kin san mutanen mu, am guessing iyayen sunje Lagos din ne neman kudi kuma sukayi zaman su acan har suka daina contacting 'yan'uwan su, maybe shi yasa bata san danginta ba, maybe kuma uban ya mutu kafin a haifeta shi yasa shima bata san shi ba. They left the poor child all alone in a strange land" Aisha ta gyada kai, story din Mami sound convincing. Maybe, just maybe.

Aisha_HumairahWhere stories live. Discover now