Washegari suna tashi Aunty ta gaya musu maganar zuwan Umma, tace "ba sai kunje ko ina yau ba, kar tazo kuma ba kwa nan. Ban san dai me zai kawo ta ba amma tace maybe a yau din zata koma". Nan fa Aisha ta zage ta shiga kitchen ta shirya wa Umma towon shinkafa miyar taushe, duk gidan duk wanda yaci sai da yayi santi, Aunty da ta ji dadin abincin har da dauko food warmer ta debar wa mijinta ta ajiye masa, tace "wannan girkin naki Aisha in kika yi aure ai sai kin siye mijin da danginsa, kai har abokansa sai sun tattaro sun dawo gidan ki" ana ta dariya amma ita Aisha zuciyar ta bata yi mata dadi sam.
Har suka gama abinda zasuyi suka yi wanka suka shirya, suka dawo palour suna kallo tare da Hafeez wanda yau baije makaranta ba, Aisha ta duba agogo taga 12:30, ya kamata ace su Umma sun iso yanzu tunda da wuri tace zata taho. Aisha ta kalli Khadija tace "Khadija kira Umma kiji ya suke, waya ta babu kudi" Khadija ta tabe baki tace "nima banni dashi" Hafeez ne yayi dialing number din Umma, tana ta ringing ba'a dauka ba, yace "maybe suna hanya, dan kinsan ku mata saiku saka waya a jaka, wani lokacin ayi ta kira ba zaku ji ba".
Wasa wasa har karfe biyu babu Umma, yanzu hankalin Aisha gaba daya a tashe yake, da kanta ta yafa mayafi ta fita shago ta siyo kati ta saka ta kira number din Umma, wannan karon a rufe taji layin, ta kuma kira a rufe, Aunty tace mata "gwada number din abbanku kiji yaushe ta taho? Maybe bata samu tahowa da wuri ba kuma wayar babu charge" jikin Aisha yana ta rawa ta kira abban, bugu daya ya dauka yace "ta karaso ko? Nayi ta kiranta wayar a kashe" a hankali Aisha tace "bata karaso ba Abba, muma ita muke ta kira yawar bata shiga" yayi tsaki yace "yanxu haka bata da chaji, ace mutun zai yi tafiya amma ba zai cika wayarsa da chaji ba? In ta karaso kya kira ki fada min" Aisha tana kokarin ta tambayeshi time din da suka taho amma har ya katse wayar, ta ajiye tayi wa anti bayani.
Har karfe uku tayi shiru, a yanzu kam har Khadija ta fara daga hankalinta, suna kokarin su sake kiran Abba sai ga baban su Aminu ya shigo, aunty tana ganin shi tasan babu lafiya dan in ya tafi kasuwa tun safe baya dawowa sai anyi sallar magriba. Tsaya wa sukayi duk suna kallonsa, shima kallon nasu yakeyi, sai kuma ya sunkuyar da kai yace "ku dauko hijabanku zamu tafi dutse" wani irin jiri Aisha taji ya debe ta, tayi sauri ta zauna akan kujera ta dafe kanta da yake barazanar rabewa biyu, Khadija da sauri ta sha gabansa tace "me zamuyi a dutsen? Ba mune zamu je dutse ba Umma ce zata taho kano, ta taho ma tana hanya yanzu" bai bata amsa ba ya shige daki, da sauri aunty ta bishi, kawai sai kukanta suka jiyo, Khadija kam afka musu tayi dakin tace sai sun gaya mata me yake faruwa, kuka kawai aunty take yi, ta jawo Khadija ta rungume ta, itama sai kuka, Aisha hawaye babu shi a idonta sam, sai maimaitawa take a ranta, "babu abinda ya samu u
Ummata, babu abinda ya samu Ummanta"Tana nan a zaune kawai taji aunty ta saka mata hijab sannan ta kama hannunta, daya hannun kuma tana rungume da Khadijah wadda take neman shidewa saboda kuka, a haka ta saka su a mota itama ta shiga, Baba yana gaba Hafeez yana tukawa suka dauki hanya.
A hanya Umma ta dauko waya ta kira tana kuka, tace "yaya Sadisu kaji abinda ya same mu yau? Allah yayi wa Rabi'a rasuwa dazu. Accident sukayi a hanyar...."
Sai kuma kuka yaci karfinta ta kasa karasa maganar. Wannan shine mugun jin da Aisha ba zata taba mantawa ba. Ta jin gina kanta a jikin murfin mota ta rufe idonta amma har yanzu babu hawaye, tana jin Khadija da aunty suna ta kukansu amma ita ta kasa, addu'ah kawai take yi a ranta akan Allah yasa a kira ace ba haka bane, ko ace dogon suma tayi amma yanzu ta farka tana nemansu, ko kuma suje su tarar da ita tana jiransu da dariya a fuskarta tace "wasa ake muku fa, so muke ku dawo gida saboda gidan duk babu dadi in bakwa nan".
Amma ina, suna yin packing suka tarar da taron mutane fal a kofar gidan su, duk da haka Aisha fada wa kanta take cewa "'yan dubiya ne, yanzu zasu ce mana ai ta tashi tana ta neman mu" tsakar gida ma a cike yake da mutane, yawanci kawayen Umma da kuma makotanta, suna shigowa kusan rabin mutanen gurin suka saka kuka, Mama ta taso da sauri ta rike Aisha, gwoggo kuma ta rike Khadija suka shiga dasu dakin Umma, anan suka ganta, a kwance akan tabarma a tsakiyar dakin, kamar wacce take baccin rana, amma kuma me yasa zata kwanta tayi bacci bayan gidan a cike yake da mutane?
YOU ARE READING
Aisha_Humairah
FanfictionIt is a story about two sisters that are like the two sides of a coin, totally different yet part of each other. It is a story about loneliness, sadness, discrimination, hypocrisy, self pity and of course love. Get your handkerchiefs ready because t...