Khausar

7.9K 671 10
                                    

A ranar kusan mutane hudu ne basu samu cikakken bacci ba a gidan. Na farkon su Al'ameen. Tunda ya shiga dakinsa har yayi wanka ya kwanta yana tunanin maganganun da sukayi da Humairah a ransa, ya maimaita conversations dinsu a kansa har ba adadi, and the more he thought about it the more yake kara jin son aurenta. A lokacin daya kwanta da niyyar yin bacci kuwa baccin kin zuwa yayi, lokacin da yazo kuma sai yazo masa da mugayen mafarkai, in yayi mafarkin Humairah as she was attacked by Mr Ojo, sai ya farka a tsorace, in ya koma baccin kuma sai ya yi mafarkinta tana bin bola tana tsintar abinci. Next baccin kuma sai ya ganta a kwance a kan kwali tana makyarkyatar zazzabi tana kiran sunansa. It went on and on dole ya hakura da baccin dan har an fara kiraye kirayen sallah. Ya tashi yayi alwala ya saka kayansa ya fita masallaci.

Humairah tana shiga dakin da Aisha take ta tarar da ita a zaune a bakin gado da waya a hannu, fuskarta cike da tsananin damuwa. Tana shiga ta tashi da sauri ta rungume ta tana sauke ajjiyar zuciya sannan kuma ta sake ta ta fara jero tambayar "daga ina kike? 'Bata kika yi? Wani abin ya same ki? Tell me" Humairah ta sunkuyar da idonta kasa tana jin babu dadi a ranta, tana jin bata kyauta wa Aishan ba da har ta shagala da magana da Al'ameeñ ta manta yadda Aisha ta damu da ita.

Tace "babu abinda ya sameni. Kiyi hakuri ban san dare yayi har haka ba" Aisha tace "to daga ina kike?" Tace "muna tare da Ya Ameen, muna ta magana dashi bamu san dare yayi ba. Kiyi hakuri Aunty Aisha" Aisha ta koma ta zauna a bakin gado tana kallon Humairan, sai kuma ta sunkuyar da kanta kasa tana tunani, Al'ameen? Tasan Al'ameen tun yana yaro, tasan irin upbringing dinsa amma hakan ba yana nufin ta yarda dashi 100% ba, he shouldn't have kept Humairah with him for this long, amma kuma ba zata iya accusing dinsa ba because of his family, familyn sa sunyi mata komai a rayuwa. She will investigate menene a tsakaninsa da Humairah amma ba yanzu ba, ba cikin taron biki ba. Later.

Mami bayan sun rabu da Al'ameen direct dakin Daddy ta tafi, tana jin wani iri a ranta. Who is that girl? Really who is she? How can she change Al'ameen a cikin awanni kadan? Me ta gaya masa? Me tayi masa? Ita dai a iyakacin sanin ta Al'ameen bai taba boye mata wani abu ba, ko laifi yayi in dai ta tambayeshi to zai gaya mata gaskiya, wani abun ma bata tambayeshi ba haka kawai zai zauna yayi ta bata labaran abubuwan da yayi daga nan ita kuma sai ta bashi shawara mai kyau. Amma yau direct yace ba zai gaya mata labarin Humairah ba, why? And then he said he wants to marry her. Marry her? Ita tasan shi kansa Al'ameen yasan abinda ya fada din is near impossible amma still ya fada with so much confidence. Look din data gani a fuskarsa shine yafi komai tayar mata da hankali. He looked dead serious. She must investigate yarinyar nan. Amma ba yanzu ba. Later. Haka ta kwanta tayi ta juyi ta kasa bacci, ga tunanin rabuwa da 'yar guda dayan 'yarta gobe, ga kuma wannan sabuwar maganar ta Al'ameen. A haka har Daddyn su Al'ameen ya farka yana tambayarta abinda ya hana ta bacci, bata son tayar masa da hankali cikin daren nan dan haka ta gaya masa cewa gajiya tayi da yawa. Da kansa ya tashi ya dauko mata paracetamol tare da ruwa da maganin bacci bayan tasha kuma ya tabbatar tayi baccin sannan shima ya koma.

Yau ne ranar daurin aure, kuma ranar da za'a kai amarya. Wannan yasa kusan duk mutanen da suka kwana a gidan basu koma baccin safe ba. Kowa daga ya tashi sallar asuba shikenan kuma sai a hau shirye shirye. Humairah ma haka. Tana tashi tayi sallah tayi karatun alqur'ani kamar yadda ta saba sannan tayi morning azkar dinta. Tana gamawa ta fara gwaran dakin da suka kwana ita da Aisha, a lokacin ita kuma Aisha ta fita dan taya Mami hidimar kula da ba'kin ta. Ko da second daya abinda ya faru jiya bai bar zuciyar Humairah ba, tayi iya kacin kokarinta gurin ganin ta ajiye maganar a gefe dan ta samu damar fuskantar yau amma ta kasa.

Babu abinda take gani a idonta sai fuskar Al'ameen sanda yake cewa "will you marry me?" And she kept repeating to herself "No" sometimes har a fili take fadar no din. Tana gama gyaran dakin ta shiga wanka, ta fito ta shafa mai ta saka powder ta kashe maikon fuskarta sannan ta saka lip gloss. She is not a make up person, dama duk kwalliyar bikin yi mata akeyi yau kuwa a wannan mood din nata bata jin zata bari ayi mata wannan kwalliyar. Ta dauko kayan data tanada saboda yau ta saka, doguwar riga ce ta material mai laushi, cream color. Tana sakawa ta kalli kanta a madubi, abinda ta gani baiyi mata dadi ba sam, gabadaya rigar tabi jikinta, ta dauko mayafin data tanada saboda rigar ta yafa taga ko rabin abinda take so ya rufe bai rufe din ba. Tayi ajjiyar zuciya ta zauna a bakin gado tayi tagumi, inama inama, inama mutum yana chanza halittarsa ita dai kam data chanza tata, data mayar da siffar ta irin na matan nan masu fasalin one wadanda maza basu fiya kallon suba, data chanza farar fatarta zuwa baka wadda bata fiya daukan hankalin mutane sosai ba. Inama inama. Sai kuma tayi sauri tayi istigfar, ta tuna yasaiyadi ya taba fada mata cewa duk abinda Allah ya halitta ya halicce shine saboda dalilin da shi kadai ya barwa kansa sani.

Aisha_HumairahDonde viven las historias. Descúbrelo ahora