*•••SANADIN MAHAIFINA•••*
_[ILLAR FURUCI]_
'''Wattpad@ SaNaz_deeyah'''*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[Karamci tushen mu'amala tagari]_
Email-Karamciwritersass@gmail.comVisit to like my page on facebook https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsapp
On youtube https://youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ
On Wattpad https://my.w.tt/NuwIi6ubScb
_Sadaukarwa ga Asmiey Abdul(Husnah Soja)_
*Zanyi amfani da wannan dama wajen bawa masoyana hakuri, hakika kun nuna min so dan har yau baku gaji da bina kuna tambayana ko zan cigaba da rubutun wannan littafi, a zahirin gaskiya yanzu abubuwa ne suka sha kaina bana samun lokacin warewa dan typing, amma insha Allah zanyi kokarin cigaba da wannan book har zuwa karshe kasancewar sa gajeran labari, nagode da nuna kulawarku a gareni, wannan shafin sadaukarwa ne a gareku❤️*
'''Shafi na 11'''________________📲A gigice mai motar ya taka burki ya fito. Tuni mutane sun taru a gurin ana ta salati.
Cikin motar shi aka saka ta, sannan shima ya koma ya ja motar zuwa asibiti.****
Kuka sosai Mommy take lokacin da taga halin da Jannat ke ciki.
Ummu na daga gefen gadon tayi shiru ta kasa bawa Mommy haƙuri, dan itama kaɗan ya hana ta yiwa Jannat kuka.Suna cikin wannan halin likita ya shigo.
Bayan ya duba ta ya kalli Umma da yake itace a gefen gadon.
"Ku daina bari tana yawan shiga damuwa saboda zai iya haifar mata da ciwon zuciya, Bp ɗin ta yana yawan hawa""Insha Allahu zamu kiyaye Doctor"
Miƙa mata takarda yaye ta karɓa ya ce "Wannan itace takardar da mukayi reffering ɗinku zuwa asibitin yoyon fitsari dake garin jos, kuma da yardar Allah zata samu lafiya"
Sai lokacin Mommy ta ce "Doctor ina ƴar uwarta da take tare da ita?"
Murmushi yayi sannan ya ce "Hajiya banda abinki ina likita ina sanin inda wani yake wanda ya wuce mai jinya. Bamu tura ta sayan magani ba bare muce ko tana pharmacy."
*1 hour later*
Ummu miƙewa tayi ta ce "Bari naje gida, in saka ayi abincin dare a kawo, zan ƙara jaddadawa Alhaji halin da ake ciki, domin kuwa na san da yasan halin da Jannat take ciki da yazo, ya ɗauka jinyar bata kai haka ba."
"Baya ƙaunarta ne kawai, kuma na gane baya ƙaunata ne, tunda har baya son gudan jinina" ta ƙarasa maganar tana kuka.
Ummu ta dafa ta tana faɗin "Kada kice haka, dan Allah ki daina kukan nan kar ki tashi mara lafiya, yana son Jannat kawai dai wannan tsautsayin ne daya ratsa tsakani, amma dan Allah ki kwantar da hankalin ki, zanje na dawo kafin Jannat ta tashi."
Hawaye kawai Mommy ke gogewa har Ummu ta fita. Tashi tayi ta ɗauki ledar fitsarin ta juye fitsarin a poo sannan taje toilet ta zubar.
Ummu kuwa har ta gitta wasu mutanen taji wasu na faɗin "Kuma itama jinyar wata takeyi, kaga itama ashe jinyarta za'ayi" Gaban Ummu ya faɗi, ta kalli mazan dake tsaye suna maganar a ƙofar emergency.
"Wace mata ce aka kaɗai?"
"Wata budurwa ce, ƴar fara haka" ɗaya daga cikin su ya bata amsa.
"Tana ina?"
"Tana cikin emergency an rasa iyayenta ma"A tsorace Ummu ta shiga cikin emergency hankalinta a tashe tana ta addu'ar Allah yasa ba Safina bace.
Kan gadon ta hangota kwance, fuskarta nannaɗe da bandage an kuma saka mata jini.
YOU ARE READING
SANADIN MAHAIFINA (ILLAR FURUCI) DONE✅
Historical FictionGajeran labari ne, da yake nuna ILLAR FURUCI musamman cikin fushi. wannan littafin labari ne akan wasu ƴan mata wanda a ranar ɗaurin aurensu mahaifinsu ya furta mummunan kalami a kansu wanda wannan kalami ya bibiyesu kuma yayi sanadiyar rugujewar ra...