Duniya gaba daya ta yiwa Al'ameen zafi. Ya rasa dalilin da yasa Mami ta hada shi da wannan aikin. Gashi kuma shi bai taba yiwa Mami musu ba ko kuma in ta saka shi wani abin yaki yi ba. Ga kuma threat din da tayi na aurawa Abdallah wannan crazy yarinyar, kuma yasan ta in tace zatayi abu to tabbas zatayi din. Amma shi ta yaya zai fara kula wannan yarinyar? Haka kawai ma yaje yayi mata magana ta kara yi masa wani ihun? Shi ko a makaranta yammatan da suke kula shi very classy ne irinsa, wadanda basu da hayaniya kuma wadanda suka san abinda suke yi, ita kuma wannan fa?Kasa kwanciya yayi ya tashi ya fita waje. In zaiyi tunani yafi son ya samu guri mai fresh air yadda kansa zai bude sosai. Ya kwanta rigingine a saman mota yana kallon yadda taurari suka yiwa sama ado. Tunanin labarin da Mami ta bashi dan gane da rayuwar yarinyar ya fara yi, amma kuma duk wannan prediction ne tunda tace yarinyar bata taba gaya wa kowa ainahin ya rayuwar tata ta kasance ba, but his mother is very good in studying people, she is hardly wrong when it comes to things like that. Dan haka chances are very high cewa abinda ta fada haka ne. Sai kawai yaji tausayin yarinyar, yaji haushinta ya dan ragu kadan a zuciyarsa.
Ya tuno babansa tun yana matashi yayi dedicating life dinsa to helping mutane marasa gata, mutane irin crazy yarinyar nan, to in har babansa zai yi why not him? He always want to be like his father, maybe he can never be, but he can try. It is not as if soyayya zasuyi, kawai dai kulata Mami take so yakeyi and ya zama nice to her. Ya mike ya shiga gida yana tunanin ta inda zai fara. A ransa yace "ya ma sunanta?"
Washegari ya dawo daga office wajan karfe biyar. A gajiye yake sosai. Palour babu kowa sai yaran gidan, suka bishi da gaisuwa ya amsa ta hanyar motsa bakinsa ba tare da sun ma ji me yace ba. Part din Mami ya tafi, ya sameta a palonta zaune tare da 'yammatan ta. Ya lura da yadda Humairah ta dauke wuta gaba daya ta fara jan hijab dinta tana kara rufe jikinta. Ya gaishe da Mami sannan ya zauna a gefenta yace "Mami na gaji da yawa wallahi" tace "gajiya kuma? Ni banga alamar gajiya a tare da kai ba. Ai da ka gaji da gani zanyi kana ta hada gumi ko inga fuskarka tayi baki ko something like that" ya shagwabe fuska "Mami" ta dungure masa kai "kai san jiki ne da kai da yawa, kayi ta wani lallaba jiki sai kace mace". Basma tayi masa sannu da zuwa Humairah ma tayi kamar yadda taga Basma tayi. Sai kuma ta mike ta kama hanyar daki, Mami tace "ina zakije kuma kuna kallon ku? Ki dawo kiyi zamanki" dole ta juyo ta dawo ta zauna tana satar kallon Al'ameen tana fatan Allah yasa ya tashi ya tafi, amma maimakon haka sai taga ya gyara kwanciya akan kujerar ya lumshe idonsa.
Nan ta samu damar kallonsa, kamar yadda Mami ta fada babu alamar gajiya a tare dashi sai tsabar hutu da fatar sa take bayyanawa. Humairah ta kalli fuskarsa da hannayensa wanda anan ne kadai take ganin fatarsa, babu ko digon tabo balle wani patch na baki, tas take kamar bai taba shiga rana ba. Askin kansa low cut ne wanda ya tafi dai dai da sajensa da akayi wa wani irin gyara mai kayatarwa sannan ya hade da siririn gashin bakinsa daya zagaye jajayen lips dinsa.
Perfect, komai nasa is perfect kamar yadda rayuwarsa take perfect. Batayi aune ba taga idonsa a cikin nata, tayi saurin dauke kanta tana wayancewa da kallon TV. Anan shi kuma ya samu damar kallonta. Tunda tazo gidan bai taba wani zama ya kalleta sosai ba dan inda za'a tambaye shi kamanninta ba zai iya fada ba except cewa fara ce. Sai yanzu ya lura cewa kyakykyawa ce, pure beauty in a very special way. Ya jima yana kallon zagayayyiyar baby face dinta da yadda tsakiyar habarta ya lotsa ya bawa face din wani special shape. Skin dinta mai kyau ce, natural kyau daya tabbatar babu mai a cikinsa.
Sai kuma ya tuna da karar muryarta sanda take masa ihu a daki, ya danyi tsaki ya dauke kansa sai suka hada ido da Mami, yasan kallon da take masa ya san ma'anar kallon, ya langwabe kai ita kuma ta bata rai. Ya juya yana kallon Humairah, a ransa yace 'yama sunanta? Yanzu yaji Mami ta fada amma ya kuma mantawa' sai yace "ke, ke" Basma ce ta lura cewa Humairah yake wa magana tace "Humairah ana miki magana" ta juyo a tsorace kamar idonta zai fado kasa tana kallonsa, taga ita yake kallo amma sai ta juya hagu da damanta kamar tana neman wani sannan ta nuna kanta tace "ni?" Saura kadan yace mata "a'a bake ba, ni" amma sai ya rabu da ita yace "kawo min ruwa in sha".
YOU ARE READING
Aisha_Humairah
FanfictionIt is a story about two sisters that are like the two sides of a coin, totally different yet part of each other. It is a story about loneliness, sadness, discrimination, hypocrisy, self pity and of course love. Get your handkerchiefs ready because t...