*•••SANADIN MAHAIFINA•••*
_[ILLAR FURUCI]_
'''Story by SaNaz_deeyah'''*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[Karamci tushen mu'amala tagari]_Visit to like my page on facebook https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsapp
On youtube https://youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ
_Sadaukarwa ga Asmiey Abdul(Husnah Soja)_
'''Shafi na 5'''
__________📲 Ɗagowa a kayi ana kallonta cike da mamaki. "Daddy kayiwa Allah kar a ɗaura auren nan, muddin aka ɗaura sai na kashe kaina wallahi, na faɗa maka bana so ka zama mai adalci Daddy" ta faɗa cikin matsanancin kuka. Ƴar hayaniya ce ta fara tashi a gurin yayinda Daddy ya taso a fusace. Alhaji Auwal(Mahaifin Khalil) ya riƙe hannunsa, tare da girgiza kai sannan ya tashi ya ƙarasa inda Jannat take a gurfane. "Tashi mu shiga ciki" "Abba dan Allah kada kuyi abinda zuciyata bata so" "Tashi mu shiga ciki nace, baki ga mutane anan ba." tashi tayi da sauri tana goge hawayen idanunta. Cikin gidan suka shiga, aikuwa Daddy ya riƙota ya fara duka, Alhaji Auwal ya riƙeshi. Matan dake ciki kuwa ƴan biki sai haƙuri suke bayar wa. Kowa yayi cirko-cirko ana tunanin ko mene ya faru ake dukan amarya!
"Ni zaki watsawa ƙasa a ido? Ni zaki ciwa mutumci a cikin dubban jama'a."
Kuka kawai take, ba tare da ta cewa Daddy komai ba. Mommy da ta shigo ranta a ɓace ta zauna a gefe tare da cewa "Jannat ban san haka kike ba, kin ɓata wayonki""Sha'anin yara sai haƙuri, dan Allah kuyi haƙuri, tunda bata so ɗin to ku bata wanda take so, shi kuma Khalil sai ya haƙura ya samu wata"
"Ai bata isa ba, tayi kaɗan, sai dana gama tara dubban mutane sannan ta kawo min iskancin banza.
Kallon mahaifin Khalil tayi da wetted tears ɗin ta tace "Abba kak..kai kaɗai ka fahimceni, tun ba yau ba na faɗawa Daddy bana so, na fasa, amma yace sai ya bani, Abba dan Allah kayi mishi magana"
Dafa kanta yayi sannan yace "To kiyi shiru zamuyi magana tashi ki koma cikin gida, amma karki zauna kiyi ta kukan nan, ba zamuyi abinda baki so ba."
Tashi tayi tana kuka ta fita. Shi kuma Alhaji Auwal ya dawo da nutsawar sa ga Daddy, wanda kana ganinshi kasan yana cikin ɓacin rai. "Na san kana tunanin raina zai ɓaci ne akan wannan abu da Jannat tayi, babu shakka banji daɗi ba ko kaɗan, domin shi kanshi Khalil zai shiga wani hali, amma wallahi ban zargeka ba, haka itama Jannat ɗin, da ita da Khalil ai duk ɗaya ne a gurina, domin da mahaifiyarka da tawa uwa ɗaya uba ɗaya suke kaga kuwa akwai zumunci mai ƙarfi a tsakaninmu. Yanzu dai haƙuri zakayi kuma daurewa zakayi ka tashi muje a ɗaura auren ita Safina da Ahmad, domin mutane na waje suna jira."
"Tabbas Jannat ta watsa min ƙasa a ido, amma zanyi maganinta zan nuna mata cewa ni ba uban banza bane."
"A dai bi komai a hankali, sha'anin yara sai addu'a."
"Alhaji Auwal idan babu damuwa ina neman alfarma a gurinka"
"Ina saurarenka"
"Ina so dan Allah ka yarda in mayar da auren Khalil kan Farhan, inaso nayi auren huci zuciya, sannan kuma in wanke kaina a gurin jama'a, dama shi Khalil ɗin""Amma kana ganin hakan ba zai bamu matsala ba, ita yarinyar zata so hakan?"
"A yanzu babu kowa tare da ita kuma bata kula kowa, ni nasan tana da nutsuwar da ba zata saɓawa umarni na ba, kamar yadda na san cewa Khalil yaro ne mai haƙuri"
"Hakane! Tabbas Khalil ba zai tsallake zaɓin dana bashi ba."
Ta ɓangaren Jannat kuwa tana shiga falo Mommy ta janyota ta fara duka, da ƙyar Aunty Mammy da Ummu suka ɓanɓareta. Faɗa da hayaniya ya kacame a gidan wasu na yiwa Mommy, yayinda wasu ke yiwa Jannat.
Su Safina kuwa suna can ɗakinsu da ƙawaye bama su san wainar da ake toyawa ba.
DU LIEST GERADE
SANADIN MAHAIFINA (ILLAR FURUCI) DONE✅
Historische RomaneGajeran labari ne, da yake nuna ILLAR FURUCI musamman cikin fushi. wannan littafin labari ne akan wasu ƴan mata wanda a ranar ɗaurin aurensu mahaifinsu ya furta mummunan kalami a kansu wanda wannan kalami ya bibiyesu kuma yayi sanadiyar rugujewar ra...