*•••SANADIN MAHAIFINA•••*
_[ILLAR FURUCI]_
'''Wattpad@ SaNaz_deeyah'''*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[Karamci tushen mu'amala tagari]_
Email-Karamciwritersass@gmail.comVisit to like my page on facebook https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsapp
On youtube https://youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ
On Wattpad https://my.w.tt/NuwIi6ubScb
_Sadaukarwa ga Asmiey Abdul(Husnah Soja)_
*_Ina neman afuwar Readers nayi mistake a shafi na 9, na saka Saturday, kowa ya san saturday weekend ne, so ku ɗauke shi a matsayin monday ne._*
_Ina godiya ga ɗaukacin makaranta wannan littafi, nagode sosai_
*Not Edited*⚠️
'''Shafi na 10'''________________📲 *04:30pm*
A hankali ta buɗe idonta da suka mata nauyi sosai, har lokacin kasala take ji da bacci, lumshe idon tayi, ta fi mintuna biyu kafin ta buɗe ido, miƙewa tayi zaune, sai jin wani mugun zugi tayi daga private part na ta. kallon jikinta tayi. _Yaushe har na cire bra nawa na kuma zage zip ɗin rigana?._ shine tambayar da ta fara yi wa kanta kafin ta bi jinkinta da kallo.
Sai lokacin ta ga jini kwance, ya bi ƙafarta, zabura tayi tare da zunduma ihu. Abu biyu ga zafin da taji na yunƙurin tashi da kuma kaɗuwa da yanayin da ta tsinci kanta.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,mene ya faru dani" ta faɗa tare da rufe bakin ta da hannu tana kuka.
Cikin barf ta shiga tana gasa jikinta da gaba ɗaya ya ke ciwo. Kuka kawai take duk da cewar har lokacin bata tabbatar da abinda ya faru da ita ba.
Ta fi mintuna talatin a toilet kafin ta fito tana ɗangyasa ƙafarta.
Jikin mirror ta tsaya tana kallon fuskarta da ta ɗan kumbura. _Ya Allah ka raba ni da jin kunya duniya da lahira._ ta faɗa tana ƙara goge hawaye. Bedsheet ɗin ta yaye ta kai toilet ta ajje sannan ta shimfiɗa wani.
Bayan ta shirya kuwa gado ta kwanta ta rufe jikinta saboda zazzaɓin da ta ji yana neman rufeta. _Allah ka sa ba aljani bane ya aureni._ ta sake furtawa tana zubda hawaye mai zafi.
Taso faɗawa Safina abinda ya faru amma sai ta fasa saboda gudun kar ta jefata a damuwa, dan ko da ta tambayeta da taga yanayin tafoyarta kawai sai ce wa tayi a toilet ta faɗi.
*4 days later*
Tana zaune tana yanke farcen ƙafarta, Safina na kitchen tana haɗa abincin lunch, saboda friday ne Ahmad baya dawowa gida sai an fito daga masallaci.
Knocking da akayi ne ya saka Jannat tashi ta zura hijab sannan ta nufi ƙofar da buɗe. Wani mayen kallo ya bita dashi, ta juya kawai ta wuce ciki.
Tana zaune kan gado ta tanƙwashe ƙafafunta ta lula duniyar tunani. Safina ta turo ƙofar ta shigo cikin sallama. Kallonta tayi ta amsa mata sannan ta kawar da kanta gefe.
"Ki taso muyi lunch."
"Na ƙoshi" ta bata amsa a taƙaice.Zama tayi a gefen gadon ta kalleta sannan ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Na kasa gane kanki Jannat, meke faruwa ne?"
Hawaye ne suka zubo daga idanunta ta kalli Safina tace "Har tsawon wane lokaci zan yi kafin Daddy ya ya fe min? Safina ta ya zaki gane kaina bayan har yanzu ina cikin fushin mahaifi, ba zan taɓa samun sukuni ba matuƙar Daddy bai yafemin ba"
"Kada ki damu insha Allahu Daddy zai yafe miki"
"Sai yaushe? Gaskiya akwai takura zamana a wannan gida"
ESTÁS LEYENDO
SANADIN MAHAIFINA (ILLAR FURUCI) DONE✅
Ficción históricaGajeran labari ne, da yake nuna ILLAR FURUCI musamman cikin fushi. wannan littafin labari ne akan wasu ƴan mata wanda a ranar ɗaurin aurensu mahaifinsu ya furta mummunan kalami a kansu wanda wannan kalami ya bibiyesu kuma yayi sanadiyar rugujewar ra...