"What?" Humairah tace cikin muryar mamaki, "mai kake fada haka ne? Don't mock me please" ya girgiza kai yana kokarin mayar da idonsal cikin nata, yace "am not mocking you Humairah, am very serious, this is what I want. Please Humairah, just say yes. Just say yes kiga yadda zan mayar da rayuwarki, kiga yadda zan daga darajarki, ki ga yadda zan ajiyeki always by my side har karshen rayuwarmu, kiga yadda zan share hawayenki kuma in tabbatar da cewa wasu basu fito ba. Just say yes Humairah, Will you marry me"Wasu sabbin hawayen ne suka sake biyo perfect cheeks dinta, ta kalleshi a zaune a gefenta dead serious, a Prince, a perfect prince wanda yafi karfinta ta ko'ina. She might be young and foolish but tasan me kalmar aure take nufi kuma tasan Al'ameen yafi karfinta ta ko'ina a rayuwa. Besides, aure is the last thing da take bukata a yanzu.
Ta dauke kanta daga kansa a hankali tace "No" da sauri yace "what?" Tace "No, I will not marry you Ya Ameen" bai taba tsammanin wannan amsar ba, cikin sanyin murya yace "saboda me? Menene laifina?" Ta girgiza kai tace "you are too perfect for me" ya mike tsaye ya sauko daga stairs din suna facing juna yace "for God's sake, stop calling me perfect. Nobody is perfect Humairah, am not. Nima ina da flaws dina kamar kowa" da sauri tace "kamar me dame fa?" Ya sosa kai yana tunanin amsar da zai bata, tace "baka da amsa" da sauri yace "kamar yanzu gashi kince min ba zaki aure ni ba" tace "wannan ai ba aibu bane ba, blessing ne. Aure na will be the worst mistake da zakayi a rayuwa. I will be nothing but a stain a rayuwarka Ya Ameen. In ka aure ni na tabbatar wata rana sai kayi danasani" da sauri yace "dana sanin me zanyi?" Cikin daga murya tace "danasanin ka zabawa 'ya'yanka uwa marar asali" sai kuma ta rufe fuskarta da hannun ta ta dora kukanta daga inda ta tsaya
Ya zauna a kusa da kafafuwanta cikin muryar roko yace "ni fa nace zan aure ki Humairah. Nasan kuma duk challenges din da auren naki zai sa in fuskanta but am ready for them all" ta bude fuskarta tare da girgiza kanta tace "am not ready ni dai, ko da ace zanyi aure ba yanzu ba, ko da zanyi aure ba irinka zan aura ba Ya Ameen" yace "to irin wa kike so kenan?" Tace "someone lower, someone that is more like me" yayi shiru yana nazarinta, amma a ransa sai yake ganin kamar ba wannan ne kadai dalilin rejecting dinsa da tayi ba, yace "is that your only reason?" Sai ta sunkuyar da kanta tana wasa da zoben hannunta. Al'ameen might be a little different from the other men she knows, but he is still a man, and to her "all men are the same".
Ashe maganar zuciyarta ta fito fili bata sani ba, nan take ransa ya baci yace "is that what you are thinking? Wannan shine kallon da kike min har yanzu? Kina ganin kamar zan aure ki ne saboda cimma wata manufa ta gangar jikina?" Nan take hawayen da bai yi nisa daga idonta ba ya dawo ya cigaba da zuba. Sai kuma ya dawo ya zauna a saitin kafafunta yana kallon titi yace "Kar kiyiwa maza kudin goro Humairah. Mutane daban daban ne kuma suna da halaye mabanbanta. Akwai na gari akwai kuma bata gari, you were just unlucky kinyi ta haduwa da bata garin a 'yar karamar rayuwarki but I assure you ko kashi daya cikin dubu na maza baki sani ba, masu kirkin mu sunfi marasa kirkin mu yawa. Kamar yadda yatsun hannunmu suke ba dai dai ba haka halayenmu suke ba daidai ba. Yanzu misali ni da Bassam, uwa daya uba daya muke amma halayenmu ba daya bane ba, nasan a dan zaman da kikayi damu zaki fahimcu haka. Wani misalin kuma shine Junaid da Tijjani. Identical twins ne kuma they share almost everything amma banda halaye, a dan zaman da kika yi dasu zaki fahimci haka, yanzu misali idan TJ ya kasance fitinanne kina ganin in aka hukunta su duk su biyun anyi wa Junaid adalci kenan? Idan kika hukunta maza gabaki dayanmu da laifin wadansu minority na cikin mu kinga ai baki yi mana adalci ba. Ko da kuwa ace marasa kirkin sune majority dole akwai exceptions, misali Yasaiyadinki na Lagos, ya taimaka miki sosai a rayuwarki, to yanzu kina nufin shima ya taimaka miki ne saboda yana bukatar jikinki?"
Da sauri ta dago kai tana girgiza kai, she looked hurt, tabbas ya taba mata wani special guri na zuciyarta, bai kula da bacin ranta ba yacigaba "wani misalin kuma shine mutumin da kike kira da Savior, mutumin daya dauke ki daga titi kina gap da mutuwa ya nema miki lafiya ya ciyar ya shayar ya tufatar dake ya kuma baki protection for over three years, shima kina so kice min yayi miki wannan taimakon ne dan yana son amfani da jikinki?" Cikin bacin rai tace "don't talk like that about him" ya juyo yana kallon cikin idonta yace "ai bani na fada ba, kece kika fada a lokacin da kika yi generalizing maza, suma wadannnan ai mazan ne, in dai kika ce all men are the same kina nufin suma duk halin su daya da wadancan mazan ko?"

VOCÊ ESTÁ LENDO
Aisha_Humairah
FanficIt is a story about two sisters that are like the two sides of a coin, totally different yet part of each other. It is a story about loneliness, sadness, discrimination, hypocrisy, self pity and of course love. Get your handkerchiefs ready because t...