The Meeting

7.8K 776 22
                                    

Yola
Kamal ya ajiye wayar yana jin amsa kuwar maganar Aisha. "there is someone I want you to meet" kuma wai a dutse. Bashi da ja a zuciyarsa yasan maganar menene, amma waye someone din? A cikin mutum biyu yasan daya ce, ko dai Khadija ko kuma Humairah, ko kuma Khadija da Humairah. Amma sai ya samu kansa da katse wayar ba tare daya tambayi clarification ba saboda yana tsoron amsar. Yana tsoron ace masa Khadija ce ta dawo amma ba tare da Humairah ba, yana tsoron ace masa wani mummunan abu ya faru da Humairah. In dai kuwa har Khadijah ta sake ya ganta ba tare da Humairah ba bai san me zaiyi mata bama, dan yana jin in ya shaketa sai numfashinta ya bar jikinta.

Ya kalli agogo yaga karfe goman safiyar alhamis. Saturday tace masa zasu hadu a dutse, tafiya daga Yola zuwa dutse kuwa ba karama bace ba dan haka dole yayi acting very past. Ya san Alhaji yana gida dan bai cika fita ba indai ba wani muhimmin abu bane ba sai kuma in zasuyi taron su na shugabannin Miyatti Allah, dan haka ya tashi ya saka rigarsa ya kama hannun Amna suka shiga cikin gida. Dakin Innar sa ya fara zuwa amma ya tarar bata nan tana dakin Alhaji. Daga nan sai ya shiga dadin Hajja Nene abokiyar zaman Inna ya gaisheta ta amsa da fara'arta tana yiwa Amna wasa tana kuma tambayar lafiyar mazajenta. Daga nan sai ya tafi dakin Alhaji. Ya tarar dashi a zaune a palonsa yana cin dumamen tuwon alkama miyar busashshiyar kubewar da taji nama da man shanu, sannan ga kunun tsamiya a gefe. Ya gaishe shi ya gaishe da Inna sannan ya jawo plate ya fara serving kansa.

Inna tace "uhum, matarka bata baka abinci bane ba?" yayi murmushi kawai wanda bai kai ciki ba saboda tunanin maganar da sukayi da Aisha dazu. Ya fara cin abincin a hankali yana tuna wani alkawari da Aisha ta taba yi masa lokacin yana nemanta, alkawarin kullum zata ke yi masa tuwo da daddare sannan da safe ta dumama masa, yayi saurin kawar da tunanin daga ransa. Some things will never change. Bashi da problem what so ever da Maryam, duk da ba auren soyayya akayi musu ba amma akwai kauna da shakuwa a tsakanin su ga kuma 'ya'ya biyar da Allah ya azurtasu dasu, kuma ko dan soyayya da Yakumbo tayi masa a duniya baya jin zai iya wulakanta Maryam.

Sai da Alhaji ya gama cin abincin sa aka kawo masa ruwa ya wanke hannunsa sannan yace "ya akayi ne Dan Yakumbo?" Kamal ya ture farantin daya ci abinci gefe sannan ya zayyanawa Alhaji yadda sukayi da Aisha da kuma abinda yake tunanin shine sanadiyyar kiran. Nan take Inna dake zaune gefe ta fara jero adduoi. "Allah yasa karshen wahalar mu ce muda yarinyar nan tazo". Alhaji yace "Abinda za'ayi, ba zaka tafi kai kadai ba, ka fita yanzu kaje gidan Saleh ka kira min shi sai ku tafi a motarsa, ku shirya a yau, gobe Juma'a da assuba sai ku dauki hanya. Idan har yarinyar aka samu ku karbo ta ku taho mana da ita nan. Allah ya kiyaye hanya ya kuma bada sa'a" Kamal yayi godiya sannan ya fita yana kokarin neman number din yayansa Saleh, wanda shi yake bi a gidan kuma shine kusan tasu tafi zuwa daya saboda sa'anni ne.

Assubahin Juma'a suka dauki hanya. Maryam tayi tayi ta bisu amma Kamal yaki, badan komai ba sai dan baisan wanne labari zai tarar a dutsen ba, idan mummunan labari ne kuwa he don't want her anywhere near abinda zai aikata.

Kano
A lokacin da aunty Bilki ta gama jin duk bayanan Aisha fada ta fara yi "yanzu Aisha kina nufin kice min yarinyar nan kusan kwanan ta biyar a gidanki amma baki fada min ba sai yanzu? Kina tunanin kinyi dai dai kenan? Sai data gudu tukunna ko? Da tabi dare tabi rana ta yashe ki ta kara gaba aida sai dai ince miki Allah ya kara. Yanzu ke ko a titi kika ga Khadija ban dauka zaki tsaya ki kulata ba ballantana har ki ajiye ta a gidan ki tsahon kwanaki. Dama yaya Khadija take ballantana ta gama yawon duniya shekara da shekaru in kikayi wasa ma mijin zata raba ki dashi. Wai ke me 'yar uwa ko?" haka tayi ta fada ita kadai Aisha tana jinta kawai, ta riga tasan wannan shine abinda auntyn zata fada shi yasa tun da Khadija tazo ta ki gaya mata. Ta tuna farkon guduwar Khadija aunty tace "ni fata na daya yarinyar nan ta mutu kawai. Yo kar muje zunubinta ya hana Rabi'a kwanciyar kabari"

Dama yaya lafiyar kura balle tayi hauka? Dama ance mutum mai fada in girma ya fara zuwa masa sai ya nunka yadda yake da. Ta rasa menene matsalar Aunty da Nura akan Khadijah. Ita fa akayiwa laifin nan amma su sunfi kowa daukan zafi. Tace "aunty duk ba wannan bane ba, komai ya wuce ai, in ana tuna baya ba za'a taba yin gaba ba. Yanzu sai mu gode Allah daya dawo mana da su kuma mu jira muga abinda ya shirya mana nan gaba" suka yi shiru tare. Sannan Aisha tace "dan Allah Aunty ki zo" aunty tayi ajjiyar zuciya tace "zanzo Aisha, amma ba dan Khadija ba sai dan Humairah" Aisha tayi murmushi a ranta tace "duk daya"

Aisha_HumairahWhere stories live. Discover now