Page 24

1.1K 123 8
                                    

💞💞💞






💞💞hamrah💞💞



💞💞

Writer: fateemah Muhammad gurin

Wattpad: muhdfatimagurin

*'yar mutan Adamawa*

Page➡️2️⃣4️⃣
************

Bayan mintuna 30 an samu an kamo Alhj murtala da kyar don shirin guduwa yayi amma se Allah ya ba polisawan nasara kan ya bar Abuja sukayi ram dashi, a gaban Alkali aka gurfanar dashi Aka sa shi rantsuwa kuma ya fad'i gaskiyar abunda ya sani, fir yaki yace shi be san komai ba, ba yadda ba'ayi dashi ba yaki ga hisham dake ta aikin ihu sbd azabar zogin da kafanshi ke mishi shima aka tambaye shi ya fad'i gsky yaki sam..................

Umarni Alkali ya bayar akan a tafi dasu a tambayesu a ajiyesu a gidan horo na sati biyu a horasu har se sun fad'i gaskiya and court ta sallami haisam sbd he is not guilty he's also a victim, amma duk da haka court na bukatar shi ranar da za'ayi shari'ar karshe bum bum bum, ya buga aka mike tsaye, ya fice abinshi, murna a wurin hamrah, dad, mom, qudra, yaqoob, Aisha da mammi kaman su zuba ruwa a kasa su sha..................

Mutane se tayashi murna suke suna tsinewa su Alhj mudan iyalansu duk da sukazo kunya kaman suyi yaya a haka aka watse, kishingid'e yake a bayan mota tana zaune gefenshi yaqoob ke tukawa yayinda Aisha ke zaune a gefenshi, idonshi a lumshe ya rasa wani irin yanayi yake ciki sam ga yana jin ciwon zuciyar nan na kara damunshi hannunta yaji cikin nashi a hankali ya bud'e idanunshi se suka sauka cikin nata murmushi me sanyi ya sakar mata itama ta mayar mishi tare da kwanciya kan kafad'arshi..................

Da sauri ya zame tare da matsawa kallon tambaya ta mishi da sauri kuma ta dafe kanta tana cije baki a hankali yace "menene?" Seda ta nyamutsa fuska tukun tace "headache amma ba sossai bane" yace "ko zamuje asibiti ne?" Kai ta girgiza mishi tare da murmushi shiru yayi sbd shi be san ance zata iya samun matsala a kai ba sbd hatsarin, har suka isa gida ba wadda ya kara magana se massaging hannunta da yakeyi.................

Direct d'akinshi ta wuce dashi dayake itama ba gidan take kwana ba da safennan ma aka bata sallama a asibiti yasa d'akinshin ba a gyare ba duk da tsab yake se d'an kura a bakin gado ta ajiyeshi ta shige toilet dinshi, gyalen kanta ta maidashi d'ankwali ta wanke bayin tsab tukun ta had'a mishi ruwan wanka me d'umi da kamshi tanayi tana tuna sanda ta had'a mishi ruwa me zafi zagin duniyan nan tana ga ba wadda be mata ba da sauri ta kau da tunanin tare da fitowa ta mika mishi towel dinshi.......................

Kar'ba yayi tare da mikewa a gabanta ya fara cire kayan jikinshi zaro ido tayi ta juya da sauri zata gudu cikin azama ya jawota ta dawo kan kirjinshi hannunshi yasa ya zagaye cikinta dashi tukun ya kwantar da kanshi kan wuyanta yana shinshuna ta cikin shagwa'ba da bata ta'ba ganin wani namiji ko jinshi dashi ba taji yace "Ina kuma zaki??? Ni ni fa ke zakimin wankan" zaro ido tayi tana jin yadda maganan yayi mata tasiri har zuciyarta a take tsikar jikinta suka fara tashi gyaran murya tayi tama rasa me zata ce..................

Murmushi me sauti yayi tare da sakinta yana cewa "tunda baza amin ba shikenan" satar kallonshi tayi ya tura lip dinshi na kasa gaba kad'an ba karamin kyau ya mata ba, juyowa yayi se suka had'a ido right eye d'inshi ya kashe mata tare da d'age gira yana tambayar yaya dai, girgiza kai tayi tare da ficewa tana murmushi shima murmushi yayi kan ya gama cire abunda ze cire ya fad'a toilet...................

Seda ta tabbatar ya shiga wankan tukun ta dawo d'akin sauri sauri ta gyara tana jin ciwon kanta na karuwa bayan ta gama ta nufi kitchen ta fara had'a mishi abunda ze ci jollof na cous cous tayi yaji veggies masha Allah ta had'a mishi zobo ta tattara ta kai dining ta dawo ta gyara kitchen d'in tana stepping foot d'inta out yana fitowa daga room d'inshi kallonta ya tsaya yi se yaga kaman tana layi a hankali ya nufe ta kan ya karasa ta tafi luu zata fad'i da sauri ya tare ta tare da rungume ta a jikinshi yana bin fuskanta da kallo a hankali ta bud'e idonta da sukayi jaa tana kallonshi ta kara mayar wa ta lumshe....................

Hamrah💞💞Where stories live. Discover now