Page 26

1K 106 0
                                    

💞💞💞





                  💞💞Hamrah💞💞




                                                   💞💞

Writer: fateemah Muhammad gurin

Wattpad: muhdfatimagurin

             *'Yar mutan Adamawa*

Page➡️2️⃣6️⃣
***********

"Am.......maah" kai ta gyad'a mishi tana zubda hawaye da mugun gudu ya karasa gabanta tare da sa gwiwowinshi a kasa ya kwantar da kanshi kan cinyarta se kawai ya fashe da kuka sossai, itama kukan takeyi da sauri qudra ta fito da mugun mamaki take kallon namiji kaman haisam na kuka haka kuma akan kafan mamminta? Kodai wani abu ne ya samu hamrah jin shesheka a gefenta yasa ta juya Ai kuwa hamrah lafiyanta bata gama tunani aka shigo parlorn yaqoob ne da sagir suka shigo sagir na dogara sandarshi a hankali...............

Turus suka tsaya suna kallon yadda haisam ke kuka sossai duk jijiyoyin jikinshi sun tashi ya kankame kafan mammi kaman his life depends on it, itama se shafa kanshi take tana hawaye da kyar ta tsayar da kukanta tace "haisam my son" da mamaki 'yan parlorn duk suke kallonta ta kara da "calm down it's okey you got me" kalamai masu sanyi ta ringa fad'amishi cikin harshen turanci har yayi shiru ya kuma d'ago tasa hannu ta share mishi hawayen fuskanshi tana murmushi shima murmushin ya mayar mata.....................

Zuciyarshi fal farin ciki "he got his mom" amma abunda ya bashi mamaki jin yadda take turanci ascent d'inta ma ba na nigeria bane qudra ce ta matso tana cewa "subhanallah kar de an koma gidan jiya" tana nufin haukan mammi ya dawo sbd abun akwai d'aure kai rana tsaka kawai mammi ta kira haisam d'anta it's unbelievable......................

Batayi mamakin turancin mammin ba sbd ko a haukanta In ta fara zuba turanci da larabci ko mutane masu wucewa se sun tsaya kallonsu da mamaki mammi ce ta kalli qudra tare da cewa "ko d'aya habibty Ina cikin hankali da tunani na" qudra tace "amma mammi taya yaya haisam ze zama d'anki?" Kallon mammi yaqoob, sagir da hamrah suka yi don tambayar da ke ransu kenan kuma taya haisam ya ganeta................

Tana murmushi tace "son" ya d'ago tace "oya man up hawayen ya isa kuje kuyi sallah ku dawo I will give you guys my complete story" gyad'a kai sukayi yaqoob yazo ya taimakawa haisam ya mike suka fice jin ana kokarin tada sallah murmushi mammi ta sakar Wa hamrah har zuciyarta tana son daughter-in-law d'inta sbd duk wani abunda ya faru na court tana sane tana kuma cikin hankalinta taga irin gwagwarmayan da hamrah tayi akan d'anta don zama na farko da akayi a wurin ne ta gama gane haisam d'anta ne...................

Hamrah ma murmushi ta sakar mata tare da juyawa don gabatar da la'asar itama se taji mammi tace "daughter-in-law" juyowa hamrah tayi tana cewa "na'am" a rarrabe sbd taji sunan wani banbarakwai mammi tace "ya kamata ki kira su mom d'inki sbd suma su san waye asalin surkinsu" hausan ta wani iri daga ji bata wani kware sossai ba murmushi hamrah tayi tana cewa "tohm" ta juya ta haura seda ta kira su mom ta gayamusu abunda ya faru In brief suka ce zasu zo yanzu tukun ta shige toilet don gabatar da alwala....................

A parlorn kasa kuma baki sake qudra ke kallon mammi bata ankara ba taji mammin ta rike mata hannu tare da janta suka shige room d'insu a bakin gado ta zaunar da ita tare da shigewa bayi don gabatar da alwala seda tayi ta fito tukun qudra ma ta shiga.................

**************
Bayan kowa yayi sallah su mom ma sun hallara kowa yana zaune a parlorn kasa a natse haisam na daga kasa ya mayar da kanshi kan kafan mammin ta ci gaba da shafa kanshi yayinda qudra ke zaune dab da haisam d'in hamrah na kusa da mom da dad dinta rike da hannun dad bayan ta kawo musu d'an abun ta'bawa da ruwa da drinks, sagir da yaqoob suna zaune daga gefe suna kallon mammi magana ta fara kamar haka:-

Hamrah💞💞Where stories live. Discover now