Ina neman afuwar jina da kukayi shiru kwana biyu, na samu matsalar waya ne amma yanzu alhamdulillah. Ku sani, na fiku damuwa da ganin mun kammala wannan littafin. Kuma ku sani, duk abinda nayi inayi ne iyakacin kokari na. Nagode da soyayyarku gareni da littattafaina. Allah yabar zumunci.
Tunda Aisha taje reception take baza idon ganin Humairah amma shiru. Tayi ta bin kawayen amarya tana dubawa amma babu Humairah babu labarinta. Sai taji babu dadi a zuciyarta, taji kamar tayi sakaci da lamarin Humairah, she should have made sure Humairah ta taho kafin ita ta taho, dan a yanzu tunaninta yafi karkatuwa ga cewa Humairah bata taho daga abuja ba, dan last ganin da tayi mata ma bacci take yi a kan gado.
Ta samu guri ta zauna ita kadai tana kara gwada number Humairah wadda har yanzu bata shiga. Tana nan zaune kiran aunty Bilki ya shigo mata, ta dan yi tsaki kadan, ba haka taso ba, taso ace ta nuna wa su aunty Humairah saboda tana so taga yadda zasu yi reacting, shin suma zasuga abinda take gani a tare da yarinyar ko kuwa ita kadai ce take gani?
Ta dauki wayar suka sanar da ita sun iso sannan ta fita ta shigo dasu. Suna ta kalle kallen tsari da haduwa irin na gidan sarautar kano, duk da kasancewarsu kanawa amma basu taba shigowa gidan ba sai yau, dalilin wa dalilata. A gurin reception din ta samar musu gurin zama sannan ta tabbatar an gabatar musu da abubuwan ci da sha sannan ta zauna ta gaishe da aunty, Zahra da Sa'adiyya kuma suka gaisheta. Sannan suka kama hirar su ta zumunci, most hirar akan sabon gidan da Aishan ta ginawa Abba a dutse ne, katon gidan ne flat mai dauke da parts biyu, part din Abba da Mama a hade, sai kuma part din da Aisha ta gina saboda ita da yayanta da mijinta in sunzo gari. A gaban gidan kuma Nura ya gina wa Abba manyan shaguna guda biyu, daya na kayan masarufi, tun daga kan kayan abinci zuwa duk abin amfani na yau da gobe, daya kuma na sitiru, atampopi, shaddoji, laces, takalma, da sauran makamantansu. Yanzu Abba an daina saida gwanjo, wannan mummunar 'yar tasa da baya so yanzu ita tayi masa rana, kyakykyawar kuwa tana can yawon duniya.
An gama komai har curtains an saka, mai furnitures ne yake ta bata musu lokaci. Aunty Bilki tace "ni ban ma san dalilin da yasa kika bashi aikin ba, da kin kawo nan anyi miki, menene banbancin Kano da Dutse? Minti nawa ne an kai can din" Aisha tace "wallahi aunty Abba ne ya dage sai an bashi, wai mutumin sane gwara a bashi shima ya samu dan wani abu" Sa'adiyya tace "ai kuwa gashi nan ya nuna muku halin 'yan Adam, basu san alkhairi ba" Zahra tace "to yanzu ya za'ayi maganar walima?" Aisha tayi ajjiyar zuciya tace "dole a daga ta, yanzu nan da kwana uku zan koma India, zuwa lokacin da zan kammala in dawo ai nasan duk abinsa ya gama by then, kinga sai a tare kawai".
Walima sosai Aisha take so ta shirya, so take ta gayyaci danginta na both barin uwa da uba saboda ayi zumunci dan aiyuka sun mata yawa sam bata samun damar yin zumunci yadda ya kamata. Sannan tana so ta gabatar musu da Humairah duk da bata san irin karbar da zasu yi mata ba, dan bata ji dadin abinda Abba ya gaya mata a waya ba sanda ta bashi labarin adopting Humairah da tayi. "Haka kawai dan nema wa kai Aisha sai ki kwaso yarinyar da baki san ko wacece ba ki kawo ta gidanki? Idan kuma mayya ce fa taje ta kama su Junaidu ta bar mu da salati? Ko kuma ta shirya miki makirci ta rabaki da mijinki? Gaskiya ni dai ban amince da wannan batu ba, ku tattarata ku mayar da ita inda kuka dauko ta" anan suka tsaya da maganar, kuma tasan yayi shiru ne saboda tafiyar da tayi amma yanzu tana dawowa zai dora daga inda ya tsaya.
Bayan su aunty Bilki sun gama ne Aisha ta kaisu gurin Mami da gurin Basma suka gaisa suka yi mata fatan alkhairi tare da alkawarin zuwa suga dakinta in komai ya lafa, daga nan Aisha ta musu rakiya suka tafi ita kuma ta dawo gurin taron.
Su Humairah basu zo fada ba sai da aka fara kiran magrib, suna zuwa gurin da aka tanada saboda ajiye motoci yayi packing ya juyo yana kallonta tana ta kalle kallen gurin da kuma mutanen da suke ta shige da fice a gurin, sai yaga fuskarta ta kara yi masa kama data babies musamman yadda kwantaccen gashin daya kwanta a goshinta ya zagaye fuskarta, ya dauke kansa yana jin wani abu yana taba zuciyarsa. Yace "ki gyara dankwalinki, gashinki ya fito" nervously ta jawo dankwalinta gaba, sannan yasa dankwalin ya sakwarkwace, Al'ameen ya danyi murmushin mugunta, a ransa yace "at least she looks less desirable now". Sannan a fili yace mata "ki shiga ciki, ni ba shiga zan ba" a take yanayinta ya chanza, ta kwabe fuska kamar zata yi kuka tace "dan Allah Ya Ameen kazo ka rakani, ni wannan katon gidan ina zan dosa a cikinsa?" Yace "ki kira Basma sai ta gaya miki inda suke, ko ta turo a tafi dake" ta nuna masa wayarta tace "wayata ta mutu fa" yace "OK. Kinga waccan kofar tanan zaki shiga, in kin shiga cikin gidan sai ki tambayi inda baƙi suke, simple" ya fada yana nuna kofar da yaga mutane suna ta shige da fice daga ciki.
YOU ARE READING
Aisha_Humairah
FanfictionIt is a story about two sisters that are like the two sides of a coin, totally different yet part of each other. It is a story about loneliness, sadness, discrimination, hypocrisy, self pity and of course love. Get your handkerchiefs ready because t...