💞💞💞
💞💞Hamrah💞💞
💞💞
Writer: fateemah Muhammad gurin
Wattpad: muhdfatimagurin
*'yar mutan Adamawa*
Page➡️3️⃣1️⃣
*******A lokaci d'aya haisam ya cirewa hamrah masifaffen kunyanshi da ta tashi dashi, suna hira irin ta masoya har ya taimaka mata ta shirya cikin doguwar riga Arab gown black me stones gold dayawa a jiki sossai ya mata kyau kuma ya amshi fatanta kasancewarta fara, cikin tsantsan so yake kallonta kanta a kasa a hankali ya furta "kinyi kyau noory" murmushinta me kyau ta sakar mai tare da cewa "thanks" yace "our breakfast is ready" girgiza kai kawai tayi yaja hannunta suka fice da kanshi ya taimaka mata ta zauna a dining taja plate zata serving ya kar'be yana mata hararan wasa, da kanshi yayi serving plate d'aya ya matso dashi ya sa spoon da fork yana bata yana ci har suka gama, duban time yayi yaga har lokacin meeting d'inshi da ma'aikatanshi yayi dama ya fad'awa Ammah da qudra akan su shirya zeyi presenting d'insu ga ma'aikatan gidan gabad'aya................
Hannunshi a nata suka gangara suna isa step na karshe ta zame hannunta ganin Ammah zaune a parlorn se lokacin ta kula da yanayin Ammah a zuciyarta take cewa tab lallai Ammah irin manyan matan nan ne masu ji da kyau, mulki da kudi se yanzu yanayinta ya nuna sanye take da atampha cikin wadda hamrah ta d'inka mata holland ne maroon da adon sea green sossai d'inkin ya mata kyau bata d'aura d'ankwali ba amma ta yana babban mayafi sea green akan tulin gashin kanta da Yasha gyara da kayan gyaran kai da hamrah ta saya musu dama wani kam qudra bata san anfaninshi ba, ta d'aura kafa d'aya kan d'aya remote a hannunta tana chanza tasha suna had'a ido ta sakar musu murmushi me sanyi............
Cikin muryanta irin na haisam me cike da kasaita da isa take cewa "masha Allah, yarana kunyi kyau" ta karasa tana mikawa haisam da ya karaso gabanta hannunta dukawa yayi yayi pecking hannun, abunda ya lura tana matukar so kenan abunka da larabawa cikin sanyin murya yace "thanks Ammah"...........
Har kasa Hamrah ta duka ta gaishe ta cikin fara'a da tsantsar kulawa ta amsa mata kallon parlon yayi yana cewa "Ammah Ina yarinyarnan nifa bana son African time" murmushi tayi tace "Tana shiryawa but ina ga ta gama zuwa yanzu kam" tana rufe baki se ga qudra cikin milk and black gown tayi kyau sossai mayafin rigan ne akanta kaman yadda hamrah tayi cikin burgewa Ammah ke kallonsu a rayuwanta tana matukar so da daraja shigar larabawa amma kuma Allah ya gani soyayyar shigar hausa fulani shima sossai ya shiga ranta maganar haisam ne ya katseta yana cewa "Shall we?".........
Tace "yeah sure" ta mike suka fice ita dashi a gaba yayinda qudra suka jera da hamrah suna magana kasa kasa a haka suka karasa mota ya bud'ewa Ammah baya ta shiga qudra ma ta zagaya ta shiga yayinda hamrah ta shiga gaba don ta san in za'ayi irin wannan meeting d'in shi ke driving motan shiru ya d'auka Ammah na kallon wannan daular da d'anta ke ciki tana tasbihi ga ubangiji..........
A haka suka isa meeting hall d'in ya cika makil da ma'aikatanshi na gidan yana shiga suka mike yau yaqoob yasa an kara kujeru a high table, mic aka ba haisam yayi musu godiya ya kara da yadda yaji daadin nuna kulawarsu a gareshi kuma ko basu mishi jaje ba ba matsala tunda everything is fine and okey now ya kara da gabatar musu da mahaifiyarshi da sister d'inshi.............
A takaice ya basu asalin labarinshi na asali don a ganinshi basu da hurumin sanin gabad'aya tarihinshi tunda ba shi ke kasansu ba su ke kasanshi wannan ma shawaran yaqoob ne don ba yadda ya iya ne ya basu labarin a takaice..........
Anan suka tayashi murna d'aya bayan d'aya suka ringa zuwa suna gabatar da kansu a wurin Ammah a mutunce suka gaisa da musulman da kuma arnan bayan kowa ya watse ne suma suka kama hanyan compound d'insu haisam be shiga ciki ba se ma komawa owners corner da yayi yaqoob ya shiga gaba driver ya shiga securities d'inshi suka zagaye shi da motocinsu suka ja suka bar gidan..............