Tunda Aisha ta shiga dakin Abba gwoggo ta ganta, sai ta rabu da ita saboda tayi tunanin tana so ta kadaice ne shi yasa ta shiga can din, amma kuma hankalinta yana kan dakin. Sai da suka gama cecekucen su da aunty Bilki sannan 'ya'yanta suka jata dakinta ta zauna suna ta maida magana, amma still tana jin hankalinta yana kan dakin Abba. Ji take yi a jikinta kamar da akwai wani abu daya kamata tayi wanda bata yi ba. Can dai ta kira Shema'u tace "je ki ki zauna da Aisha, tana dakin babansu, zaman ita kadai babu dadi" Shema'u ta tashi ta tafi.
Tana zuwa tayi knocking kofar taji shiru, tayi sallama taji shiru, sai kawai ta koma gurin gwoggo tace "ina jin tayi bacci ne, nayi magana naji shiru" gwoggo tace "wanne irin bacci kuma? Ki dai je in ma baccin take yi ki zauna a kusa da ita". Shema'u tana komawa direct ta bude kofar ta shiga, a kan gado ta ga Aisha a kwance, tayi sallama babu amsa, ta matsa kusa da ita taga idonta a rufe, a zuciyarta tace "ikon Allah, wannan wanne irin bacci ne kike yi Aisha?"
Ta zauna akan bedside kenan taji kafarta ta taka wani abu mai danshi, mai kauri kuma mai danko, da sauri ta kalli gurin, wani irin bugawa zuciyarta tayi da karfi wanda sai da taji shi har cikin kanta kafin tayi wani abu taji wani abu ya zubo akan kafar tata, ta bi gurin da abin yake tahowa da kallo, idonta ya sauka akan hannun Aisha da yake reto a bakin gado, wani irin amai taji ya taso mata ganin katon yankan da yake kwance a wrist din Aisha, bata san sanda ta kwalla kara ba da duk kan karfinta, sai bayan da ta yi karar kuma sannan ta tuna cewa in bala'i ya samu innalillahi wa inna ilaihir rajiun akeso musulmi ya fara yi ba ihu ba. Nan ta dauki salati tun karfinta take yi, tama kasa taba Aisha saboda tsabar rawar da jikinta yakeyi. Abinka da gidan biki, nan take mutane suka yo dakin, kowa yazo yaga Aisha sai ya bi layin Shema'u gurin ihu ko kuma salati amma an rasa mai courage din ta ba ta.
Aunty Bilki ce kusan karshen shigowa, da sauri ta durkusa gaban Aisha ta saka hannunta daya ta rufe jijiyar da take fitar da jinin sannan ta saka daya hannun a side din wuyan ta ta saurara tana son taji bugun zuciyarta, ta jima a haka amma bata ji komai ba nan take idonta ta fara kawo kwalla tana kiran sunan Allah "ya Allah kar ka dauki ran wannan baiwa taka a wannan hali, ya Allah kai mai tausayin bayin ka ne Allah ka tausayawa baiwarka Aisha ka kara mata tsahon ran da zata tuba akan laifin da tayi maka, ya Allah kar ka dauki ranta a lokacin data aikata sabo a gareka bayan kuma ita din tayi rayuwa a bisa biyayya a gareka, Allah mun tuba Allah, Allah ka yafewa Aisha ka yafe mana baki daya" ta kife kanta a cikin Aisha tana rera kuka.
Gwoggo ce ta fita waje da sauri zani a hannu tana neman maza su kawo musu agajin motar da za'a kai Aisha asibiti, duk kuwa da cewa kusan duk mutanen da suke gurin sun gama fitar da rai da Aisha saboda yawan jinin da yake kwance akan carpet.
Wani makocinsu ne ya shigo da kansa har cikin gidan, yana ganin Aisha yace a kawo masa dankwali, ya yaga ya daure hannun Aisha tamau yadda zai tsayar da zubar jinin sannan ya dauke ta ya fita da ita. Suna fita Abba yana kawo kai, an kira shi a waya an gaya masa, yana magana amma aunty Bilki ko kallonsa bata ji ba ta shige mota ta rungume Aisha tana kuka marar sauti, da sauri Abba ya bude gaban motar ya shiga, ya juyo yana taba fuskar Aisha wadda tayi sanyi kalau, nan take jikinsa ya kama rawa yana kiran sunan ubangiji "na shiga uku yau me zan gani, na kashe 'yata da kaina, wannan wacce irin masifa ce ta sauka a gidana, Aisha kar ki mutu ki barni da alhakin ki a kaina" sumbatu yake tayi shi kadai har suka isa asibitin babu wanda ya kula shi, jikin Aisha sai kara saki yake yi yana kara yin sanyi, suna zuwa asibiti emergency suka zarce da ita, da sauri su Abba suka shiga suka kira nurses aka fito da gadon asibiti aka dora Aisha akai aka kuma saka mata oxygen, duk da dai har yanzu babu numfashin a tare da ita, aka tura ta zuwa ciki su kuma suka tsaya daga waje.
Kafin kace meye wannan waiting room din ya cika da mutane, da 'yan 'uwa da suka zo biki da kuma 'yan unguwa da sauran 'yan gari da suka zo tsegumi dan su samu na adarwa. Ba'a jima ba sai ga Yakumbo tare da Innar Kamal da Maryam sun zo suma. Maryam idonta ya kumbura luhu luhu alamar ta ci kuka ta koshi.
YOU ARE READING
Aisha_Humairah
FanfictionIt is a story about two sisters that are like the two sides of a coin, totally different yet part of each other. It is a story about loneliness, sadness, discrimination, hypocrisy, self pity and of course love. Get your handkerchiefs ready because t...