💞💞💞
💞💞hamrah💞💞
💞💞
Writer: fateemah Muhammad gurin
Wattpad: muhdfatimagurin
*'yar mutan Adamawa*
Page➡️8️⃣
************Ta kai minti ashirin a tsaye duk kafanta sun gaji gashi tana tsoron zama ya mata rashin mutunci kallonshi tayi hankalinshi kwance yana aikin danna waya zura mishi ido tayi tana kallon hallitan Allah a zuciyarta kuma yabon kyaun shi take, ji yayi a jikinshi Ana kallonshi dago dara daran idonshi yayi ya zuba su cikin nata da sauri ta kawar da kai kasa kasa yace 'Mayya' sarai ta jishi kuma kalmar ta mata zafi amma ya zatayi..............
Rawa kafanta ya fara kaman zata fadi lura da hakan da yayi ne yasa shi nuna mata wani room da yatsa ba tare da yayi magana ba da sauri ta nufi room din tana shiga ta zube a bakin gado tana sauke numfashi "amma Allah ya isa" ta fada afili tana hararan kofan tare da murguda baki, kallon dakin tayi yayi kyau sossai cikin Ash and milk furnitures cornered bedroom ne ba wani tarkace daga gado dressing mirror se wardrobe se kuma wasu coffee table ta jikin window se one siter dake kusa kadan da gadon...................
Mikewa tayi ta bude wardrobe ba komai se akwatunanta guda uku Allah ya taimake ta mom ta aiko dashi tare da masu jera furnitures dama ta riga da ta hada kayayyakin da take son zuwa dashi se ta ajiye a dakin mom bama ta san mom ta turo ba da bata san ya zatayi ba don be mata kayan aure ba Sam...................
Toilet ta fada ta cire kayan jikinta don duk sun ishe ta wanka tayi tare da brush ta fito daure da towel Wardrobe din ta koma ta fito da akwati guda ta bude tare da zaro sabbin man shafa da ta zuba a ciki tare da turarukanta, dressing mirror ta je ta jere su ta ja kujera ta zauna tare da shafe jikinta da mayukanta ta fesa turare ta dawo ta sake bude akwatin ta cire cotton nightie fari kal dogon wando da rigarshi iya cinya me guntun hannu ta saka, zaro dogon hijab tayi ta nufi inda taga an shimfida sallaya ta tada sallah Isha tayi tare da shafa'i da wutiri tana idarwa ta mike ta linke hijab din ta ajiye kan sallayan................
Ta juya da nufin hayewa gado kenan ta ji an turo kofar ido suka had'a da sauri ta kauda kanta tare da zama a bakin gadon ta jayo jakanta ta fiddo wayanta ta fara dannawa, jinginuwa yayi da kofan tare da harde hannunshi a kirjinshi ya zuba mata lumsassun idanunshi ko a jikinta tunda be yi sallama ba me ya dame ta, a hankali ya warware hannunshi tare da zuba su a aljihu ya nufo gurinta cikin takun isa da kasaita................
Yana taku da daidai tsoro fal ya cika ta duk takunshi daya se ya kara bugun zuciyarta har ya karaso hannu ya sa ya zare wayanta dake hannunta ya d'an danna na mintuna tukun ya Mika mata komawa yayi kan one siter ya zauna abunshi ya fara danna waya, rike wayan tayi sossai don tana ji kaman ze kubuce ya fadi yadda jikinta ke rawa duba me yayi dashi tayi se taga yayi dialing number..............
Wani special number ta gani da alamun nashi ne kallonshi tayi, ya hada gabas da yamma ya mai da hankalinshi kan waya tabe baki tayi tare da kunna data ta fara chatting da friends dinta da duk turawa ne se ji tayi sako ya shigo ta sms dinta komawa tayi ta bude se taga special numbern nan kenan shi ya turo mata sakon a zuciyarta tace tsabar miskilancin ne baza a iya min magana da baki ba kenan se ta sms Allah ya kyauta..................
Budewa tayi tare da fara karantawa kaman haka "welcome to HMS prison yard kaman yadda ko wani prison suke da rules and regulations hk nima nake da and you must abide by them, firstly dole idan gari ya waye ki duka har kasa ki gaishe ni ko zan amsa ko bazan amsa ba, secondly my meals three times a day yana wuyanki kuma ba'a yimin abinci kala daya se sama da haka...................