Hannah part 3

513 33 2
                                    

💥 *Hannah* 💥

        0️⃣3️⃣

*Maryam Abdullahi(oumramada)*
Whattpad@oumramadan1

Plate ta d'akko zata zuba musu ya rik'e hannunta murya k'asa k'asa yace "zuba mana akan naki"  kallansa tai ta saki murmushi kad'an ta k'ara guda 2 ta zuba souce d'in, cokali ta mik'a masa tace "eat"  a hankali ya fara cin alalen itama ta cigaba da ci ,d'ago da kanta tai ganin ya daina cin alalen ya zuba mata ido sai murmushi yake,turo baki tai tace "Yanaga ka daina ci"
Ajiyar zuciya ya sauke a hankali yace "ae bazan iya ciba"  ta zaro dara daran idanunta tace "sbd "
  "Sbd bazan iyaci da kaina ba"  yace mata a hankali, dariya ta saki tace "abu mai sauki,ai bayau na saba baka abinci ba" kusa dashi ta dawo ta  dauki cokalin  ta d'ebo takai bakinsa ,ganin yaki bud'e bakin yasa ta turo baki tace "to ka bude bakin "   lumshe ido yayi ya bude ta zuba masa a baki ,sai da ta basa sau 3 sannan ta ya kar6i cokalin shima ya fara bata hakan ba sabon abune a wajen suba sbd dama sun saba , da kansa ya yake bata a baki ita kuwa uwar san jiki har wani kwantowa take a kafad'arsa mamii ce ta fito kallo d'aya tai musu ta d'auke kai ,Farouk kunya ta kamasa ,shafa kansa yayi ya ajiye cokalin ya mik'e ,hanna tace "ka k'oshi ne yaya?"
Yana tafiya yace "eh"  bai yarda ya kalli mamii ba yace "mamii sai anjima" 
"To ALLAH ya kaimu"  tace masa bayan ta zauna akan kujera ,hanna tana gama ci ta dawo kusa da mamii ta kwantar da kanta akan kafad'ar ta tace "mami na koshi "
  Jin shiru yasa ta d'aga kai ta kalli mamii tuni ta shiga taitayinta ganin yadda mamin ta d'aure fuska hanna tai narai narai da ido tace "mamii"
Mamii ta sake had'e rai tace "wato hanna bakyajin magana ko"  ta marairaice tace "menayi mamii"  mamii ta sake d'aure fuska tace "naga randa zaki hankali shekaraki 18 a duniya amma kin kasa nutsuwa, bana hanaki kwanciya a jikin maza ba ko" 
  Hanna tai narai narai da ido tace "ALLAH mamii na daina "  hararta mamii tai tace "banason shashanci yaushe kika daina ,lallai zamu raba jaha dake tunda bakijin magana,"  tuni ta fara kuka amma ba hawaye tace "ALLAH mami na daina kiyi hkr "   shiru mami tai ta had'e rai, sai da taga hanna ta fara kukan gaske sannan ta lallasheta tace "kefa budurwace yanzu ,nasha fad'a miki ki daina zama jikin maza idan kuma kinaso raina yacigaba da 6aci to shikkenan " cikin rawar murya tace "aa mamiina na daina kar ranki ya 6aci kinji"  mamii tace "to yayi kyau maza kije lokacin makaranta yayi "   "to Kin hkr" hanna tace tana marairaice fuska ,murmushi tai tace "eh share hawayen"
Tana sharewa wani nabin wani ,mamii ta rumgumota jikinta taba shafa bayanta a hankali har hawayen ya tsaya sannan tai mata sallama ta wuce part d'insu,
Haydar yana tsaye  a bedroom d'insa fitowarsa kenan daga wanka sanye yake da farar bathrobe yana tsane jikinsa da wani farin towel ,gaban mudubi ya tsaya ya goge jikinsa ya fesa turare sosai kayan bacci farare k'all yasa ,wayarsa ya kalla da take ringing sai da ya gama kintsa jikinsa kamar wani mace sannan ya zauna ya janyo wayar da aka sake kira karo na 3 siririn tsaki ya saki yana kallan screen d'in wayar, *seeyama*  ya gani mayar da ita yayi batare da yayi picking ba ,sosai ya hassala ganin kiran ya sake shigowa ya sake janyo wayar ya sata a silent kashe Kwan d'akin yayi bayan ya kunna mara haske sosai ,
Tun da asuba hanna ta tashi ta shiga gyaran gidan tana tsaka da goge goge aunty ta fito, murmushi ta saki tace "Sannu da aiki auta"  hanna tace "yawwa aunty ,ina kwana "
"Lfy lau ya karatu,ina basma"  hanna ta tace "tana bedroom bata tashi ba"  wucewa bedroom d'in tai ta zauna bakin gadon ta bubbuga pillown da basma take kai ,basma da bacci yasha kanta sosai tace "wlhy hanna na tashi ranki saiya 6aci"  tsaki aunty ta sake cikin tsawa tace "maza tashi kafin na saya miki"  da sauri ta mike tana mutsutsuke ido aunty ta d'aure fuska tace "wlhy basma kin fiye san jiki da yawa ,Kamar hanna da take kanwarki tasan ta gama aiki tun asuba ke kizo kina baccin asara,banace tare tare zaku ringa komai na gidannan ba har sai in wani yanada uzuri"
  Basma tace "wlhy aunty jiya kwana nai karatu shiyasa ban tashi ba kinsan Exam ta kusa "  aunty ta tabe baki tace "to kidai fito ku k'arasa kinji dai na fad'a miki"
Sakkowa basma tai bayan tafiyar aunty ta zura hijab suka had'a breakfast ,suna gamawa hanna ta fad'a bandaki basma kuma tai kwanciyarta dan yau bazata shiga makarantaba,
  A dinning ta samu abba da bassam sai aunty da take zuba musu breakfast d'in,zuwa tai ta fad'a jikin abba tace "abbana ina kwana"  shafa kanta yayi yace "lfy lau auta kin tashi lfy,ya shirye shiryen jarabawa"
  "Lafiya lau abba"
Bassam yace "ina kwana parrott "  turo baki hanna tai tace "yanzu fa zan gaidaka yaya bassam "  dariya yayi yace "banga alamaba aunty hanna shiyasa "  ta kyalkyale da dariya tana zama a kujerar tace "wlhy yaya bassam bakaji yadda sunan yayi dad'i ba ka ringa fad'amin kaji"  ta k'arashe a shagwab'e, tabe baki bassam yayi yace "to sannu gyambo uwar son girma"
Abba dai murmushi yayi ,aunty ta tabe baki tace "to surutun zaki tsayayi yauma kisa su makara "  abba yace "ina basma ne "
  "Bacci take abba ,yau batada lecture "  hanna tace tana kurbar tea din da aunty ta had'a mata ,ba wanda ya sake magana har suka gama breakfast d'in abba ya wuce office  hanna kuma ta wuce makaranta.
  Tun daga nesa leemat take k'arewa haydar kallo lokaci d'aya ta nemi nutsuwarta ta rasa ,da sauri ta mik'e ta kar6i briefcase d'ij hannunsa murya na karkarwa tace "yalla6ai brk da safiya"
Ko kallan inda take baiyiba ya shige office d'insa ,rufa masa baya tai tana jin tamkar ta janyosa ta rumgumesa a jikinta ko zataji sassaucin abinda takeji a kansa ,leemat sakatariyar haydar ce sosai take bala,in shawa,arsa  irin yarannan nanne masu bala,in kwallafa rai akan namiji burinta kullum ta samu ko kissing d'inta yayi sai dai ko kusa bataga fuskar haka a wajensa ba dan ko kallo bata isheshi ba gaisuwarta ma sai yaga dama yake amsawa a rayuwarta kuma tafi yadda da makirci da kissa akan sihiri ko kad'an leemat bata yadda da bokaye ba ta rainawa ajinsu hankali tun ranar da kawarta taje yayi mata fyad'e yasa mata cutar kanjamu daga karshe bukatarta bata biyaba takekin bokaye dan ita bada kowa take had'a jikiba
  Turare ta sake fesawa tad'an zamo da rigar jikinta k'asa ta yanda kirjinta ya sake fitowa sannan ta turo k'ofar office d'in har wani lankwashe murya take sannan ta shiga ,
  File ta ajiye masa akan tebur cikin kissa tace "sir ga wad'annan file din Alhaji yace ka cikesu yanzu"  kusan 10mnt ya d'auka yana danna loptop sannan ya dauki file d'in ya cike, ba tare daya kalletaba ya ajiye  akan tebur ya cigaba da aikinsa,
  Leemat taji kamar ta d'ora hannu taita rusa ihu ko zataji dad'i haka taji taso ace ko kallanta ne yayi rai  6ace ta kwashi file d'in ta fice .

HannahWhere stories live. Discover now