Haunted

8.2K 733 8
                                        

A tsorace ta farka with the feeling na cewa ta makara. Ta mike zaune da sauri tana kallon hasken ranar da ya fara shigowa ta window sai kuma ta kalli agogon da yake makale a bangon da yake facing gadonta. 7:38 ta gani. Ta mike zaune da sauri "innalillahi! yau ya akayi na makara haka? Yau kam nasan yasaiyadi sai yayi min bulala" ta sauko daga gadon tana tunanin ko sallar asuba batayi ba, dama babu wanda yake tashin ta, babu wanda yake cewa tashi kiyi sallar ko kuma tashi ki shirya ki tafi makaranta, ita take tashin kanta kullum kuma ta shirya kanta zuwa makaranta ba tare da taimakon kowa ba, wani lokacin ma har ta fita daga gidan ba zata ga kowa ba, in ta dawo kuma babu wanda zai ce zo kiyi homework dinki, abinda kawai mamanta ta damu dashi shine taga taci exams dinta, dan kullum tana gaya mata "Baby so nake kiyi karatu ki cika min burina dani na kasa cikawa da kaina, so nake ki zama likita".

Da sauri ta tashi ta shiga toilet dinta tayi brush tayi alwala, yau kam ba zata yi wanka bama saboda ta makara, ta dawo daki ta daura zani akan doguwar rigar baccin ta ta saka hijab ta tayar da sallah, bata yi wata doguwar addu'ah ba kamar yadda ta saba, addu'ar da tayi kawai shine Allah yasa kar yasaiyadi yayi mata bulalar makara, duk da tasan yana rangwanta mata sosai saboda sanin da yayi wacece mahaifiyarta, yasan cewa ita da kanta ta saka kanta a islamiyyar kuma ita take kai kanta ta dawo da kanta gida ba tare da jagorancin kowa ba.

Tun tana shekaru bakwai ta saka kanta a islamiyyar kuma take zuwa har yanzu data ke da shekaru goma sha biyu, bata taba fashi ba sai dai in bata da lafiya. Kuma tana daga cikin best students dinsa dan sosai yake alfahari da ita wanda hakan ya saka har tsayar da ita yakeyi kullum su shafe kusan awa guda tare yana mata nasihohi akan kula da kanta da addininta da kuma duk wani abu na tarbiyya wanda ya tabbatar bata samu daga gida, and he was proud of what she has so far became.

Tana idar da sallar ta dauko uniform din islamiyyar ta tana ayyana cewa ba zata tsaya yin breakfast ba, dan yau weekend kuma tasan uncle yana gida dan haka indai har ta bari suka hadu bata tafi ba to ba zai barta ta tafi ba, dan sai ya sakata wani abin kuma Mama zata ce lallai sai ta yi masa zata tafi, kafin nan tasan an riga an tashi daga makarantar. Ta cire hijab din ta cire zanin, sannan ta cire doguwar rigar baccin, ya zamanto daga ita sai pant sai half vest din da Mama ta bata tace ta ringa sawa saboda yadda kirjinta ya soma tasowa, ta tuna sanda mamanta ta lura da hakan, tana kallon ta tana dariya tace "My Baby is no longer a Baby, wannan wa zai ganki yace 12 years kike. Dole ne ki kara kiyaye abinda nake gaya miki kullum, babu ke babu wani namiji ko magana ban yadda ta shiga tsakanin ki da wani namijin ba, they only want one thing from you and one thing only, they only want to get in between your legs shikenan amfanin ki a gurin su, dukkanin su haka suke, duk wanda yace miki ba haka yake ba karya yake yi".

And with time, she has come to believed that. Dan haka ko a makaranta bata kula maza, ko matan ma dai dai ne suke kula ta saboda sun san wacece uwar ta, da kunnenta tasha jin iyaye suna yiwa 'ya'yansu warning akan kar suyi abota da ita " she is a bad girl, her mother is a very bad person, babu ku babu ita". Dan haka bata da kawa ko aboki sai littattafanta sai kuma yasaiyadin islamiyyar su.

Ta dauko rigar uniform din ta zura a kanta, it got stuck, saboda bata balle buttons din rigar ba, sai kawai taji a jikinta kamar ana kallonta, ta saba da wannan feelings din dan kullum cikin kallonta ake yi, a gida kowanne uncle yazo gurin mamanta kallonta yake yi, a makaranta yara kallonta suke yi amma data kalle su sai su dauke kai, a unguwa ma haka, but this time was different, this time she was naked.

Da sauri ta cire rigar daga kanta ta kalli bakin kofa, yana tsaye hannunsa daya a jikin kofa dayan kuma a jikin bango and he was stark naked, tsoro taji a ranta wanda bata taba jin irinsa ba, bata san sanda rigar hannunta ta fadi ba, kallonsa kawai take yi ido a waje tana kallon abinda bata taba gani ba. Kato ne, dan duk cikin abokan da mamanta take yi bata taba yin wanda yakai wannan girma ba, baki ne sosai, dan a fuskarsa idonsa kawai kake gani sai fararen hakoransa in yayi dariya. Kansa ya sha kwal kwal sai kyalli yake kamar mudubi. Da baya da baya ta fara tafiya shi kuma yana tahowa, a haka har ta hadu da bangon dakin, nan take ta fahimci cewa bata da gurin gudu dan haka ta bude bakinta da dukkan karfinta ta fara kiran mahaifiyarta "Mama, Mama, Mama" amma sai taga ko gezau baiyi ba sai kara kusantota ma da yake yi fuskarsa da wani yanayin da bata taba gani ba, he must be crazy, in ya sake ya taba ta Mamanta will surely kill him, dan duk wanda yasan Mamanta yasan it is better not to mess with her precious daughter.

Aisha_HumairahTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang