Hannah part 28

385 41 5
                                    

💥 *Hannah* 💥
*Romantic love story*
        2️⃣8️⃣

*Maryam Abdullahi(oumramadan)*
Whattpad@OumRamadan1

  Sakin wayar yay  ya runtse ido cikin  wani irin tashin hankali ,Cikin raunanniyar murya yaji hanny tace "ashe abunda ake fad'a akan wasu masu kudin gskyne, ashe duk abinda kafad'amin da farko ba haka bane,yanzu in yarkace ta nunama wannan shedar zaka karyatata?" Ta goge kwalla tana sheshsheka tace"shikkenan bakomai Zanje inda za,a bimin hakkina kamar yadda ka fad'a ba wanda yafi karfin hukuma zanje kotu na shigar da k'ara na tabbatar wannan shedar kad'ai dazan nuna ta isa tasa a zartarwa da d'anka hukunci, duniya zatasan abinda danka ya aikatamin mutane zasuyi turr da halinsa " cikin fad'uwar gaba ta juya zata wuce da shakakkiyar murya senate yace "dawo ki zauna muyi magana" wani murmushi ta saki cikin jin dad'i tana juyowa ta sauya fuska zuwa kalar tausayi ,tsadaddiyar wayarsa ya miko mata bai kalletaba yace "ki samin number mahaifinki" jiki na rawa tasa number duk da gabanta ba karamin fad'uwa yay ba in mahaifinta yaji wannan zancan amma ta yarda ta jure komai indai zata rama abinda mk yay mata muryan senate taji yace "Zaki iya tafiya zan nemi shi mahaifin naki" sum sum ta fice daga parlourn ranta fari tass kamar takadda,
  Tana fitowa taga motoci 2 sun shigo a wani lungu ta la6e tana kallan masu fitowa bata wani gane ko suwaye ba sbd ba abba a tafiyar, tana tsaye taga big daddy ya ciro waya yay Kira ,minti 5 wani security yazo ya taho dasu bayansu kuma an fito da akwatuna ana shiga dasu side d'in senate, jitai kamar ta daka tsalle dan murna har wani ihun dad'i ta saki tana ganin sun gama shigewa ta fito kamar zata kifa da sauri ta fice daga gidan,
  Senate bai gama fita daga tashin hankalin da hanny tasa masa ba yaga ana shigowa da akwatuna ga kuma su daddy ko wanne fuskarsa ba yabo ba fallasa mikewa yay cikin fad'uwar gaba da tashin hankali jirine ya kwasheshi zai fad'i  small dad ya tarosa da sauri yace "Subhanallah bakada lfyne" baice komai ba sai murmushin takaici daya saki yanabin kayan da aka jere da kallo yace "Bismillah ku zauna" Zama sukai big daddy yace "to ranka ya dad'e maganace me muhimminci take tafe damu akan auran yaronka da Yar wajenmu"  tagumi yay ya tsurawa waje d'aya ido ya kasa kallansu yace "Ina jinki alhaji abdullahi"
Big daddy yace "bayan dogon binciken da mukai muka tabbatar da gaskiyar abinda muka gani yasa muka yanke shawarar fasa wannan auran, sbd akwai cutarwa a ciki ga kayan da aka kawo nan da kudi dama ba abunda aka ta6a a ciki" shiru senate yay jikinsa yay bala,in sanyi dakyar ya bud'e baki zai magana ya kasa sai tagumi daya zabga ,sai can ya bud'e baki y shiga basu hkr muryan sa har rawa take tsaban bacin rai , tausayinsa sukaji sbd ba karamin kaduwa yay ba ace d'anka daka haifa ya ringa aikata wannan aikin har yana ikirari da gadara,
  Duk yadda senate yay su koma da kayan ki sukai daga k'arshe mikewa sukai zasu tafi senate yace "Dan Allah Ina neman wata alfarma a wajenku" daddy yace "toh munaji" senate yace "banaso ku nunawa wannan yaron komai akan maganar fasa wannan bikin dan Allah kumin wannan alfarmar, sannan nima zanzo masallacin da tun farko aka tsara daurin auren, akwai auran da zamu d'aura"  big daddy yace "to indan wannan ne ba matsala Allah ya kaimu"
Daga haka sukai sallama,zama senate yay ya tsurawa kayan ido wayarsa ya d'auka ya Kira number da Hanny ta bashi kusan wayar minti 10 sukai kana ya kuma Kiran wata wayar,
  Daga k'arshe kayan yasa aka kwashe kaf aka zubasu cikin mota ,ko minti 5 ba,ae da kwashe kayan ba mk ya shigo, tsura masa ido senate yay cikin tsallan 6acin rai  yana kallansa zuciyarsa har wani tiriri take ba karamin yaki da zuciyarsa yake ba ganin inya cigaba da zama zai iya aikata abinda zuciyarsa take raya masa ya 6ata shirinsa yasa ya mike a karo na biyu ta tafi zai kifa mk ya tareshi a rude yace "daddy bakada lfyne" rufe ido yay kansa na wani irin sarawa ga zazza6i daya lullu6esa ,taimaka masa yay ya kwanta da sauri ya dakko wayarsa yay dialling number dr da yake dubashi kana ya kira hajiya sara da kanta ya fara d'aukar caji sbd yadda gidan nata ya dinke da jama,a,
  Duk sunyi jugum jugum suna kallan dr dayake cirewa senate ledar ruwan daya kara masa,magaunguna ya bashi sbd hawan jininsa daya tashi yay musu sallama ya fice,
  Aunty ce da Mami zaune a bedroom aunty ta Kuma share hawayen daya zubo mata Mami tace "haba Maryam kukan me kike,muda yakamata ace munfi kowa farin ciki Allah ya tsallakar da ita daga azzaluminnan me fuska biyu " aunty tai murmushi tace "wlhy Mami kukan farin ciki da godiya ga Allah nake, tunda aka tsaida maganar aurannan hankali bai gama kwantawa dashi ba ban ta6a kai sujja ba batare da nayi addu,ar Allah ya tabbatar da aurannan in alheri bane ,in Kuma ba alheri bane Allah ka watsa abun ,duk Wanda ya kasa kaiwa Allah bukatunsa hakika ya ta6e inba Allah ba waya isa ya fito masa da mugun halin yaronnan mami," itama murmushi Mami tai tace"hakane Maryam shiyasa akeso Koda yaushe bawa ya kasance me neman za6in Allah a kowanne lamari nasa hakika Allah yayi gsky da yace duk Wanda ya rokeshi zai amsa masa,ni dotana nake tunanin halin da zata shiga dan naga tana bala,in sonsa , amma kansa ya cuta Kuma insha Allah zai gamu da daidai shi" jikin aunty ya karayin sanyi tace " ni kaina Ina wannan tunanin  Mami, gashi Abban nasu yacemin bikin hanna yananan ba fashi a tsaitsaye dai yamin maganar yace zai karasamin zancen ajima" kafad'ar ta mami ta dafa tana murmushi sosai tace "karki wani damu Maryam inaji a jikina insha Allah zasu za6a mata miji na nunawa bazasu ta6a mata za6en tumin dare ba ,insha Allah wannan karan nagartaccen miji dotana zata aura " aunty tace "ni kaina duk wannan karan hankalina yafi kwanciya haka kawai zuciyata tai na,am banajin rashin jin dadin abun kamar wancan, duk da har yanzu bai fad'amin mijin da za,a aura Mata ba amma dai anjima zamu karasa maganar nasan zai fad'amin ko waye , dama tuni nasa basma ta d'aukemin wayarta na Kuma hanata bata tata wayar karma tai kokarin kiransa "
  "To ae shikansa yaron baisan an fasa ba haka Alhaji ya sanar min,uban yaron yace kar a nuna masa an fasa a barshi harsai ran d'aurin auran" ta6e baki aunty tai  tace "toh Allah ya kyauta " haka suka cigaba da tattaunawa akan lamarin bikin,
  Dama tun safe senate ya fice shida d'an uwansa zuwa gidansu Hanny duk da har yanzu jikin bai masa daidai ba haka ya d'aure dama ko kusa bai shirya sanar da hajiya sara hukunci daya yankeba harsai an d'aura auran, danya tabbatar saita fad'awa mk Kuma ita kanta bazata goyi bayan wannan hadin ba , a parlourn baki daddyn hanny Alhaji lawan ya saukesu jiki na rawa tuni aka cika Masa gabansu da kayan motsa baki,  a haka ya zauna suka gaisa a mutunce saida aka kwashi kusan minti 5 senate ya rasa ta hanyar da zai sanarwa da alhaji lawan , haka ya d'aure cikin kunar rai da takaicin abun ya shiga sanarwa da alhaji lawan abinda ke tsakanin mk da Hanny da irin hukuncin daya yanke,
  Mutuwar zaune alhaji lawan yay yanabin senate da wani irin kallo kwata kwata bai yadda da maganar da senate yazo Masa da itama cikin kokwanto yace "ranka ya dad'e Anya kuwa ba kuskure aka samu wajen bada number ba?"  Murmushin takaici senate ya saki yace "Alhaji lawan kenan, nima da farko irin kokwanton daka shiga na shiga ban gasgata zancen ba Saida na samu gamsashshiyar hujja me karfi kafin nazo amma ka shiga ciki ka tambayi ita yarinyar taka kaji" Girgiza Kai Alhaji lawan yake jiki na rawa ya mike ya shiga cikin gidan tun kafin ya k'arasa ya shiga kwalawa Hanny da mahaifiyarta Kira .

HannahWhere stories live. Discover now