💞💞💞
💞💞hamrah💞💞
💞💞
Writer: fateemah Muhammad gurin
Wattpad: muhdfatimagurin
Page➡️1️⃣3️⃣
**********Yinin ranar gabadaya yayi ne a kula da ita duk da yadda wayanta ya tsaya mishi sossai a rai, magana be kara hadasu ba har dare bayan ya tabbatar tayi bacci tukun ya wuce dakinshi waya ya dauka ya kira Alhj mudan "salamu Alaikum an yini lafiya?" Da mamaki Alhj mudan ya kara duba caller Id dinshi tabbas haisam ne yau haisam ke gaisheshi?.................
Da dan rashin gaskiya yace "waslm lfy klau ya iyali" runtse ido haisam yayi tabbas akwai muryan Alhj mudan don be taba mai da hankali akan maganan shi bane yasa da yaji voice recorder din be gane ba, me Abba ya musu mai zafi hk? Akan kudi? Wani irin tsanan Alhj mudan ne ya dirar mishi fiye da baya ba tare da ya kara magana ba ya kashe wayan................
Kiran Alhj halliru yayi shima kamar yadda ya ma Alhj mudan haka ya mishi, tabbas shima akwai muryanshi tar a ciki, a zuciye ya kira Dr zubair shima akwai muryanshi d'ayan muryan ne ya kasa samu ya kira abokan baban nashi kusan biyar duk be ji dayan muryar ba daga baya hakura yayi yayi nafilfilin shi ya kwanta................
************
Ta bangaren su Alhj mudan a take suka hada meeting a daren, a rude suka hadu a wani tangamemen gida da yaji kayan duniya a wani babban parlor suka zazzauna sun kai mintuna 10 da zama kowa yayi shiru tunanin abun duniya ya ishe su suna tsoron Allah suna tsoron tonuwar asirin su..............
Wani babban mutum ne kusan sa'anninsu ya fito sanye da suit bakake ya saka hulan tabani kaji hadisi a kanshi tare da face mask a fuskanshi idonshi da girarshi kadai ake gani a tare suka mike gabadayansu seda ya zauna tukun suma suka zazzauna, "me yake faruwa ne? Bad news" Ya tambaya..............
Dr zubair ne ya fara magana kamar haka "boss yaron nan ne yake son zame mana barazana, bamu da masaniyar wa ya kai mishi voice recorder a takaice ma a lokacin da mukayi maganan ma iya mu hudu ne ya akayi recorder ya fito bamu sani ba, last two days kenan ya kira abokinshi wani soja da secretary dinshi yaron nan da suka tashi tare ya musu bayani a cikin jakan da aka kai mishi recorder din akwai paper rubuce da suna da address din drivern da ya tayamu aiki....................
Sunyi shawarar zuwa washegari a jiya kenan su ziyarci malam isa amma se muka rigasu muka tura aka kashe shi sunje sun Tarar da gawanshi" Alhj mudan ne ya daura da "se yau a dazu ya kira mu daya bayan daya da alamu so yake yaji muryar da yayi kama da na recorder din da alamu kuma ya gane"...................
Shiru wadda akewa bayanin yayi na kusan minti daya tukun yace "good news" Alhj halliru yace "yaron na dauke da ciwon zuciya bamu sani ba se shekaran jiya" wani irin dariya mutumin ya fara babbakawa har na kusan mintuna biyu tukun yayi shiru yana kallonsu se yake sukeyi............
A gadarance yace "in ya san wata be san wata ba kar ku damu I will handle him ubanshi ma yayi ya gama balle yaron da aka Haifa a gabanmu? Ku tashi kuje ku barmin komai" mikewa sukayi suna godiya kaman aljannah ya basu suka fice................
************
Washegari ta tashi jikin da sauki se mura da take yi sossai, shiryawa tayi ta fita ta fara aikinta cikin natsuwa, bata wani bata lokaci ba ta gama hada mishi yam balls da Irish potage da yaji veggies da hanta ta shirya komai a dining ta gyara parlorn tas ta saka turaren wuta, dakinshi ta shiga yana nade akan gado yana bacci kallon fuskanshi tayi da ya fita tar a hasken rana daya taso ta windownshi............Yayi kyau sossai kaman ba bacci yakeyi ba kafa mishi ido tayi tana morewa kallonshi gaskiya kyakyawa ne ya tserewa hisham sossai abunda kawai hisham ze nuna mishi shine hasken fata, amma fatan haisam me tsada ne don d'ai-d'ai kune masu irin fatan, tana cikin kallonshi tana kiyasta komai na fuskanshi ya bude ido tar a cikin nata.................