Sai da Khadija tayi breakfast sannan Aisha ta hada mata ruwan wanka a baho, ta zuzzuba sabulan wanka kala kala wanda har saida ta fara tunanin anya bata hada wani chemical reaction din ba kuwa? Sannan ta sa Khadija ta cire kayanta kaf ta zuba a leda aka fita dasu sannan ta shiga ruwan ta kwanta kawai. Aisha tazo da kanta ta bude kan Khadija da niyyar wankewa amma abinda ta gani yasa ta mayar mata da shower cap din ta rufe. Gashin Khadija yana nan irin na fulani amma yanzu ko hannu ba zai iya shiga cikinsa ba ballantana comb saboda dankarewar da yayi a fatar kanta, Aisha tasan babu abinda ba za'a samu ba a cikin gashin nan, kwarkwata, dandruff da kuraje. Sai da Khadija tayi 30 minutes a cikin ruwan sannan Aisha ta taimaka mata suka chuda jikinta, amma abin mamaki duk hade haden da Aisha tayi a cikin ruwan sai taga ko kumfar kirki baiyi ba saboda dattin jikin Khadija ya kashe kumfar. Anan Aisha ta fara tunanin wannan wacce irin prison ce Khadija ta zauna a ciki? Ita dai a iya sanin ta government tana kula da prisoners tun daga cinsu da shan su da tsaftarsu har kula da lafiyarsu, amma bata jin Khadija ta samu wannan kulawar, why? Amma bata tambaye ta ba, tasan she will tell her duk lokacin data shirya.
Sai da tayi mata ruwa uku sannan ta rabu da ita ba wai dan ta fita ba sai dan an dan rage babu laifi. At least yanzu zata iya fita da ita zuwa wajan gyaran jiki. Sai data samo kayanta wadanda sukayi mata kadan basa shiga jikinta sannan ta kawo wa Khadija, amma sai ga Khadija tana yawo a cikin kayan kamar ta saka buhu. Haka dai ta lallabata ta shirya ta tace tazo su fita. A palo Khadija ta tsaya tana rarraba idon ko zata ga Humairah amma taga bata nan. Aisha tace mata "sun tafi islamiyya da twins, yau weekend ba boko sai islamiyya suke zuwa bayan la'asar su dawo" Khadija tayi rau rau da ido tace "Aisha ke kam kinji dadinki, zuciyarki mai kyau ce, kin rike Baby da gaskiya tun kafin kisan 'yar uwarki ce, kuma yanzu ma kin rike ta duk da kinsan 'yata ce" Aisha tayi murmushi tace "Humairah is a very good girl. She deserves a good life, kuma shine abinda zata samu insha Allah"
Khadija ta goge wahayen daya taro a idobta tana tuno kaddarar data rabata da Humairah, lallai ubangiji yana yin komai nasa a bisa dalilin dashi kadai yasani, wato ya raba ta da Humairah ne saboda yasan cigaban zamansu a tare zai kasance cutarwa ne ga Humairah shi yasa ya raba ta da ita daga karshe ya hada ta da inda zata samu kulawar data dace da ita.
Basu fita daga gidan ba sai da suka biya ta BQ gurin yasaiyadi suka gaya masa zasu fita su dawo, ya tambayesu Humairah Aisha ta sanar dashi tana makarantar islamiyya amma ta kusa dawowa. Maganar islamiyyar nan tayi masa dadi sosai. Daga nan gurin wani gyaran jiki suka je, gurin da Aisha takanje ayi mata kitso, manicure da pedicure ko kuma duk sanda take so tayi pampering jikinta. Suna yin gyaran jiki kuma suna sayar da duk wasu mayuka na gyaran jiki wanda suka dace da kalakakan skins. Suna zuwa Aisha tace a gyarawa Khadija kanta first. Sai da aka saisaye gashin Khadija aka mayar dashi kamar na maza sannan aka samu aka wanke shi tas aka cire duk wata halitta da take ciki. A take Khadija taji wata irin iska tana shigarta, ji take kamar ta kwanta a gurin tayi bacci. Daga nan suka koma hannayenta da kafafuwanta. Sai da aka jikasu a wani ruwa na musamman sannan aka zo aka kankare fason kafarta sama sama aka shafe kafar da mayuka na musamman da zasu taimaka gurin healing kafar sannan aka yanke mata faratanta na hannu dana kafa aka gyara su tas.
Bayan sun gama ita da kanta ta zauna take ta tattaba hannunta, ji take yi kamar ba nata ba. Kafin su bar gurin aka hada mata mayukan da zasu taimaka gurin gyara mata fatarta data lalace, mayuka da magungunan da zasu gyara mata gashinta, aka kuma bata shawarwarin yadda zata cigaba da kula da jikinta.
Daga nan bayan Aisha ta biya kudi sun fita sai gurin gyaran baki. Khadija bata san irin dattin da hakoranta sukayi ba sai da aka fara wanke mata su, ana yin wanki na farko aka bata wani ruwa akace ta kuskure bakin dashi ta zubo a wata tasa, wani irin datti data gani sai da taji kunyar duniya duk ta lullube ta. Haka aka kankare mata hakorin tas aka wanke mata shi. Sai wani numfashi mai dadi take shaka tana ajjiyar zuciya. Basu sayi kayan sawa ba saboda Aisha babu abinda bata sayarwa na sakawa sai under wears. Dan haka su kadai suka siya. Ba kadan ba, account din Aisha ya girgiza, dama kuma gashi bata farfado ba daga gini da kudin data kashe gurin walima, amma ko a jikinta. Abinda tayi da kudin a gurin ta yafi kudin muhimmanci.
BINABASA MO ANG
Aisha_Humairah
FanfictionIt is a story about two sisters that are like the two sides of a coin, totally different yet part of each other. It is a story about loneliness, sadness, discrimination, hypocrisy, self pity and of course love. Get your handkerchiefs ready because t...
