Page 24

91 9 0
                                    

*•••SANADIN MAHAIFINA•••*
           _[ILLAR FURUCI]_
'''Wattpad@ SaNaz_deeyah'''

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
  _[Karamci tushen mu'amala tagari]_
     Email- Karamciwritersass@gmail.com

Visit to like my page on facebook https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsapp

On youtube https://youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ

On Wattpad https://my.w.tt/NuwIi6ubScb

_Sadaukarwa ga Asmiey Abdul(Husnah Soja)_

                    '''Shafi na 24'''

Ta gaban Jannat tazo zata wuce, Jannat ta riƙo hannunta tare da dawo da ita baya. Hannu ta saka ta yaye niƙab ɗin fuskar Hanne. "Kina tunanin niƙab zai saka in kasa gane ki? Sanin da nayi miki Hanne, zan iya gane ki a ko wane irin yanayi." har lokacin idanun Hanne a rufe suke, sai hawaye da suke kwarara daga cikinsu.

Cikin tashin hankali Jannat ta ce "Wa kika kawo? Waye babu lafiya?" kukanta ya fara ƙoƙarin fitowa fili, tayi ƙoƙarin janye hannunta daga cikin na Jannat amma ta kasa.

Jajayen idanunta ta buɗe ta kalli Jannat "Ana jirana, lokaci na ƙuremin dan Allah ki sakeni in tafi" "Duk inda za kije muje tare, ina son sanin abinda ke faruwa, hankalina ya tashi dan Allah ki sanar dani kinji."

Rungume Jannat tayi tare da ƙara fashewa da kuka. Ɗaya daga cikin securities ɗin gurin yazo kusa dasu "Hajiya please, ko zaku ɗan fita saboda majinyata ne anan masu hawan jini, kinga kukanta zai iya ɗaga masu hankali."

Jannat bata samu damar basu amsa ba kawai taja hannun Hanne suka fita. Mota ta buɗe mata ta shiga ta zauna sannan itama ta koma driver seat ta zauna. Kallon Hanne take wadda ta cusa kai cikin gwiwa tana ta kuka, hakan yasa Jannat ta tabbatar da cewa wani ne ya rasu, ko Umma ko Sa'ad. "Innalillahi wa inna ilaihi riji'un" ta furta cike da damuwa, har lokacin Hanne bata ɗago ba. Jannat ta ƙyaleta kawai domin ta tabbatar kuka na wanke damuwa dan itama tayi experiencing haka.

Sai da Hanne tayi kuka na kusan mintuna goma sannan ta ɗago tana goge hawaye, idanunta sun ƙara ƙanƙancewa sun zama jajir, fuskarta duk ta kumbura, tayi jajir musamman kan hancinta, kasancewarta fara ce sol. Ajiyar zuciya Jannat ta sauke ta dafa hannayenta kan sitiyari tare da ɗora kanta.

"Jannat zan tafi lokaci na ƙure min" cikin damuwa Jannat ta kalleta "Nayi tunanin kece zakka a gidanku, Hanne nayi mamaki da za kiyi kuka irin haka, kuma kina  neman tafiya ba tare da kin sanar dani komai ba, ga wayarki sai ringing take kinƙi ɗagawa, dan Allah ki sanar dani" Dogon numfashi Hanne taja tare da cewa "Faɗa miki damuwata bashi da wani amfani Jannat" "Kenan babu wani taimako da zan iya bayarwa?" shiru Hanne tayi a lokacin saƙo ya shigo wayarta.

Gabanta na faɗuwa ta ɗago wayar 12missed calls na Doctor Isma'il sai message daya shigo yanzu. _Babe ke nake jira, naga har kin ƙara mintuna 8 a cikin mintunan dana baki, fatan dai kina hanya? Na kira baki ɗaga ba, ko dai kin canza ra'ayine, idan kin canza nima bazan fasa watsa videonki ba, kuma dangin mahaifinki zan fara kaiwa su gani, shawara ya rage naki._ da sauri ta buɗe murfin motar za ta fita sai kuma ta koma.

"Inaso ki yafewa Umma da Yaya Sa'ad laifukan da suka miki, ta yuwu wannan ne haɗuwarmu dake na ƙarshe, gaba ɗayansu sunyi nadamar abinda suka aikata miki" "Ba zan yafe ba" Jannat ta faɗa idanunta na kallon hanya. Hannaye Hanne ta haɗe, wanda su kansu karkarwar suke. "Dan Allah Jannat na roƙeki daki yafe musu dan girman Allah" juyowa Jannat tayi ta kalleta, za tayi magana kira ya ƙara shigowa Hanne, da sauri ta saka wayar a silent sannan ta dawo da kallonta ga Jannat.

"Zan yafe musu amma sai kin sanar min da abinda ke faruwa, in ba haka ba, bazan taɓa yafe masu ba" "Tsoro nake Jannat" ta faɗa tare da fashewa da wani kukan. Kiran daya ƙara shigowa  ne ya ƙara saka Hanne a tashin hankali, da sauri Jannat ta fuzge wayar ta ɗaga tare da karawa a kunne ba tare da tayi magana ba.

SANADIN MAHAIFINA (ILLAR FURUCI) DONE✅Donde viven las historias. Descúbrelo ahora