Hannah part 6

413 33 0
                                    

💥 *Hannah* 💥

        0️⃣6️⃣

*Maryam Abdullahi(oumramada)*
Whattpad@oumramadan1

Zaro ido tai ta had'iyi wani miyau tanabin uban abincin da kallo ,lokaci d'aya ta fashe da kukan shagwab'a tace "wlhy bazan iya cinyewa ba"  ya sake tamke fuska yace "ok ina wasa dakene?"  Girgiza kai tai yace "na baki few minutes inba haka ba" ya k'arashe cike da keta, tsakurar abincin ta farayi jitake kamar tai amai tun tana kukan shagwab'a harta koma na gaske ,marairaice murya tai tace "yaya haydar na koshi" mugun kallon daya aika mata yasa ta cigaba dashi kuka take bilhakki shi kuwa banda danna waya ba abunda yake ,sai da yaga ta cinyesa tass sannan ya mik'e yana hararta, ta yunkura dakyar tana wani nishi taku biyu tai ta sake fashewa da kuka tace "nidai bazan iya tafiya ba yaya haydar "  ya wurga mata harara yace "uban wa kike jira ya d'aukeki to"
  Shiru tai tana wata tafiya dakyar a duk'e tana matse kwalla,tana gani ya wuceta fuska a tamke ,harara ta zabga masa tace "kuma ALLAH ya isana mugu"  koda ta shiga bedroom d'in mamii kasa kwanciya tai sbd cikinta dayayi wani iri sai da ta dad'e sannan ta kwanta tana ta hararar d'akin,
  Tafe suke itada fannah dawowarsu kenan daga islamiyya ,turo get d'in gidan sukai tsaye sukaga mutum sanye da kananun kaya Jean's da tshirt hanna tace "ga yaya Farouk da yayimana alkawarin kaimu shopping"  fannah tace "ae wlhy muje saiya kaimu gsky"  har rige rige suke wajen k'arasawa ,hanna ta rumgumesa ta baya cikin shagwab'a tace "ALLAH na kamaka yaya Farouk " Jin shiru yasa fannah ta riko hannunsa ta leka fuskarsa lokaci d'aya ta saki hannun cikin wani masifaffan tsoro daya kamata tuni jikinta ya fara rawa kamar mazari hanna kuwa sake kalailayeshi tai tace "shine kamin shiru ko yaya Farouk "  fannah sai kyafta mata ido take a tsorace sam bata kulaba,juyowa yayi ya rik'e hannayensu yana musu wani mugun kallo, sai sannan hanna ta gansa ta zaro manyan idanunta tana kallansa a mugun tsorace, Farouk da yake tahowa daga part dinsu tun sanda hanna ta rumgume haydar yake kallansu murmushi ya saki yana shafa kansa ya k'arasa wajen ,murya na rawa hanna tace "dama mun zata yaya Farouk ne"  fannah ta gyad'a kai ji take kamar ta saki fitsari dan tafi hanna tsoro wayarsa ya maida aljihu ya kama hannuwansu duka ya koma can wajen balcony Farouk binsa yayi yace "pls haydar kai musu afuwa"  bai saurareshi ba sai da ya zauna yayi musu wani kallo yace "ku kama kunnuwanku"  zaro ido hanna tai ta fasa kukan shagwab'a fanna kuwa mitsi mitsi tai da ido kamar ta arce haka takeji,
  Farouk yace "pls haydar"  sai nannan haydar yace "ka barni na koya musu hankali ko yayane"  sanin halin haydar d'in in yayi magana inba mamii ko daddy ba bamai canza masa ra,ayi yasa Farouk yabar wajen yana sakin karamin murmushi,
  D'ora kafa d'aya Kan d'aya yayi yana operating wayarsa,kusan minti 30 suka d'auke a tsugunne kafafunsu banda tsami ba abunda suke kuka kuka sunyi har sun gaji,jin karar hon yasa haydar kallansu yana dariyar mugunta wucesu yayi yana sakin tsaki, zubewa a wajen fannah tai tana kukan zugin da kafarta take mata ,hanna kuwa ko kallanta batai ba ta wuce part d'insu tana zuwa ta zube a parloun ta fasa sabon kuka ,
  Da sauri aunty ta fito daga bedroom tace "ke lafiyarki kuwa"  ta sake rushewa da kuka cikin sheshsheka tace "ba yaya haydar bane" sai ta sake fasa ihu, aunty ta rud'e duk ta d'auka wani abunne ya samu haydar d'in tace "ke banason shashanci meya sami haydar d'in?" Tana kuka tace "kamun kunnefa ya samu aunty"  da gudu ta mik'e ta shige bedroom d'insu ganin aunty tana niyyar kai mata mari, da harara aunty ta rakata tana huci tace "sakaryar yarinya kawai"
  Tana shiga ta fad'a Kan gado tanaji basma tana tambayarta tai mata shiru sai da tai kuka mai isarta ta mike tana tafiya a kaikaice, basma ta kusa  sakin dariya tace "meya samu kafar taki"  mates kwalla tai tace "ba wannan mugun bane ya samu kamun kunne"  zaro ido basma tai ta ajiye handout d'in hannunta tace "wai yaya haydar kike cewa mugu?"   Kallanta hanna tai tace "to ba mugun bane,nidai wlhy saina rama mugu kawai"  tana gama fad'a ta fad'a bathroom tabar basma tana mata dariya,
  Wanka tai da ruwa me dumi ta fito d'aure da towel zama tai bakin bed ta marairaice fuska tace "yaya basma dan ALLAH ki shafamin aboniki kafata ciwo take"  basma ta fashe da dariya harda kwanciya tace  "ba ruwana ina gama miki zakimin fitsara"  hanna ta matse kwalla tace  "ALLAH bazan miki ba"  aboniki ta d'akko ta shafa mata a kafafun duka duk da yadda take rakin kafarta a ranta kuwa tunanin irin muguntar da zataiwa haydar take.

HannahWhere stories live. Discover now