*•••SANADIN MAHAIFINA•••*
_[ILLAR FURUCI]_
'''Wattpad@ SaNaz_deeyah'''*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[Karamci tushen mu'amala tagari]_
Email- Karamciwritersass@gmail.comVisit to like my page on facebook https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsapp
On youtube https://youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ
On Wattpad https://my.w.tt/NuwIi6ubScb
_Sadaukarwa ga Asmiey Abdul(Husnah Soja)_
'''Shafi na 27'''
Gabanta taji yayi mummunan faɗuwa, ta dafe ƙirji tare da karanto "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Khalil ya kalleta ya ce "Calm down insha Allah komai zai tafi lafiya." Ajiyar zuciya ta sauke ta ce "Kawai ji nayi gabana ya faɗi sosai, ni fa hankalina a tashe yake Yaya Khalil" "Ki zauna ki samu nutsuwa" ya faɗa yana nuna mata nuni da kujera.
Tana zama aka fito da Farhan daga ɗaki, tana kwance ana turata, da sauri Jannat da Khalil suka ƙarasa gurin. Hawaye na bin gefen idanunta tana kallonsu kawai ta lumshe idanunta. Bin su suka yi har sai da aka shiga da ita theater room sannan suka tsaya, zama Jannat tayi ta rufe fuskarta da hannayenta.
*1 hour Later*
Nurse ne ya fito da Babyn a hannu, tun kafin ya ƙaraso suka yi saurin tashi, Jannat ce ta karɓa a hannu tana murmushi. "An samu Baby girl" "Wow Allah ya raya" kallon nurse ɗin tayi yana ƙoƙarin juyawa ta ce "Maman Babyn fa?" kafin ma yayi magana an fito da ita kamar yadda aka shiga da ita akan gadon dai, sai dai kuma yanzu tana kwance idanunta a rufe kamar gawa.
Kallon shi tayi yayi murmushi ya ce "Allurar ce bata saketa ba, yanzu za a kaita ɗakin hutu sannan a jona mata jini" "Amma bamu sayo jini ba" Khalil ya faɗa yana kallon nurse ɗin, lokacin Doctor ya ƙaraso ya ce "Ai ta ba da nata, kasancewar group ɗin jininsu ɗaya" Kallonta Khalil yayi ya ce "Jannat ke kika bayar da naki?" murmushi tayi ta ce "Eh, tunda jinina zai mata to ai ba sai an saka mata na wanda bamu sani ba" "Lallai ke ta da ban ce Jannat" murmushi kawai tayi.
*30 minutes later*
Farhan na daga kwance Babyn tana hannun Jannat, Farhan ta kalleta a sanyaye ta ce "Jannat an bata zam-zam da dabino?" "A'a ke muke jira ki tashi sai ki bata" girgiza kai tayi sannan ta ce "Ke nake so ki bata, ina so tayo haƙuri irin naki" murmushi kawai Jannat tayi "Ki bata please" Khalil ne ya janyo trolley ya buɗe, ta ɗauki tabino tayi addu'a ta tauna sannan tayi addu'a ta sakawa babyn a baki, ta ɗisa mata ruwan zam-zam, sannan ta miƙawa Farhan. Rungumeta tayi tana murmushi ta ce "Wai ni ce da Baby" Murmushi Jannat tayi ta ce "Au wai ne ma?" "Eh mana, ni gani nake kamar mafarki" "To ba mafarki bane zahiri ne" Kallon Khalil tayi ta ce "Yaya Khalil, dan Allah ka yafe ni akan abinda nayi maka, Jannat kema kiyi haƙuri dan Allah" "Wannan magana ba anan ya kamata ayi ta ba, ni na daɗe da yafe miki, Allah ya ba ki lafiya" "Amin ya rabbi."
Waya Jannat ta sake ɗagawa ta kira su Daddy amma dukkansu wayarsu switched off. "Har yanzu number tasu bata shiga?" Farhan tayi tambayar "Wallahi fa, Allah dai yasa lafiya" cewar Jannat. "Amin." Khalil juyawa yayi ya fita dama bai ce komai ba.
Sake kiran Abbansa yayi ya ce "Abba ya ake ciki yanzu?" "Khalil gamu har mun dawo gidan ma, yaushe za'ayi sallama?" "Ai ba yau ba, saboda C.S aka mata" "To kar a faɗawa Farhan ɗin saboda tana cikin matsala, ita Jannat ɗin kayi mata dubara ku dawo gida"
"Amma Daddy Jannat ma tana da ciwon zuciya, kana ganin ba matsala?" "Khalil rashin faɗawa Jannat zai iya jawo komai, gara ta ganta kafin a kaita, kasan dubarar da zakayi ka kawota ba tare da Farhan ta gane ba, yanzu bara na shiga gidan na sa a turo wata ta zauna da Farhan ɗin" "To shikenan" "Dan Allah kayi sauri ka kawota, ita ake jira har an gama shirya gawa, ka ga yamma tayi" "To gamu nan."
KAMU SEDANG MEMBACA
SANADIN MAHAIFINA (ILLAR FURUCI) DONE✅
Fiksi SejarahGajeran labari ne, da yake nuna ILLAR FURUCI musamman cikin fushi. wannan littafin labari ne akan wasu ƴan mata wanda a ranar ɗaurin aurensu mahaifinsu ya furta mummunan kalami a kansu wanda wannan kalami ya bibiyesu kuma yayi sanadiyar rugujewar ra...