Kwanan Aisha uku a asibiti aka sallameta, dinkin da akayi mata a hannu ya dinku kuma an kara mata enough jini dan haka physically bata da wani sauran problem but mentally fa?
Babu labarin Khadija babu kuma na Kamal, dan shi tunda abin ya faru ma wayarsa a kashe take amma ita wayarta a kunne take sai dai duk kiran da za'ayi mata ba zata dauka ba, dan haka suka hakura suka rabu da ita. Tunda aka kwantar da Aisha kullum sai yakumbo da Maryam sunje sun dubo ta, Maryam duk jikinta yayi sanyi sosai, ta rantse musu cewa bata taba tunanin akwai wani abu a tsakanin Kamal da Khadija ba kawai dai tasan sun saba sosai.
Tun a asibiti aunty Bilki tayi kokarin yiwa Abba bayanin da likita yayi mata, bai gane me ciwon yake nufi ba amma shi kansa ya fahimci cewa Aishan bata da lafiya dan gaba daya ta chanza sosai. Ko zaku wuni a gaban Aisha kuna hira ba zata daga kai ta kalleku ba ballantana ta baku amsa, ko ita ake yiwa maganar ba lallai bane ta kulaku ba, babu abinda take yi sai bacci sai sallah sai kwanciya, babu kuka babu dariya, bata farin ciki kuma bata bakin ciki, wannan shine yafi komai dagawa aunty Bilki hankali.
Ranar da za'a sallame su, har office doctor ya sake kiran aunty Bilki da Abba, ya sake musu bayani akan ciwon Aisha kuma ya jaddada musu cewa lallai su tabbatar sun nema mata magani tun kafin karamar magana ta zama babba. Sannan ya rubuta musu referral letter zuwa asibitin malam Aminu Kano inda zata cigaba da ganin likita.
Suna komawa gida aunty Bilki ta shiga dakin Aisha ta fara hada mata kayanta, sai a lokacin tayi realizing yanzu Aisha ko kayan sakawa bata dasu sai kayan da aka dinka mata na fitar biki, tunda duk kayan nata an kai gidanta kuma duk Kamal da Khadijah sun kwashe sun tafi dasu, wato Khadija ko kayan sawa bata bar Aisha dashi ba, hawaye kawai taji yana bin fuskarta tayi sauri ta goge dan kar Aishan ta gani duk da dai tasan ko ta ganin ma babu abinda zata ji tunda a yanzu she is emotionless.
Sai data gama hada kayan sannan ta samu Abba a palour ya zuba uban tagumi yana tunani tace "Ina son zan tafi da Aisha kano gurina" ya dago da sauri yana kallonta yace "haba Bilki, Khadija ta tafi yanzu Aishan ma dauke ta zakiyi? Shikenan duk na rasa su?" Ta zauna a kujera tana fuskantarsa tace "tabbas a lokacin da abin nan ya faru naji haushinka sosai, na dora maka laifin duk abinda ya faru, amma yanzu na riga na sawa zuciyata salama, na yarda cewa abinda ya faru Allah ya riga ya rubuta shi tun kafin a haifi Aisha da Khadija, wata bata ta ba auren mijin wata, Kamal mijin Khadija ne bana Aisha ba shi yasa Khadija ta aure shi. Yanzu abinda ya kamata mu saka a gabanmu shine neman lafiyar Aisha, kaji dai abinda likita yace a kanta, dan haka ina ganin tafiya ta da ita shine mafi alkhairi a garemu da ita baki daya. Kaga dai na farko in na tafi da ita kamar zan raba ta da memories din nan ne da abinda ya faru anan din, zata fara sabuwar rayuwa kenan. Sannan na biyu kuma doctor din da zata ke gani a kano yake, kaga an huta da zirga zirgar kaita asibiti kano".
Abba yace "to amma karatun ta fa? Kar ki manta tana makaranta anan kuma a iyakacin sani na Aisha tana son karatun ta sosai" aunty tace "yanzu wa yake zancen karatu ne wai? Lafiyar ta fa ake nema, in babu lafiya ta yaya zata yi karatun? Yanxu ko ta koma makaranta na tabbatar babu abinda zata ke fahimta a karatun nata, tunda hankalinta sam baya tare da ita, She is depressed" sai kuma ta fara goge hawaye, a hankali Abba yace "shikenan Bilki, ki tafi da ita din kawai, ni nasan wannan wani hukuncin ubangiji ne akai na, ina fatan Allah yasa wannan abu ya zamo alkhairi a gurin yaran nan duk su biyun gaba daya".
Aunty da kanta ta gayawa gwoggo yadda suka yi da Abba, kuma gwoggon ma bata ki shawarar Aunty ba, ta juya tana kallon Aisha wadda take ta aikin juya abinci har yanzu bata kai ko loma daya ba tace "Aisha kina son kibi auntyn ki kano ko kuma kinfi son ki zauna a nan tare da ni?" Ta dago kai ta kallesu su biyun sannan ta cigaba da juya abincinta, kamar ba zata yi magana ba sai kuma tace "kowanne ma, duk daya" kuma har cikin ranta gaskiyar kenan, bata da zabi, bata damu ba, bata damu da ko gurin wa ye zata zauna ba.
VOUS LISEZ
Aisha_Humairah
FanfictionIt is a story about two sisters that are like the two sides of a coin, totally different yet part of each other. It is a story about loneliness, sadness, discrimination, hypocrisy, self pity and of course love. Get your handkerchiefs ready because t...