Abdallah

10.9K 910 56
                                    

Aunty tace "to shikenan doctor, mu dai tsakanin mu da kai babu abinda zamu ce sai godiya, Allah ya saka maka da alkhairi ameen. In dai har kana ganin wannan shine solution to mun amince 100%, Allah yasa mu dace" yace "Ameen" sukayi sallama.

Washegari yana zuwa office ya dauko file din Aisha ya rubuta transfer letter zuwa office din da yake so ya tura shi ya aika. Sai da aka kusa tashi sannan aka aiko masa da acceptance letter. Yana zuwa gida bayan yayi wanka ya zauna cin abinci tare da family dinsa kamar yadda ya saba sai ya aika a kirawo masa Aisha, tana shigowa ta tsaya daga bakin kofa tana kallonsu taki karasowa, Anisa tayi dariya dan duk sun san tsoron me take yi, doctor ya daga tsokalin hannunsa yace "kinga abinda yake hannuna? Ko kin taba ganin anyi allura da chokali?" Suka yi dariya gabaki daya.

Ta tako a hankali ta shigo palourn, ta zauna dan nesa kadan dasu. Ya cigaba da cin abincinsa sannan yace "gobe zan tafi dake asibiti" ya kalleta yaga yadda ta bata rai ta turo baki, ya cigaba "I want you to meet my friend there, she is also a doctor amma bata allura, magana kawai zakuyi da ita shikenan" Amira tace "kuma nima kinga friend dita ce, dama nace miki wata rana zan hada ku kafin ki koma gida" doctor yace "gobe da sassafe zamu fita tare in ajiyeki a asibiti gurinta, daga nan zan wuce kano, da yamma driver zaije ya dauko ki tunda ni a kano zan kwana sai jibi zan dawo" "to" kawai Aisha tace, yace "ko kina da sako kano?" Ta girgiza kanta, ta mike ta dauki Annur da yake kwance akan kujerarsa ta saka shi a kafadarta ta fice, bayan ta fita Amira tace "I like her, ina son tarbiyyarta da nutsuwarta, ji nake inama kanwata ce tunda ni ba kanwa ce dani ba. Har bana son ta koma gidan su" doctor yace  ba tare daya kalle ta ba "ko bata koma gidan su ba ai dole zatayi aure ko?".

Washegari da sassafe suka fita, sama suka hau direct, Aisha bata taba zuwa wannan part of the hospital din ba tana dai ganin mutane suna shiga. Sukayi ta wuce wurare ana ta share share sannan suka zo wata babbar kofa suka shiga wani waiting room. Mutanen gurin suka tashi da sauri suna gaishe da doctor Mahdi, ya amsa da fara'ar sa tare da ambatar sunan kowannen su, sannan yace "is she here?" wata tace "yes sir, tace in kazo ace ka shiga" yayi dariya yace "yau bata makara ba kenan" suma duk suka taya shi dariyar banda Aisha.

Yayi knocking kofar sau biyu sannan ya tura ya shiga da sallama. Aisha ta bi bayansa. Yana shiga yace "ba sa banba yau nazo office da wuri" matar ta kirkiri hammar karya tace "kuma bacci bai ishe ni ba" yace "ke dama ai bacci baya isarki, in da za'a barki zakiyi tayi ne" tayi dariya shima yayi sannan suka fara gaisawa, ya karasa shiga ya zauna akan kujera. Sai a lokacin Aisha ta samu damar ganin fuskar matar, lokaci daya kawai taji bata yi mata ba, too much of everything, too beautiful, too smart, too wealthy, too educated, she have too much of everything that Aisha lacks.

Ta tsaya kawai daga bakin kofa taki karasowa. Tana kallon su suna ta hirar su suna tambayar lafiyar iyalan juna, sai da suka gama sannan yace "to ga kanwata nan na kawo miki, if you read through her file zaki fahimci abinda nake so kiyi mata, I have done my best, she just need your magic touch" ta dago kai ta kalli Aisha, wacce tayi saurin sunkuyar da kanta kasa, tace "hmm, OK. I will see what I can do" ya mike yace "to, ni nayi nan, i will see you guys tomorrow" ya karasa kusa da Aisha yayi mata magana a hankali sannan ya bude kofa ya fita.

Ta karaso ciki kamar wadda kwai ya fashewa a ciki ta zauna a kan wata kujera da take can gefe, ji take yi kamar ta dora hannu aka ta fashe da kuka, what on earth is she doing here? Matar bata jima tana karanta file din ba tayi dan karamin tsaki ta ture shi gefe, a hankali tace "theory, theory, wannan sai ya saka min ciwon kai da safen nan" ta dago tana kallon Aisha wadda ta sake sunkuyar da kanta kasa, tace "Aisha, bamu gaisa ba fa, doctor Mahdi yace min ke kanwarsa ce kuma ni na san ba haka bane ba, dawo kusa dani ki fada min gaskiya" Aisha bata dago kai ba ballantana ta bata amsa, ta sake cewa "naga a file dinki an ce ke 'yar dutse ce, ni ma 'yar jigawa ce amma ban taba zuwa dutse ba ko sau daya, will you like to tell me about it?" Shima babu amsa.

Aisha_HumairahWhere stories live. Discover now