Page 32

1.1K 99 6
                                    

💞💞💞







             💞💞Hamrah💞💞



                                                     💞💞

Writer: fateemah Muhammad gurin

Wattpad: muhdfatimagurin

           *'yar mutan Adamawa*

"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!! May the mercy and blessings of Allah SWT be with u and ur family now And always, Happy Eid Mubarak Allah ya maimaita mana Ameen summa Ameen.

Page➡️3️⃣2️⃣
*************

Bayan sunyi dinner ne haisam ke shedawa Ammah tafiyarsu baze yiwu gobe ba sbd shiga court da za'ayi cikin next week sede washegari Bayan zaman In Allah ya kaimu, tace "Ba komai Allah ya kaimu" ya kara da "Am ina son gobe in Allah ya kaimu zan tafi lagos bazan dawo ba se ana gobe za'a koma court sbd zan shiga kd, kano da yola Ina ga daga Chan ma zamu dawo da sagir"................

Ammah tace "Ohk Allah ya kaimu" ya kuma cewa "Ammah gobe zaku je shopping da yamma se ku saya duk abunda kuke bukata har trolleys sbd shirin tafiya" zatayi magana yayi saurin cewa "Adu'a Ammah" murmushi tayi kaman ya san ki zatayi se kawai tace "Allah ya kaimu yayi albarka" cikin farin ciki yace "Ameen" ya mike tare da mata se da safe ya haura yana satan kallon hamrah da suke hira qasa qasa da qudra............

Bayan ya shige ne qudra ta fara tsalle tana jin daadi zasu shopping girgiza kai kawai Ammah tayi tana murmushi kallon hamrah tayi tace "habibty tashi maza ba'a barin miji shi kad'ai se da safe" a kunyace hamrah ta mike tana amsawa ta haura, a parlor ta same shi yana zaune gabanshi ATM cards ne kusan guda biyar na first bank ya d'auka ya mika mata ta kar'ba tana tambayarshi "me za'ayi dashi" yace "in kunje shopping se kuyi anfani dashi" girgiza kai tayi tana cewa "A'a be dace ba gaskiya, Ammah baza taji dad'i ba mahaifiyarka ce fa be kamata komai zaka bata ya dinga fita daga hannun matarka ba, ka bata da kanka ka fad'a mata pin d'in hakan ze fi".....................

Gyad'a kai yayi se yanzu yake ganin kuskurenshi hakan ze iya sawa Ammah taji ba daadi murmushi yayi yace "na gode da tunatarwa, yauwa noory dama ina tunani me kike ganin zanyiwa Ammah da ze sa taji daad'i sossai" Shiru tayi tana tunani Chan kuma se tace "ka bari muje jordan d'in tukun" Kai ya gyad'a ita kuma tunani ta fara In har Ammah ta fito daga Hashemite kingdom to ba abunda zata bukata mijinta me kud'i ne sossai haka babanta ba abunda zata nema ta rasa toh me zata ba haisam shawara ya mata? Zata tambayi mom d'inta In shaa Allah....................:

"Ina so inyi having words da qudra" tace "Ohk lemme let her know" ta mike ta gangara bayan ta kirata ta shige d'akinshi don had'a mishi kaya ta barsu a parlor, shiru duk sukayi se kuma yace "hey sis" Kai ta d'ago tana murmushi tace "hello bro" shima murmushi yayi yace "wow ashe kina jin turanci" tace "Eh Ina d'an ji nayi primary a class, secondary ne de sede kullum naje na tsaya a window Ina kallon me akeyi wani lokacin har duka akemin amma hakan baze hana gobe na koma na makale a window ba, dukda government ne amma ba lefi na tsinci abubuwa dayawa"...................

Kai ya gyad'a Allah sarki rayuwa In ba kaddara ba kanwarshi? 'Yar sarkin jordan fa amma suka sha wannan wuya a duniya, don son kau da yanayin da ta shiga yasa shi cewa"me burinki?" Tace "Ina so inyi karatu amma na san yanzu kam ya wuce sbd na girma" yace "and wa ya gaya miki ana girma da karatu" kallonshi tayi da alamun tambaya yace "eh zaki iya yin karatunki Amma aure fa?".................

A sanyaye tace "wa ze iya aurena yanzu yaya? Neman 25 fa nake kuma banda ilimi" idonta ya ciko da hawaye, shiru yayi kaman baze ce komai ba se kuma yace "na miki miji In har kina so fa kenan ze rike ki da gaskiya da amana" tace "shi yace yana sona?" Girgiza kai yayi yace "sam sede nasan ko yanzu na bashi shawaran aurenki ze aureki sbd yadda ya yarda dani ya kuma yarda bazan cuceshi ba, ya kuma san bazan mishi za'bin banza ba".......................

Hamrah💞💞Where stories live. Discover now