Page 15

1K 110 1
                                    

💞💞💞





💞💞hamrah💞💞



💞💞

Writer: fateemah Muhammad gurin

Wattpad: muhdfatimagurin

*'yar mutan Adamawa*

Page➡️1️⃣5️⃣
************

A hankali take saukowa cikin yanayin tafiyarta kaman me yanga tunda ta fara saukowa idanunshi a kanta duk da baza ka taba gane hakanba sbd a kwance yake jikin kujera idanunshi a lumshe har ta karasa saukowa be motsa ba ita kuwa idanunta akan su qudra yanayin fuskanta ya nuna tausayinsu don ta lura yarinyar a matukar tsorace take se kalle kalle take.................

Kan kujerar dayake zaune ta nufa da yake three seater ce a chan karshe ta zauna tana gaida mammi amma se taga tana ta shiririta da alamu de hankali be ishe ta ba amsa gaisuwar qudra tayi taja bakinta tayi shiru, a hankali ya bude lumsassun idanunshi ya sauke a kanta gabadaya kaman baze ce komai ba kuma se yace "ki basu masauki me kyau da abinci" cikin cika umarni tace "an gama" ta mike ta nufi wani daki a kasan ta bude................

A gyare yake tsab kaman da mutum a ciki seda ta tabbatar da komai lafiya ta fito tana kallon qudra a hankali tace "zaku iya karasowa" mikewa qudra tayi tana rike da hannun mammi suka shige dakin har hamrah, bayi ta shige tare da kiran qudra ta nuna mata yadda zatayi komai da yake yarinyar ba laifi akwai saurin daukan abu tsab ta fahimta se cewa take "mun gode Anty" ..................

Duk da alamu sun nuna qudrar zata girme ma hamrahn murmushi kawai hamrahn ke mata ta kara jaddadda mata "ki tabbatar kin wanke mama da kyau plz kuma ki wanke kanki da kyau bari na samo muku abinci da kayan sawa" da "toh" ta amsa tana fitowa suka hada ido da shi ya kafe kofar da ido murmushi ta sakar masa da ita kanta bata san sadda ya kubce mata ba da sauri ta haura sama.................

Cikin kayan sawanta ta zakulo wani garen mata irin bubu dinnan da ake daurewa da igiya kaman belt ta san ze yima mamar sbd sam bata da kiba sossai, hk ta dubawa qudra da kusan jikinsu daya sede zata dan fita tsai doguwar riga Dubai fashio me kyau ta fito abincin da ta girka ba wani yawa ne da shi ba tana da stew a fridge se kawai ta daura shinkafa ta fice don kai musu kayan.................

Yana nan zaune yadda ta barshi fuskan nan a hade ya kurawa wayarshi ido sabanin dazu da fuskanshi ke sake duk da ba murmushi yakeyi ba be dago ba har ta shige dakin da ta sauke su qudra ta samu basu fito ba se ta ajiye kayan ta kuma komawa yanzu waya taji yanayi da sagir cikin zafi yake magana "wai ni sukewa barazana? Wlh Allah basu isa in ja musu baya ba Alkawari ne se na tabbatar da kashe su da hannnu na" zaro ido hamrah tayi tana mamakin furucin nan nashi bata san me sagir ya gayamishi ba taji yaja tsaki tare da kashe wayan da sauri ta karasa hawa...............

Tana tsaye a kitchen tana duba shinkafan hannunta a kugu tana mamaki kisa? Toh waye ze kashe? Dafe kanta tayi don har ga Allah furucin ya dake ta a haka har ta gama ta duma miyan ta jujjuye a flask ta saka a tire tare da plates, spoons da ruwa ta gangara, da sallama ta shiga a lokacin har sun gama shiri ita mamar tana kwance shiru se ka rantse me hankali ce yarinyar na zaune a gefenta ajiye abincin tayi daga kasa tace .................

"Ya sunanki?" Cikin murmushi tace "qudratullah" murmushin hamrah ta mayar mata tana cewa "masha Allah suna me daadi, yanzu taso mama ku ci abinci" Da toh qudra ta amsa tana tashin mamar nata ita kuma hamrah ta basu guri Dan su ci a natse da tunanin maganan haisam ta kwana sossai abun ya tsaya mata gashi tana tsoron yi mishi magana..............:...

Zaune suke da yaqoob a cikin garden suna tattaunawa akan companies dinsu duk da yamma ce lis don an kusa kiran magrib, duk da suna cikin gida daya amma tunaninshi be nan Sam ya rasa dalilin shigo mishi tunani bayan suna gida daya se da ya nisa ya gama hada abunda ze fada tukun yace "in tambayeka mna?" Yaqoob yace "yes boss" yamutsa fuska yayi tukun yace .......................

Hamrah💞💞Where stories live. Discover now