A lokacin da Buhari ya samu labari, yayi bakin ciki sosai, saboda da gaske yaso auren Khadija, amma kuma shi mai biyayya ne, baya ja da hukuncin iyayensa, dan haka sai ya samu Murtala, mijin Shema'u yayi masa bayanin duk abinda ya faru kuma ya roke shi da yayiwa Khadija bayani yadda zasuyi rabuwar lafiya ba tare da an samu bacin rai ba.
Ai kuwa dai Khadija bata dauki labarin da sauki ba, dan kuka ta zauna tana yi a tsakar gida, ba wai rabuwa da Buhari ne ta dame ta ba, saboda dama ba wani son sa take yi can ba, bakin cikin ta shine sharri da mutane sukayi mata, a cewar ta, tace " haka kawai a unguwar nan an bi an saka min ido, duk abinda nayi mutane idonsu yana kai, ni ban damu dasu ba amma su sun damu dani, ina ruwansu koma me nake yi ina ruwansu?"
Gwoggo tace "bakin ciki ne suke miki, dan duk sunga 'ya'yansu basu kai ki kyau da farin jini ba, shine suke so su kala miki sharri dan su hana ki aure, to aniyarsu ta koma kansu, insha Allah sai kin samu mijin da yafi wannan komai" Aisha tace "to kema ki daina yawon mana Khadija, wayon nan fa ba shi zai samar miki miji ba, kin tuna abinda Umma ta kan ce duk inda mijinki yake kina gida a zaune zaizo ya same ki" Khadija tace "dama ai haka zaki ce, ke ma ai duk bakin ku daya da 'yan unguwar, ba zan yi mamaki bama in aka ce min harda ke a masu bada muguwar shaida akaina, ni ban taba ganin 'yar'uwa irinki ba, dake da babu duk daya a gurina" ta cigaba da kukan ta.
Aisha dai tayi shiru bata kara cewa komai ba. Da Abba yazo aka bashi labarin abinda ya faru kasa magana yayi, girgiza kansa kawai yayi yace Allah ya kyauta. Sai daga baya yazo ya samu gwoggo yace "ni ina ganin Yaya, da zaki bar Khadija ta koma kano gurin dangin mahaifiyarta ta dan zauna dasu, tunda nan din an riga an bata mata suna, in mutane suka dan daina ganin ta sai su manta da ita...."
Da sauri gwoggo ta daga masa hannu, "dakata haka nan, so kake mu nuna wa mutane cewa abinda suke fada gaskiya ne kenan? Ai in dai aka daina ganinta wani ma cewa zaiyi ciki tayi ta tafi zubarwa, yo mutane da sharri ballantana an basu abin sharrin? Ai kawai tayi zamanta, aniyarsu ta koma kansu" Abba dai baiji dadi ba, shi yasan in Khadija taje kano gurin Bilkisu to dole kunnenta zaiyi laushi, shima kuma hankalinsa zaifi kwanciya.
Aisha da Kamal kullum soyayya tana kara karfi, sanda yaga result dinta cewa yayi "wai Humaira da akwai abinda baki iya ba a duniya?" Dariya tayi tace "sosai ma, akwai abubuwa da yawa da ban iya ba, ai babu wanda zaice ya iya komai a duniya" yace "amma ke dai ta daban ce a cikin mutane, you are among the lucky ones, ina fatan 'ya'yan da zamu haifa suyo halayenki gaba daya, kuma suyo kwakwalwarki ta karatu, dan in suka yo tawa akwai matsala" dariya suka yi gaba daya tace "kaji ka ko? In wani yaji sai ya dauka irin dondis din nan ne, bayan Nura ya gaya min irin points din da kake ja a department din ku" da sauri yace "Nuran? Nura munafiki ne ashe? Shi ya gaya miki nasa, bayan shine overall a kaf wadanda zasuyi graduating this year? Muna sa ran ma makaranta zata biya masa scholarship ya tafi kasar waje karatu" ta jinjina maganar tace "bai taba gaya min ba kuwa" yace "ai baya so a sani, ban san me yasa ba, in da nine ai rubutawa zanyi a goshina in ringa yawo ana gani" tayi dariya kawai.
Duk sanda suke tare da Kamal ji take kamar bata da wani problem a rayuwarta, Kamal ya zamanto shine farin cikinta, ko da an bata mata rai daga ta tuno shi zata ji zuciyarta tayi wasai. Kullum in suna tare sai yayi ta gaya mata kalamai masu dadi, har sai yasa ta jita on top of the world, taji ta kamar tafi kowa sa'a a duniya. Bata taba sanin soyayya ba sai akan Kamal, kuma tana saka ran daga kansa ta rufe soyayyar dan ya ishe ta komai duniya da lahira. Shima a gurinsa jin ta yake yi har cikin jinin sa, she is exactly what he wants for a wife. Yana ganin yadda friends dinsa masu aure suke ta fama kullum cikin rigima da matansu, shi baya son hakan, shi so yake yi ace idan yayi aure mutu ka raba, kuma yana da hope cewa in dai ya auri Aisha to kuwa mutuwar ce zata raba, dan bayajin zai samu problem da ita.
Kamal baya kwana uku bai je gurin Aisha ba duk kuwa da irin abubuwan da suke kansa, dan gaba daya harkar dukiyar yakumbo da 'ya'yanta yana hannunsa, ga makaranta da yake zuwa, ga kuma shagon dinkinsa, duk da ba kullum yake zama a shagon ba. Sannan kuma kullum sai yaje yaci abincin Aisha a cafeteria, dan yanzu har take away yake yi ya tafi da na dare.

VOUS LISEZ
Aisha_Humairah
FanfictionIt is a story about two sisters that are like the two sides of a coin, totally different yet part of each other. It is a story about loneliness, sadness, discrimination, hypocrisy, self pity and of course love. Get your handkerchiefs ready because t...