*•••SANADIN MAHAIFINA*•••
_[ILLAR FURUCI]_
'''Story by SaNaz_deeyah'''Visit to like our page on facebook https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsapp
On Youtube https://youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ
_Wannan Gajeran labari ne,da yake jan hankali akan iyaye wanda ke saurin furta mummunan kalami ga ƴaƴansu cikin fushi,wannan labarin jan hankali ga irin wannan iyayen._
*_Garen labari ne akan wasu ƴammata da mahaifinsu ya furta kalami a kansu cikin fushi. Kuma wannan kalami shine yayi sanadiyyar rugujewar rayuwarsu duk da cewar mahaifin yayi kalamin ne ba tare da yasan furucin zaiyi tasiri akan ƴaƴan nashi ba_*
_Salon labarin ya banbanta da sauran hausa novels domin wannan labarin zanyi shi ne akan zallar abinda ke faruwa. So zaku ga abubuwan da bazasu maku daɗi ba sai dai kuyi haƙuri._
'''Duk wacce ta san zata zageni akan wannan labari to karta karanta please'''Littafin gaba ɗayanshi Sadaukarwa ne ga Asmiey Abdul(Husnah) Nagode sosai da gudunmawarki, Allah ya saka miki da dukkanin alkhairinsa.
Tukwuici ne ga DANDALIN TAURARI✨
🎉🎉🎉Happy 1year Anniversary KARAMCI WRITERS ASSOCIATION, Allah ubangiji ya ɗaukaka ƙungiyar nan ya ƙara ma membobin cikinta basira da ɗumbin masoya, ina alfahari da ƙungiyata😍🎊🎊
'''Shafi na 1'''
_*Ƙofar Nassarawa*_
_Maitama Sule University_Su uku suka fito daga cikin hall ɗin, suna bin steps suna sauka ƙasa. Dukkansu ukun fuskokinsu cike da murmushi, a haka suka sauka ƙasa sannan suka tsaya. Safina ce ta fara rufe fuskarta da handout, sannan ta sauke ta kalli ƴammata biyun da suke tare tace "To yanzu mun fito a cigaba daga inda aka tsaya" Farhan tayi dariya tace "Ni fa bazan sake cewa komai ba dan naga ke da Jannat musu baya ƙare maku, sai dai a sakar maku. Jannat sai a lokacin ta sauke ajiyar zuciya tare da faɗin "Ni fa yunwa nakeji, gaskiya mu tafi gida tunda mun gama lectures" "Ai dama aikin kenan ci, acici kawai. Wannan ko bamu gama lecture ba ai dole a samo miki abinci kafin ki sume mana anan" Farhan ta faɗa cikin tsokana.
"Ni dai koma me zaki ce na yarda da ulcer ta kamani gara ace min acici" Duk sukayi dariya.*Asalinsu*
Alhaji Mu'azu wani shahararren mai kuɗi ne wanda a duk faɗin Nigeria ake ji dashi, saboda irin dukiyar daya tara da kuma taimakon mararsa ƙarfi da yakeyi. Cikakken ɗan kasuwa ne, wanda ya jiƙu da naira. Mutum ne da baya da ganin ƙyashi, sannan mutum ne mai tsare gida. Matan shi biyu Hajiya Falmata itace uwargida ƴar asalin garin maiduguri ce, aure ne ya kawota Kano, sun haɗu da Alhaji Ma'azu a wani biki na ƴan uwanta da tazo, to daga nan kuma soyayya ta ƙullu tsakaninsu har ta kaisu ga yin aure, Ƴaƴanta biyu Safina da Jannat. Sai Hajiya Bilki ita kuma ƴar asalin kano ce, kuma auren zumunci sukayi da ita, domin ɗiyar yayan babanshi ce, ƴarta ɗaya Farhan. Ƴaƴan Alhaji Ma'azu uku kuma dukkansu mata. Safina itace babba, sannan Jannat sai Farhan da ta kasance itace auta a cikinsu. Tare suka taso kasancewar tsakanin Jannat da Farhan shekara ɗaya ne, ita kuma Safina itace ta bawa Jannat Shekara biyu Farhan kuma uku.Zaman lafiya ne ke wanzuwa a wannan gida,domin yaran ma ɗakinsu ɗaya sai dai kowa da gadonta. Tun Safina na jss2 Alhaji Ma'azu yayiwa Farhan da Jannat Jumping suka dawo tare. Kuma ko bayan da suka gama secondary school sai duk suka nuna cewar sunfi ƙaunar suyi course ɗaya, dan haka dukkansu tare suke a fannin Accountancy. A yanzu haka suna L200 ne.
*Cigaban Labari*
Tare suka ƙarasa har jikin motar tasu, Safina ce ta shiga driver seat, sai Farhan a gefenta, yayinda Jannat ta koma baya, ta kwanta kan kujera. Hira suke har suka isa gida. Gidansu mantion ne mai masifaffan kyau ya haɗu iya haɗuwa idan kana cikinsa baza kace a kano kake ba. Babu kowa a duka faluka biyu da suka wuce. Ɗakinsu suka nufa kai tsaye. Suna shiga Jannat ta nufi fridge ta buɗe ta ɗauki fresh milk ta kafa a baki. "Uhmmm acici kenan, gaskiya ina tausayin Khalil dan gaba ɗaya sai kin taƙaitashi" Safina ta furta tana cire kayanta. "Shi yaga zai iya ko sis" Farhan ta faɗa tana zama kan gadonta. "Wallahi kuwa faɗa mata dai, kuma shi wannan arziƙi ya masa yawa babu abinda zai ji" Dariya Safina tayi sannan tace "Bari dai na fito daga wanka ki bani labarin wannan Sa'ad ɗin da kika ce ya taimakeki" Ta faɗa lokacin tuni ta ɗora towel ta nufi hanyar bathroom. "Ni yau ma zamu shirya da yamma muje gidan nasu please" "Gaskiya ni dai kin san Assignment ne dani" "Assignment ɗin ba dukkanmu ne ke dashi ba, ni fa bani son wannan iyeyin naki" "Babu wani iyeyi wataƙila ma ni zan maku" "Naji idan bazaki ba, Safina ta rakani" Dariya Farhan tayi tana faɗin "Taɓ Safina ce zata bi ki" "In tayi niyya sai ki hanata ai" Dariya Farhan tayi tana jan ƙatuwar tedy ɗinta.
YOU ARE READING
SANADIN MAHAIFINA (ILLAR FURUCI) DONE✅
Historical FictionGajeran labari ne, da yake nuna ILLAR FURUCI musamman cikin fushi. wannan littafin labari ne akan wasu ƴan mata wanda a ranar ɗaurin aurensu mahaifinsu ya furta mummunan kalami a kansu wanda wannan kalami ya bibiyesu kuma yayi sanadiyar rugujewar ra...