💞💞💞
💞💞hamrah💞💞
💞💞
Writer: fateemah Muhammad gurin
Wattpad: muhdfatimagurin
*'yar mutan Adamawa*
Page➡️9️⃣
**************Washegari da wuri ta gama duk abunda yake aikinta ta koma dakinta da ya tashi cin abincin ma se da ya kirata tayi serving kuma ta tsaya har ya gama ci tukun ya fice ita kuma ta tattare gurin tayi wanke wanke tukun ta daura abincin rana, bayan ta gama ne ta shirya ta fice zuwa tsakar gidan da sauri wani ya taso zuwa wurinta yace "barka da fitowa hjy, yallabai yace duk inda zakije ni zan dinga kaiki" ba tare da tace komai ba yaje ya fito da mota ta shige shikuma yaja suka bar gidan.................
Seda suka dau hanya tukun ya tambayeta inda sukayi cikin sanyin murya tace "copa cabana" shiru motan ya dauka har suka isa garden din wuri ne Mara hayaniya shiyasa ta zabi zuwa inda zata ji dadin tunaninta da kuma nazari akan sabon rayuwan da ta tsinci kanta sallamanshi tayi Tace yaje duk inda yake so in ta gama zata kira shi ficewa yayi ita kuma ta samu bakin wani ruwa ta zauna akan wasu kyawawan kujeru da aka kawata su...................
Tsam ta tsunduma duniyar tunani, tunda ya shigo gurin yake kallonta kyakyawa ne ba laifi fari sol kaman ka taba shi jini ya fito wani munafikin murmushi ne akan fuskanshi har ya samu kujera dake facing dinta ya zauna a fili ya furta "what a beautiful damsel" lura da yayi ta fada duniyan tunani kuma fuskanta is so pale da alamun akwai abunda ke damunta ya sashi mikewa ya nufe ta.................
A kujeran gabanta ya zauna shima yayi tagumi kamar yadda tayi tare da shagwabe fuska, jin wani kamshin turare na daban yasa ta kallon wurin ganinshi a haka ya tsoratata ta zaro manyan idonta zata mike yayi saurin cewa "Amincin Allah su tabbata a gareki ya ma'abociyar kyaun fuska dana jiki" komawa tayi ta zauna tana sauke ajiyar zuciya................
Murmushi me sanyi ya mata ita ma ta mayar mishi tukun tace "god ka tsorata ni wlh" Dariya yayi tukun yace "matsoraciya kawai by the way my name is hisham nasir and yhu?" Tace "hamrah fareed" zaro ido yayi har ta dan tsorata tukun ya juya su kaman mace tare da cewa "wow what a nice name" dariya tayi tana cewa "wlh kana da ban dariya" yace "haka ake cewa, me ke damun priceless flower ne?".................
Tabe baki tayi tana cewa "you are a stranger you know?" Hada baki sukayi wurin cewa "how can I tell you my problem" a tare sukayi dariya tace "ya akayi kasan abunda zan fada kenan" yace "Kin san ko ina da super power?" Murmushi ne sossai akan fuskanta tace "hmmm I hear this" shima murmushin ya mayar mata a hankali suka fara hira sossai yake jan ta da hira har ta sake suka kwashi hira ta ma manta da wani haisam da damuwar da ya sa ta ciki......................
Hira sukayi sossai a lokaci kankani suka shaku sossai kasancewar hisham me saurin sabo da raha duk wani damuwanta ya kau kallon agogo tayi taga 5pm zaro ido tayi tare da mikewa a firgice har seda hisham ya dan ji tsoro kallonta yake da alamun tambaya kafin yayi magana ta fara magana ta waya "yi sauri kazo muje gida"...................
Katse wayan tayi ta fara Jeka ka dawo tana tunanin abunda zata girka me sauki sbd yace mata baya dinner in har 7:30 ya wuce innalillahi Allah ka tsare ni da bala'in wannan bawa a zuciyarta take maganan har drivern ya iso kallon hisham tayi tace "zan tafi hisham se munyi magana" hannu kawai ya daga mata da tarin tambayoyi a zuciyarshi amma tunda ya karbi numbernta ze samu amsan su..................
************
A rude Alhj mudan ya kira Alhj halliru "hello Alhj akwai matsala, mugu ne ya kira ni" Da karfi Alhj halliru yace "what!!!!! Me yace maka?" Alhj mudan yace "cewa yayi kudin hannunshi sun kare ko mu kara mishi ko asirin kowa ya tonu" Alhj halliru yace "me ke faruwa ne dama mugu na raye? Shekaru ashirin yayi mana aiki kuma mun sallame shi se yanzu ze ce mu bashi kudi? Aka gayamishi mun anfana da aikin ne?"...................