*•••SANADIN MAHAIFINA•••*
_[ILLAR FURUCI]_
'''Wattpad@ SaNaz_deeyah'''*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[Karamci tushen mu'amala tagari]_
Email-Karamciwritersass@gmail.comVisit to like my page on facebook https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsapp
On youtube https://youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ
On Wattpad https://my.w.tt/NuwIi6ubScb
_Sadaukarwa ga Asmiey Abdul(Husnah Soja)_
*Not Edited*⚠️
'''Shafi na 19'''
Da sauri ya bi bayan Jannat lokacin har ta fita. Tarar da ita yayi ta lafe da bango, hannunta na kan saitin zuciyarta, idanunta a lumshe. "Jannat kiyi haƙuri dan Allah" buɗe idanunta tayi ta diresu akan na shi. "Baka min laifin komai ba, nagode da kulawarka, amma ina so ka koma gurin matarka domin tana buƙatarka a wannan lokacin, na san a yanzu tana cikin ƙunci, kaje ka rarrasheta" "Bari in ɗauko mota in mayarki gida" "A'a ka bari zan samu Napep ya kaini, yanzu ma zuciyata naji tana zafi shiyasa na tsaya na ɗan huta" "Jannat ki bari na kai ko gida" "A'a" ta faɗa cikin rawar murya. "Jannat kin san Daddy da ƙyar ya bari kika zo, kuma nina ɗauko ki, ni ya kamata na mayarki, idan har wani abu ya sameki ai laifina ne, dan Allah ki yi min alfarmar in ɗauko mota in maida ki gida" kai ta gyaɗa. "Dan Allah karki tafi ki jira ni" Kai ta sake gyaɗawa" da sauri ya juya ya komabita kuma ta sauke ajiyar zuciya.
Yana fito da motar ya parker a gabanta, sannan ya fito ya buɗe mata ƙofa, bata musa ba ta shiga ya rufe, sannan ya zagaya ya shiga. Yana driving a hankali yayinda ita kuma ta kwantar da kanta a jikin kujera. Ɗan kallonta yayi kafin ya mayar da kanshi ga titi.
"Yaya Khalil na yanke shawara kawai" ta furta a hankali sannan ta ɗago kai ta kalleshi. "Wace shawara kika yanke?" "Na san ba lallai tayi maka daɗi ba amma ita ce mafita a gareni" "Inajinki" "Zan aure Ahma......" bata ƙarasa ba ya ci wani burki, saura kaɗan ya karawa motar gabanshi, a hankali ya koma gefen titi ya faka motar.
Har lokacin hannunta na ƙirji ta runtse ido, dan a tunaninta ma accident za suyi. "Gara ki kashe ni kawai ki huta, da in ga wannan baƙar ranar" sai a lokacin ta buɗe idanunta, titi ta fara kalla sannan ta kalleshi. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, idanunsa gaba ɗaya sun canza launi.
"Yaya Khalil abu biyu ne zai sakani auren Ahmad, na farko, saboda in rama cin mutumcin da yayi min in muzgana masa har yaji ya tsani duniya, na biyu kuma saboda in kawar da zargin da Farhan take min game da kai" "Sai me tayi ta faɗa, ta dsɗe bata faɗa ba" yayi maganar cikin shouting. Kallon shi kawai take cike da mamaki.
Dafe goshi yayi sai kuma ya cire hannun ya kalleta. "Wan can ɗan iskan da na san baki son shi kika saboda tausayine ya saka kika fasa aurena da bazan yarda hakan ta faru ba, sanyin halinki shi yake cutarki Jannat" shiru ya ɗanyi, sai lokacin ta sauke ƙwayar idanunta ƙasa. "Kin san kuwa har yanzu ina sonki, anan ɗina nake jinki" ya nuna saitin zuciyar shi.
Zaro idanu tayi tana kallonshi, gabanta ban da faɗuwa ba abinda yake. "Jannat ina sonki kema kin san ba zan taɓa iya daina sonki ba, sai dai kawai son da nake miki ba zai taɓa bani damar aurenki ba, shiyasa na ɗauki alƙawarin kare miki mutumcinki, kuma ni da kaina zan zaɓa miki mijin daya dace dake wannan shine alƙawarin dana ɗaukarwa kaina, muddin kika ce za ki auri Ahmad ba zan taɓa yafe miki ba"
Kwantar da kai tayi ta fara kuka a fili, ya ƙara da faɗin "Dan Allah karki aure shi, baku dace ba, please Jannat ki min wannan alfarmar" Hannu ta saka ta goge hawaye sannan ta ce "Na baka damar zaɓa min mijin daya dace dani, amma dan Allah ka nusar da Farhan cewa ba yanda za ai mijin ƙanwa ya auri Yaya, ita kanta ta san a yanzu aurenka ya haramta a gareni, kuma kaima ina so kayi min alfarma" "Inajinki" ya faɗa da raunanniyar murya. "Ina so ka daina cewa kana so na har yanzu saboda gudun zargi, idan kuwa baka daina ba, to zan nisanta idanuna daga gareka"
Driving kawai ya cigaba dayi ba tare da ya bata amsa ba. Suna cikin tafiya, tayi tari ɗan kaɗan, ta tare da hannunta yayin da tayi tarin, kawai sai gani tayi gudan jini ya faɗo baƙi. Gabanta ya faɗi, ta kalli Khalil ta ga tuƙi yake dan haka kawai ta yi saurin buɗe jakarta ta ɗauki hanky ta goge sannan ta euga hanky ɗin waje.
Ganin suna ɗaukar wata hanya ya saka ta ce "Na ga mun kauce hanyar gida?" "Za muje asibiti" "Asibiti kuma, waye ba lafiya?" "Ke mana, ko kina tunanin ban ga abinda ya faru ba?" bata ce komai ba har suka isa asibiti.
2 hours later
Bayan result ya fito sun kaiwa likita ya duba, ya ce ta fita yana son magana da Khalil. Kallon Khalil tayi, cikin tattausan kalami ya ce "Cool your mind, ba komai bane ki zauna yanzu zan fito" jikinta a sanyaye ta tashi ta fita.
A kujerum gurin ta zauna, ta danna number Mommy ta kara a kunne. "Yanzu nake shirin kiranki, ina kuka tsaya haka?" "Naje ganin Farhan ne amma muna hanya yanzu zamu dawo" "Lafiya naji muryarki ta canza, ko har yanzu baki daina kukan ba" murmushin yaƙe tayi "A'a Mommy kawai dai voice ɗin ne ya shaƙe" "To ki kula da kanki sosai, Allah ya dawo daku lafiya" "Amin Mommy."
"Ban fahimta ba Doctor" ya faɗa yana kallon shi. "Eh ina nufin ta samu tsaga a zuciyarta, to kuma jini ya taru a gurin, dole sai anyi aiki a fitar da jinin" "Tsagar fa?" "Ita wannan gaskiya sai dai magunguna" "Doctor kana nufin shikenan za mu rasa ta?" "A'a ai cuta ba mutuwa bace, za ta samu sauƙi a hankali da yardar Allah."
Yana fitowa tayi saurin miƙewa tsaye, ƙarasawa gabanshi tayi yadda taga ya fito a sanyaye sai hankalinta ya ƙara tashi. "Doctor ya ce mutuwa zanyi ko?" ta faɗa a sanyaye "A'a" "To amma ya ka fito a haka na san akwai abinda ya faɗa maka" "Zo muje" ya faɗa tare da yin ga, ita kuma ta bishi" a gurin cashier ya biya kuɗi sannan aka bashi recept wani nurse ya biyosu ya nuna masu wani ɗaki.
Suna shiga komai a gyare gadon ma an shimfiɗa bedsheet fari sol "Jannat ki zauna ko ki kwanta idan kin gaji" "Ban gane ba, yanzu fa nayi waya da Mommy na ce mata muna hanya" har zai yi magana sai ga nurses biyu da Doctor sun shigo.
"Sannu ko" Doctor ya faɗa, bata bashi amsa ba, kawai da kallon mamaki take binsu. "Madam ki kwanta zamu saka miki drip" kallon Khalil tayi, ya ɗan kauda kai, dan haka kawai ta kwanta suka jona mata. Tashi yayi da sauri ya fita dan ya samu ya kira su Mommy. Yana sanar musu kuwa suka ce gasu nan zuwa. Dan haka ya koma ɗakin.
Tararwa yayi har ta yi bacci, cike da tausayawa yake kallonta, lokaci guda wani banza can ya ruguza rayuwarta, har cikin ransa yake jin zafin abin.
******
Hannd tana daga jikin ban go tayi tagumi, yayinda shi kuma yake tsaye ya fuskanci Umma. Zulaiha kuwa gaba ɗaya ta shiga duhu.
"Yaushe har Safina ta rasu da bamu sani ba?" Umma ta faɗa tana kallom Sa'ad. "Umma ni kaina wallahi ban sani ba, sai yanzu da ta faɗa, sai inga kamar ban mata adalci ba"
"Babu wani rashin adalci, idan ka bibiya ma wallahi ƙarya suke, sun yi haka ne dan su ɗaga maka hankali" Kallon Umma Hanne tayi sannan ta ce "Haba Umma taya za tayi ƙaryar mutuwa da yayarta, yadda Jannat tayi maganar ma sam babu alamun ƙarya a ciki"
"To ko mutuwa Safina tayi mu mene namu a ciki?" kallonta kawai Hanne tayi, tama rasa me za ta ce saboda ɓacin rai dan haka kawai ta tashi ta shige ɗaki.
*****
Yana shiga falon kai tsaye ya nufi upstairs tana yi masa sannu da zuwa amma sam bai kulata ba. Bin bayan shi tayi, tana shiga ɗakin taga yana cire kaya.
"Saboda Jannat shine kake wani haɗe min rai?" bai ce mata komai ba ya wuce bathroom, har yayi wanka ya fito tana nan zaune gefen gadon.
"Ka shirya muci abinci" sai a lokacin ya kalleta ya ce "Na ƙoshi, kuma Jannat tana asibiti, nan da kwana uku za a mata aiki, dan haka ki shirya yanzu mu wuce"
"Oh wai dama shirin da kake can ka nufa kenan?" "Daga can nake kuma can zan koma" "To ni bazan je ba" kallon ta yayi ya ce "Farhan wai mene a kanki? Ko dai kinyi hauka ne?" "Ras nake" "Okay" ya faɗa bai ƙara mata magana ba har ya gama shiryawa, ya juya zai wuce ta ce "Allah yasa ta mutu kowa ma ya huta" a sama yaji maganar dan haka ya juyo ya kalleta. "Me kika ce?" murguɗa baki tayi sannan ta ce "Nace matar da bata ƙaunarka amma ka wani liƙe mata kamar mara zuciya" "Eh bani da ita" "To Allah yasa ma ta mutu kowa ya huta" "Da gaske dai bakinki ne ya faɗa ko?" "Eh ɗin na faɗ.........." bata ƙarasa ba ya wanke ta mari....
#Follow
#Vote
#Comment
#Share
DU LIEST GERADE
SANADIN MAHAIFINA (ILLAR FURUCI) DONE✅
Historische RomaneGajeran labari ne, da yake nuna ILLAR FURUCI musamman cikin fushi. wannan littafin labari ne akan wasu ƴan mata wanda a ranar ɗaurin aurensu mahaifinsu ya furta mummunan kalami a kansu wanda wannan kalami ya bibiyesu kuma yayi sanadiyar rugujewar ra...