*•••SANADIN MAHAIFINA•••*
_[ILLAR FURUCI]_
'''Story by SaNaz_deeyah'''*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[Karamci tushen mu'amala tagari]_Visit to like my page on facebook https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsapp
On youtube https://youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ
On Wattapad https://my.w.tt/NuwIi6ubScb
_Sadaukarwa ga Asmiey Abdul(Husnah Soja)_
'''Shafi na 6'''
__________📲Tana shiga bedroom ta ɗauki wayarta tayi dialling number Jannat ta ji ta a kashe. Hankalinta sosai ya tashi sai dai kawai daurewa take dan kar tayi kuka gaban mutanen da suke ta ƙara bata haƙuri.
Ta ɓangaren Jannat kuwa, tafi mintuna talatin tana kuka a gurin, kafin taji magana daga bayan ta. Da sauri ta ɗago rinannun idanunta ta kalli wanda ke mata maganar. Alhaji sani ne, maƙotansu, gidanshi na jikin nasu. "Me kike yi anan haka?" "Daddy ne ya koreni" ta faɗa tare da fashewa da sabon kuka.
"Kora kuma? Tun ɗazu fa na bashi haƙuri ban san meyasa yayi haka ba, yana cikin gidan?" gyaɗa kai tayi alamar eh. "Bari nayi mishi magana.Maigadi ya saka yaje yayi kira shi, yana fitowa kuwa sukayi ido huɗu da Jannat. "Wato baki bar ƙofar gidana ba."
"Idan ta bari ina zataje? Wa take dashi wanda ya fika?"
"Ita kuwa ke dashi, tunda a filin taron ɗaurin aurenta ta nuna hakan"
"Alhaji Mas'ud kayi haƙuri don Allah, sha'anin yara sai haƙuri da kuma addu'a"
"Wannan dai ba zan yi haƙuri da ita ba, bata da hali, dan haka dole ta bar gidana ta tafi duk inda taga ya fi mata ta zauna"
"Tun ɗazu muke baka haƙuri, kamata yayi ka tausheta kaji dalilinta kafin ka yake mata hukuncin kora, kora ba ƙaramin illa bane ga ƴaƴa, domin baka san wane hali zata faɗa ba"
"Ina ruwana to? Ko ma wane irin hali ne ni ban damu ba"
"Amma...." "Ka ga malam, wannan fa ƴata ce ba ta wani ba, to dan haka ku ƙyaleni kawai."
Yana gama faɗa ya juya ya shige gidan.
Alhaji sani girgiza kai yayi yace "Jannat zo mu shiga gidana ki kwana a can kafin zuwa gobe ya huce"
"Nagode" ta faɗa tana goge hawayen da suka kwanta a fuskarta.Juyawa yayi ya shiga motarsa yayi horn maigadi ya buɗe masa gate. Yana shiga da motar itama ta shiga. Tsayawa tayi har sai da yayi parking ya fito, sannan yace su shiga. Tabi bayanshi. Da sallama ya shiga falon, itama cikin sallama ta shiga duk da muryarta bata fita sosai.
Ƴaƴanshi biyu mace da namiji. Macen ana kiranta da Khairat namijin kuma Rayyan. Rayyan ne babba, shekararshi 27, Khairat kuma 20. Dukkansu suna kan kujera suna kallon tashar Zeeworld.
"Zauna Jannat ga guri" ya nuna mata kujera yayinda ta zauna a ƙasa.
"Ki zauna a kujera mana"
"Nan ma ya isa" ta faɗa cikin sanyi murya.
"Daddy sannu da dawowa"
"Daddy barka da dawowa" Ƴaƴan suka faɗa yayinda Haj Bilkisu ta zuba masa ido tana jiran yayi mata bayani.Zama yayi tare da sauke ajiyar zuciya. "Alhaji wannan fa?"
"Kina nufin baki gane ta ba?"
"Gaskiya dai"
Kallon Khairat yayi yace "Kefa kin gane ta?"
"Eh to kamar neighbor ɗinmu"
"Au kama ne ma?"
"Daddy ka san da yake ba wata mu'amula muke da su ba"
"Ko kunyar faɗa bakyayi, ni dai ina mutumci da mahaifinta"
"To ƴammatan gidan ne akwai girman kai"
"kada in ƙara jin kin faɗi haka" ya furta cikin rashin jindaɗin furucin.
Haj Bilkisu kuwa cewa tayi "To ai gaskiya ta faɗa, shiyasa ko da suka kawo I.V ban leƙa bikin ba"
"Mommy wannan itace wadda nake faɗa miki taje wajen taron ɗaurin aure tana faɗin a fasa" Rayyan ya faɗa yana kallon Mommyn tasa"Jannat kanta na ƙasa tana ƙara zubar da hawaye. "Bana son shashanci banza, ya zaku zauna kuna cin mutumci yarinya a gaban idanunta, bana son haka"
"To kayi haƙuri yallaɓai, yanzu dai meya faru na ganka da ita?"
YOU ARE READING
SANADIN MAHAIFINA (ILLAR FURUCI) DONE✅
Historical FictionGajeran labari ne, da yake nuna ILLAR FURUCI musamman cikin fushi. wannan littafin labari ne akan wasu ƴan mata wanda a ranar ɗaurin aurensu mahaifinsu ya furta mummunan kalami a kansu wanda wannan kalami ya bibiyesu kuma yayi sanadiyar rugujewar ra...