*•••SANADIN MAHAIFINA•••*
_[ILLAR FURUCI]_
'''Wattpad@ SaNaz_deeyah'''*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[Karamci tushen mu'amala tagari]_
Email-Karamciwritersass@gmail.comVisit to like my page on facebook https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsapp
On youtube https://youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ
On Wattpad https://my.w.tt/NuwIi6ubScb
_Sadaukarwa ga Asmiey Abdul(Husnah Soja)_
'''Shafi na 23'''
"Haba Hajiya, ya kamata zuwa wannan lokaci ace komai ya wuce, mu bamu riƙe ki da komai ba, kuma mu ba mu gaba dake, dan Allah idan har wani abu muka miki wanda kika riƙe mu a ranki, ki faɗa mana sai mu baki haƙuri" cewar Mommy.
"Sai an cuceka ace kayi haƙuri, idan har kin ɗaukeni a matsayin abokiyar zama ba kishiya ba, kuma kin ɗauki Farhan a matsayin ƴa, to wallahi da za ki ji zafin abinda wancan mugun ya mana, kamar yadda ni naji zafin abinda aka yi wa taki ƴar, amma unfortunately sai gashi ke kina neman tura ƴar ki gidan, bayan kunyi asiri kun fito da ƴata" Ummu ta faɗa cikin ɓacin rai.
"Hajiya Bilki idan kina irin wannan maganganun ranki zai yi bala'in ɓaci" Daddy yayi maganar a fusace. Ummu karɓa tayi da "Eh ai dama dole kace haka, tunda kaima an gama shanyeka, insha Allahu sai asirinku ya tonu" tayi tsaki ta wuce ta bar parlorn Daddy.
Jannat kukanta har neman fitowa fili yake "Na gaji gaskiya, ciwon zuciya ina tunanin nima shi ne ke ƙoƙarin kamani, bana iya samun isashen bacci, kullum cikin tashin hankali, gaskiya kama daina maganar aure tsakanin Jannat da Khalil domin ba ƙaramar tozarma za'a ƙara haɗawa ba"
"Ki daina wannan maganar Haj Falmata, ni na ba da goyon bayan hakan, domin na san Khalil bashi da laifi, don me zan goyi bayan ƙarya" Kallon Jannat yayi ya ce "Ke goge hawayen naki, ki yi tunani akan Khalil na baki sati ɗaya ki zo ki faɗamin hukuncin da kika yanke, sannan kuma maganar asibiti yaushe za kije kuma waye zai kaiki?" Share hawayen idanunta tayi ta ce "Daddy ni zan kai kaina, na daɗe banyi driving ba" "Za ki iya kuma, ke da ba isashen lafiya ba?" "Eh zan iya Daddy" "To zan bawa Falmata kuɗi sai ta baki, zan kuma kira Doctor ɗin kafin kije dan komai yazo miki a sauƙaƙe" "Nagode Allah ya saka da alkhairi" "Amin ya rabbi."
*****
Cikin tashin hankali ta kalli Doctor ta ce "Amma taya za'a ce lokaci ɗaya Ummata ta haukace?" kuka ta ƙara fashewa dashi Doctor na ta bata haƙuri. Ta ɗago jajayen idanunta ta kalleshi tare da sake faɗin "Kuma a gidan mahaukata dukansu ake kamar dabbobi, yanzu haka za ayi ta dukan Ummana."
"Wannan ba gaskiya bane, acan sai anfi mata magani, domin a yanayin zantukan da take da kuma wasu abubuwa ya tabbatar mana da cewa ta samu taɓin hankali, amma kada ki damu acan za afi bata kulawa, amma idan aka ce anan za a ajjeta to wata rana za ta gudu ne, tunda kin ga yadda takeyi, sannan kuma in aka ce dawwama za ayi da yi mata allurar bacci to gaskiya tana da side effect sosai."
"Shikenan Allah ya bata lafiya" "Amin ya rabbi, wannan ita ce kaɗai addu'ar da za ki riƙa mata" "To maganar Yayana fa?" "Shima jikin nasa ya ƙara zafi, amma idan ba damuwa zan baki wata shawara" "Ina sauraronka" "Me zai hana ku karɓi sallama ku mayar dashi private hospital sun fimu kayan aiki, duk da cewar a nan nake aiki, amma can sai kun fi samun kulawa ta musamman"
"Mu talakawa ne, kuma kusan komai namu ya ƙare a jinyarsa, bani da kuɗin da zan ɗauki Yaya zuwa private hospital" "Amma baku da ƴan uwa?" shiru tayi na wani ɗan lokaci kafin ta ce "Mu uku ne muke tafiyar da rayuwarmu, yanzu gashi jigon bata nan" ta faɗa tare fashewa da sabon kuka. "Calm down, ka da ki damu, idan nima kin ɗaukeni a ɗan uwa zan taimaka muku, duk da cewar nima ba wani ƙarfi gareni ba" kallonshi tayi ta kasa magana, shi kuma ya cigaba da cewa "Za muje asibiti, zan biya kuɗin har zuwa ya warke" ai jin haka ya saka ta tashi daga kujerar ta sauka har ƙasa ta fara masa godiya. Kallonta yake yana murmushi ya ce "Please tashi zauna mu ƙarasa maganar" zama tayi kan kujerar tana kallonshi.
YOU ARE READING
SANADIN MAHAIFINA (ILLAR FURUCI) DONE✅
Historical FictionGajeran labari ne, da yake nuna ILLAR FURUCI musamman cikin fushi. wannan littafin labari ne akan wasu ƴan mata wanda a ranar ɗaurin aurensu mahaifinsu ya furta mummunan kalami a kansu wanda wannan kalami ya bibiyesu kuma yayi sanadiyar rugujewar ra...