💞💞💞
💞💞hamrah💞💞💞💞
Writer: fateemah Muhammad gurin
Wattpad: muhdfatimagurin
* 'yar mutan Adamawa *
Page ➡️5️⃣
**********
Kwance yake a kan gadonshi ya takure sossai se kace alamjirin da ya rasa makwanci idonshi a runtse me yasa be ji daadi ba da hamrah ta amince bayan shi ya bukaci hk? Sam ba haka ya so ba yaso karasa rayuwar shi ne a hk shi kadai, tabbas ya san kwanakin shi ba masu yawa bane a duniya abu daya ne ya rike shi har ya kai warhaka..............."Fansa" yeah he's just alive bcos of that, rayuwanshi is full of miserable be san amfaninshi ba, bashi da kowa bashi da wadda ze gani ya ji daadi, wani irin shesheka ya fara ba tare da hawaye ya zubu ba shi da ze samu kukan ya zo ma da ya fi farin ciki amma abu ne me matukar wuya kirjinshi ya dafe yana murkususu a kan gadon idonshi kaman an zuba yaji tsabar jan da yayi...............
Hannunshi na rawa da kyar ya samu ya danna wani kararrawa se ga yaqoob ya shigo ganin me gidanshi a wannan hali yasa shi karasawa da gudu ya bude bedside drawer ya dauko wani farin roba karami maganin ciki ya zazzago se gasu guda biyu a hannunshi da gudu ya koma wajen fridge ya dauko ruwa me rangwamen sanyi ya haura gadon da kyar ya samu haisam ya sha maganin a take ciwonshin ya lafa ya kwanta a kan pillow tare da lumshe ido yana sauke ajiyar zuciya, fita yaqoob yayi yana me tausayawa oganshi bai gushe ba kullum se yayiwa oganshi adu'ar samun farin ciki a rayuwarshi............
*********
Washegari da sassafe ta shirya ta nufi airport da kyar ta samu jirgin India amma na yamma dawowa gida tayi ta hada kaya 'yan daidai a cikin trolley dinta, bayan ta gama ta koma part din mahaifinta tana kula dashi dayake mom na da case da safen, hira sossai sukayi da dad dinta ta kara karfafa mishi gwiwa a kan maganan company dinsu a haka har mom ta dawo sallama ta mishi tare da komawa dakinta ta kwanta a kan gadonta tana kara gwada layin simra na india amma duk daya switch off...................Kiran yaqoob tayi yana dagawa suka gaisa cikin mutunci kafin tace "ka cewa mai gidan ka idan ya gama shiri ze iya turowa gidanmu wurin dad dina don ko ya kira baze sameni ba sbd zan tafi india and I don't really know when I'm coming back" cikin mamaki yaqoob yace "ban gane ba turo me?" Cikin bacin rai tace "just tell him what I said" har zata kashe wayan tace "and batun company zasu iya signing contract din da assistant na kafin na dawo".............
Dip ta kashe wayan ta bar yaqoob da tunani wai me oganshi ke shirin yi ne? Tabe baki yayi ya karasa parlorn da sallama don isar da sakon CEO of fareed tower.............
Bayan laasar ta shirya cikin mafi soyuwar shigarta Arab gown peach color ba karamin kyau tayi ba iyayenta da kansu suka raka ta airport kasancewar dad yaji sauki sossai sallama tayi dasu kafin jirginta ya lula se New delhi, tana sauka ta tari taxi har gidan su simra ta sallame shi tare da jan trolley dinta ta nufi ciki da sallama ta tura kofar parlorn..............
Idonta ne ya sauka a kan wurin da mahaifin simra ya saba zama kullum in ta zo a wurin yake wuni komai a wurin yakeyi hawaye ne taji ya cika idonta Allah sarki bestie, ji tayi an rungumeta da sauri ta kalle wadda ya rungumetan tsugunawa tayi ta rungumeshi itama kawai se ya fashe da kuka breaking hug din tayi tana shafa kanshi cikin harshen indiyanci tace .................
"Uhmmm Arjun inace kai soja ne?" Gyada kai yayi tayi murmushi tukun tace "toh ai sojoji basa kuka ko kana so ka zama rago ne?" Sake girgiza kai yayi tace "good boy oyaa wipe the tears" sharewa yayi, ta kara cewa "where is Ammah?" Da indiyanci yace "she's in the kitchen" tace "ohk" kafin ta mika mishi trolley dinta jaa yayi ya nufi upstairs don kaiwa dakinsu ita da simra ita kuma ta nufi kitchen................