Love don't cost a thing

9.3K 871 33
                                    

A daddafe Nura ya kwana a asibitin, shima kuma dan doctor yace suna son su yi monitoring dinsa for concussion. Aisha a waya ta kira Amir ta gaya masa kar yaje daukanta tana asibiti, sannan tayi masa bayanin abinda ya faru. Da la'asar sai gashi nan yazo, har da ledarsa yayo musu takeaway din abinci. By then Zainab ta tafi gida sai friends din Nura su biyu da suka zo amma ganin idonsu baisa Aisha ta tafi gida ba sai da Amir ya ce lallai ko tazo su tafi ko ya kira Mami ya gayamata cewa gata nan ta zauna jinyar saurayi a asibiti, haka ta dauki jakarta ta rataya ta turo baki ta fita, ko Nuran batayi wa sallama ba saboda shima ya saka baki yace ta tafi gida ta huta.

A mota Amir ya tarar da ita ya tayar suka tafi. A hanya yace mata "so, it is now settled ko?" Tayi murmushi kawai shima ya tayata, yace "dama bana gaya miki ba? That guy is in love with you, maybe he was hiding it maybe kuma bai sani ba shima, amma yanzu naga ya fito daga shell dinsa, kema kuma kin fito daga naki. But how will you handle the doctor?" Tace "God has already handled that for me, Dr ya janye, yace shi zai raka Nura har dutse gurin Abba" Amir yace "masha Allah, congratulations" a lokacin suka yi packing, ya juyo yana kallonta yace "ina tayaki murna Aisha, duk da nasan nayi rashi sosai amma kuma I wouldn't have it any other way, wannan shine zabin Allah dan haka shi zamu karba hannu bibbiyu. Allah ya sanya alkhairi a cikin lamarin. Allah yasa this will be the beginning of happiness a rayuwarki kinji?"

Kanta yana kasa tana murmushi ta gyada masa kai, ya sake cewa "kamar da akwai wani abu a ranki kuma" ta dago tana kallonsa tace "I have lost a friend, Nura friend dina ne yanzu kuma zai zama something else" Amir yayi murmushi yace "OK, will you like to be my friend then?". Tayi murmushi tace "you are already my friend Amir. Bazan taba mantawa da soyayyarka da kulawarka gareni ba. You will always have a special place in my heart". Har ta bude kofa zata fita sai ya kira sunanta "Aisha" ta juyo tana kallonsa amma bata amsa ba, yace "ina so in gaya miki wata magana. Something has come up, something related to my parents" Aisha ta mayar da kofar ta rufe da sauri tana kallonsa idonta kamar zai fado, ya dan yi murmushi yace "relax, it might be something and it might be nothing. Ba wanda na gaya wa, not even Sultan, bana so in saka wa mutane rai kuma maganar ta zama ba haka bane ba. I want to investigate first, Zan danyi tafiya kwana biyu, zanje Kaduna, inna dawo I will let you know duk abinda ake ciki" ta gyada kai da sauri idonta yana kawo kwalla amma ta rasa da wanne kalaman zata yi masa magana, yana kallonta cikin ido yace "adiós Aisha Humarah" ta bude kofa ta fita ta rufe sannan tace "adiós my friend".

Soyayya ce lafiyayya ake zubawa tsakanin Aisha da Nura, duk wanda yasan Nura yasan Aisha kuma duk wanda yasan Aisha yasan Nura. Aisha ta bawa Mami labarin abinda ya faru kuma tayi farin ciki sosai, musamman ma da ta fahimci cewa da gaske Aisha tana son Nuran, dan haka ta basu support dari bisa dari. Nura yana samun sauki yayi shirin tafiya Yola, dama kuma tun kafin ya tafi din ya fada musu ta waya halin da ake ciki kuma daga innarsa har baffansa sunyi murna sosai, dama duk sun damu akan rashin aurensa.

Dr Mahdi ya cika alkawarinsa, shi yayi wa Nura da iyayensa jagora zuwa kano gidan aunty Bilki, nan suka tarar da Alhaji da Hafeez sun shirya suna jiran isowarsu, sunyi mamakin ganin cewa ba Dr ne mai neman auren ba shima wani yake nemarwa amma babu damar su janye maganarsu tunda sun riga sun amince, daga nan suka dunguma zuwa dutse. Ya kasance cewa mota daya Hafeez da Nura suka shiga, wannan ya bawa Hafeez damar studying Nura tare da yi masa tambayoyi sama sama wadanda ya tabbatar ba zasu bata masa rai ba, shi kuma Nura saboda sanin dangantakar Hafeez din da Aisha sai ya saki jikinsa sosai yake bashi duk amsar tambayoyinsa. Hafeez yaji cewa Nura ya kwanta masa a rai, He looked and acted matured, educated and well mannered, and then he is strong and handsome. Above all, he is in love with Aisha. What more could a woman want? Ganin tambayoyin da yake masa ya saka Nura ya bashi labarin dangantakarsa da Aisha, asalin haduwarsu, rabuwarsu da kuma sake haduwarsu. Hafeez yace "ina tayaka murna, Aisha is the best wife you could ever asked for. Allah ya sanya alkhairi" Nura yace "Ameen, and thanks for understanding, I know you don't have feelings for each other amma nasan fasa auren da akayi will be a kind of disappointment to you" Hafeez ya yi dariya yana girgiza kansa yace "no, not a disappointment. Na taya Aisha murna, musamman yanzu dana ganka, am sure you will make her happier than I can. Dama babban tsoro na game da auren shine ina gudun kar in cutar da ita" sai kuma ya shafa kansa yace "the good thing is, na samu nayi gini na, na hada kayan lefe na, at least kaga yanzu duk sanda mata tazo I will be ready. Amma nasan da haka bata faru ba da maybe ko fili ban siya ba" duk 'yan motar suka yi dariya. Nura yace "ka zo Yola, kasan Yola akwai kyawawan 'yammata, ni ma ina da kannai in dai kace kana so zan baka".

Aisha_HumairahDonde viven las historias. Descúbrelo ahora