💞💞💞
💞💞Hamrah💞💞
💞💞
Writer: fateemah Muhammad Gurin
Wattpad: muhdfatimagurin
*'yar mutan Adamawa*
*Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! I dedicated this page to "Mu Karu da Juna" group thanks for your prayers na ji sauki sossai and in shaa Allahu hamrah yazo karshe two pages to go........
Page➡️3️⃣9️⃣
*************Yau kwana uku kenan da aka sallamota daga asibiti sossai ta saba da duk 'yan uwansu haisam ta bangaren mahaifiyarshi zasu fita dasu Iman su zaga tana nuna musu gari, shopping ne gidan kawayenta ne, wurin aikinta ne da dai sauransu duk kuma a fitan da sukeyin nan bata ta'ba tambayar haisam ba hasali ma se sun fitan yake sani wani kam sede yaga shigowarsu sossai abun ke damun haisam tunda hamrah tayi sauki ko hannunta taki yarda ya rike se ya yini be ganta ba iyakacinta kwana a bangarensu kwanan ma d'aki daban daban tun yana tambayarta matsalanta har yazo ya fita harkanta shima gudun ruwan ta yake son gani tunda ya san shi be mata wani laifi ba but weird halintan hurts him a lot................
Kwance yake kan doguwar cushion dake a parlorn part d'insu ya dulmiya cikin duniyar tunani sagir ya tafi jiya da yamma sbd nemanshi da akeyi a office, kaman daga sama yaji sallamanta a hnkali ya amsa kallon bakin kofar yayi se yaga itama shi take kallo abu tazo d'auka sam batayi zaton samunshi a part d'in ba da bata shigo ba, 'bata fuska tayi ba tare da ta ce mishi komai ba ta nufi d'akinta tana shiga taji an turo kofar da sauri ta juyo tana kallonshi shima ita yake kallo he missed old her so very much sam be san lefinshi gareta ba....................
Matsowa ya farayi jikinta ita kuma ta fara matsawa baya a haka a haka har suka isa jikin gini hannunshi yasa ya dafe ginin gefe da gefenta ya rankwafo sossai kanta da d'an fusata tace "wai me haka ne dan Allah?" A hankali yace "tambaya kike? Wai hamrah me ke damunki ne? Laifinme na miki da na chanchanci shariya daga gareki?" Da sauri ya matsa ganin ta rufe hanci tana kuma kokarin amai don sossai take kakari da mugun mamaki yake kallon hannunta da ta rufe hanci dashi he just can't believe this ba de shi ke wari ba, runtse ido yayi yana fatan kar tunaninshi ya zama gaskiya don baze iya ba wlh, da gudu tayi bayi tana kwarara amai jin amantan yayi yawa yasa ya nufi bayin don ya taimaka mata yana shiga ya riko ta jikinshi ganin yadda take layi da sauri ta fisge jikinta tace "bana so haisam Dan Allah ka dena zuwa kusa dani" cikin sanyin murya yace "meyasa?" Shiru tayi seda ya kara matsota tukun tace da karfi "wari kakeyi sossai wlh" zaro idonshi yayi yana kallonta maganan ya dake shi, shi ke wari? Jikinshi ya shunshuna kamshin fitinannun turarukanshi ke tashi maida kallonshi yayi zuwa kanta se kawai ya juya ya fice da sauri kuka ta fashe dashi tana zamewa a kasan bayin ta had'a kai da gwiwa......................
Sossai tayi kuka tana sonshi ba wai bata sonshi ba amma ta rasa me yasa in yazo ganganta se take jin wari da tsananin tashin zuciya ga wani haushinshi da ta rasa dalilin da yasa take jin hakan a ranta kuka ta ringayi na kusan mintuna 40 tukun tayi wanka jiki a sanyeye ta fito ta shirya cikin wando da riga da ya sauka mata har gwiwa rigan yellow wandon kuma black color se ta samu veil black tayi wrapping kanta dashi yellow flat Vincci shoe ta saka tayi wanka da turarukanta ta d'auki wayanta ta fito a parlor ta sameshi yanzu ma yayi wanka sanye yake da maroon Armani shirt se dark blue Jean da ya haska shi sossai gashin kanshinnan a gyare se sheki yakeyi kallon kallo suka tsaya yi, ya bata tausayi sossai ta san yadda yake sonta hk itama tana sonshi amma ta kasa zama dashi suyi solving matsalansu yanzu ma ba yadda ta iya ne ta furta mishi d'auke kai tayi ta nufi kofa ji tayi yace "hamrah!!!" Muryanshi a matukar sanyaye.................