💞💞💞
💞💞Hamrah💞💞
💞💞
Writer: fateemah Muhammad gurin
Wattpad: muhdfatimagurin
*'yar mutan Adamawa*
Page➡️2️⃣8️⃣
************Shiru yayi kaman baze ce komai ba se kuma yace me yasa kike son sani? Nace sbd zargi ba daad'i bawai don ina sha'awar komawa aurenka bne, Shiru yayi yana kallona har ga Allah ni abunda ke zuciyata ne na fad'a don ban da sha'awar yin wani auren In nayi kaman banyiwa Umar adalci ba ko shekara ba'a rufa da rasuwarshi ba ace nayi aure...................
Wayanshi ya d'auko ya nuna min abunda aka turomishi da videonmu a restaurant din da muka ci abinci kan zuwanmu apartment dinshi da picture din da ya d'auka lokacin Umar ze shiga ciki da wata a gefenshi, murmushi nayi hawaye na gangara a ido na Ina tuna moment d'inmu na lokacin dashi da murmushi na kalli Abdallah nace................
Lallai Abdallah kishi ya riga ya rufe maka ido kallon cikina nayi na cigaba Ina shafawa nace tabbas wani baya haifan d'an wani kenan rabon wannan cikin ne yasa ka sakeni, da mamaki yake kallona yace ban gane ba, nace ka manta ni renonka ce Abdallah ko da duniyan nan gabad'aya zasu ce nayi zina na san kai ba me yadda bane sbd kasan abunda zan iya ka kuma san wadda bazan iya ba.................
Ya sake cewa ban gane ba, nace toh me yasa baka ci gaba da tsanata da kuma fushi da ni ba har yanzu? Yace Wlh na rasa wannan dalilin, nace sbd ka yarda dani kenan, Abdallah ka kalli videon mu na restaurant ka kalle ni da kyau ka koma ka kalli hoton da ka d'auka da hannun ka na wata dake kokarin shiga building nasu Umar....................
Kallon videon yayi tare da kuramin ido a cikin wayan yana son gane abunda nake son nuna mishi ya koma ya kalli hoton ya kurawa buduruwan ido, da karfi yace shiiiiiiiiiit Wtf!!!!!! Kau da kai nayi Ina murmushi haushin kanshi ne ya kamashi ganin banbanci karara da be kula dashi ba se yau, kayan dake jikina a cikin restaurant da kayan jikin wancan ba d'aya bane kuma structure na jikinmu ma ba d'aya ba na fita cika da hips sossai ita kuma tsiririya ce kaman zata karye.................
Hawayene ya fara zuba a idonshi yana cewa I'm sorry noor am so sorry na mareki na kuma yi miki fad'a a kan abunda baki aikata ba, nace Abdallah bakayi komai ba abunda kayimin nan ma shine daidai a matsayinka na yayana na cancanci duka fiye da marin da kamin sbd haramcin soyayya da wani bayan akwai aure a kaina wadda na san hakan na take Abdallah ka yafemin danne maka hakki da nayi na dibi fushin Allah da mala'iku Allah baze kama Umar da laifi ba sbd wallahi shima bai sani ba....................
Ina tsoron fad'a mishi ya rabu dani, ajiyar zuciya Abdallah ya sauke yace na yafemiki ukhty Allah yaji kan Umar ya gafarta masa, zan amsa kenan naji ance In kina son yafiyar Allah se ki koma d'akinki ki gyara duk wani abunda kika bata tunda har yanzu d'an uwanki na sonki, kallon kofa nayi Ammi, Abbu, Abbi da Ummi ne a tsaye ashe tunda muka fara magana akan abunda ya raba mu suke tsaye sossai sukayi mamakin boyemusu abu irin haka da mukayi ya kamasu..............
Ko da shike lokacin bazan ji zafin zargi ba sbd murnan zan auri Umar sun yarda da kaddara sun kuma yarda rabon d'an cikina ne ya kashe auren, kowa ido ya zuba min yana jiran jin me zance Abdallah yayi karfin halin cewa ba wadda ze miki dole 'yar uwata In baki so, a hankali nace Allah ya bamu zaman lafiya hawaye na gangaromin, murna sossai iyayenmu sukayi har mamakin murnan Ummi nake ashe tana sona da d'anta amma take kauda kai.....................
A lokacin suka tsayar da Auren bayan na haife abunda ke cikina, wata hud'u da nayi a tsakankanin nayishi ne cikin farin ciki da soyayyar 'yan uwa da iyaye na sossai Abdallah ke nuna min kulawa har nima na fara sonshi duk da har ga Allah be kai son da nayiwa umar ba na yarda kuma so d'aya ne na riga na ba umar ya tafi dashi kabarinshi ban ta'ba mantawa da shi cikin adu'o'i na ba, ranar wani Juma'a na tashi da nakuda.................