Shafi na 13

120 12 0
                                    

*•••SANADIN MAHAIFINA•••*
           _[ILLAR FURUCI]_
'''Wattpad@ SaNaz_deeyah'''

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
  _[Karamci tushen mu'amala tagari]_
     Email-Karamciwritersass@gmail.com

Visit to like my page on facebook https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsapp

On youtube https://youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ

On Wattpad https://my.w.tt/NuwIi6ubScb

_Sadaukarwa ga Asmiey Abdul(Husnah Soja)_

                    '''Shafi na 13'''

*30 Minutes Later*

A hankali Mommy ta buɗe idanunta, akan Aunty Mammy ta fara diresu, a hankali abubuwa suka dawo mata, ta miƙe cikin tashin hankali tana ƙoƙarin dirowa daga gado. Aunty Mammy ta riƙeta sannan ta saka hannu ta goge hawaye tare da faɗin "Kiyi haƙuri" cikin tashin hankali Mommy ta kalleta hawaye kwance a idanunta. "Dagaske Safina ta rasu?" "Haƙuri zakiyi dukkanmu ita muke jira" "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Safina bata rayuwa?" kuka ya kubce mata, Aunty Mammy ta kasa hanata domin itama kukan take ta kasa tsayar da hawayenta. Likita da nurses biyu da suka shigo rarrashinsu suka farayi, kafin nan suka sallameta.

             *******

Cikin matsanancin kuka ta ƙara yunƙurin tashi, Aunty Farida ta sake riƙeta tana kuka itama. "Sis kiyi haƙuri baki da lafiya, dole ta sa aka baki sallama, dan Allah ki zauna"  cikin matsanancin kuka ta ce "Safina bata rayuwa? Dan Allah karki hanani zuwa ganin gawar ƴar uwata." "Za ki ganta idan an gama shiryata." Kuka ta cigaba dayi suka rungume juna suna kuka.

Daga waje kuwa, Khalil yayi parking motarsa ya fito. Gaba ɗaya shima idanunsa sun canza launi saboda damuwa. Gurin da Daddy yake tsaye yana karɓar gaisuwa nan ya tsaya. "Ka sanar masu?" "Daddy baya nan, sai maigadi kawai, shima kuma ya ce min lallai akwai abinda ya faru, domin  a wancan satin ya ɗauke su duka ya saka su a mota kuma ko wacce kamar gawa. Da ya dawo kuma kwana biyu bai ga matar gidan da ƙanwarta ba, sai Ahmad ɗin da yake ta zirga-zirga kuma  yana cikin damuwa, to wai a kwana biyu ya haɗa kaya ya fito ya sanar masa cewa zai yi tafiya ta tsawon shekara, kuma ya bashi kuɗi masu yawa yace in yaga dama ya tafi ko kuma ya zauna har ya dawo" Shiru Daddy yayi na tsawon lokaci kafin ya kalli Khalil. "Bani da ɗa namiji da zamuyi shawara da shi, Khalil kai ne dai nake ganinka a matsayin ɗan nawa, dan haka idan an kai ta kushewa an dawo zamu tattauna matsalar" "To Daddy."

Farhan kuwa kuka take a fili kamar ranta zai fita, mutane da dama sun bata haƙuri amma taƙi haƙura, Ummu ma ta yi iya yinta amma taƙi saurarenta. Gidan a cike yake maƙil lokacin da su Mommy da Aunty Mammy suka dawo daga asibiti, idanun Mommy sunyi jajir sun kunbura. "Ku shigar da ita ɗaki ta ɗan huta" shine abinda mutane da dama ke faɗa.

*20 minutes later*

Tana kwance a kan gado tana jan casbaha wata mata ta shigo ɗakin. "Hajiya ki fito kuyi sallama an gama shiryata" miƙewa tayi, Hajara yayar Hajiya Bilki ta riƙeta tare da faɗin "Dan Allah ki saka nutsuwa kinji, ki yiwa ƴarki addua sosai, Allah daya fi ki son ta shine ya karɓa" Kai kawai ta gyaɗa sannan ta fita.

Suna durƙushe gaban gawar Safina, suna ta addu'a. Mommy har lokacin dai bata cigaba da kuka ba ta daure sosai, Ummu da Farhan ne ke ɗan goge hawaye. Daddy da Khalil da Alhaji Sani suna tsaye a gefe.  Farhan ce idan kukanta zai fito fili sai yayi saurin kwaɓarta cikin nasiha. Kukan Jannat shine sallamarta na shiga ɗakin da gawar Safina take. Tare suke da Aunty Farida amma a lokacin ta fuzge hannunta daga na Aunty Farida.

"Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un na shiga uku, na shiga uku meyasa ban mutu ba sai ke Safina?"  da sauri ta ƙarasa gurin cikin kuka, Farhan kuwa kamar jira take aikuwa itama ta fashe da kukanta a fili. Mommy da Ummu ma haka, gidan dai gaba ɗaya ya ƙara birkicewa.

SANADIN MAHAIFINA (ILLAR FURUCI) DONE✅Donde viven las historias. Descúbrelo ahora